_*YIN SALLAR NAFILA BAYAN SALLAR JUMA'A*_
_Sunnace ga wanda yaje Sallar juma'a yayi Nafila bayan juma'a raka'a hudu a masallaci ko raka'a biyu a gida. An ruwaito adadin raka'oin da suka tabbata anayi na sallar Nafila bayan Sallar juma'a acikin Hadisai da dama ga kadan daga cikin su:_
_*1-ANAYIN RAKA'A GUDA BIYU(2)*_
_Daga *Ibn Umar R.A* yana cewa: *"Annabi ﷺ ya kasance baya yin Nafila bayan Sallar juma'a har sai ya juya sanna yayi Sallar raka'a biyu"*_
*@ ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ( 937 ) ﻭﻣﺴﻠﻢ ( 882 ) .*
_Awata Riwayar: *"Annabi ﷺ ya kasance baya yin nafila bayan juma'a har sai ya fita daga Masallaci sai ya Sallaci raka'a biyu a gidansa".*_
*@ ﻣﺴﻠﻢ ( 882 ) ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺰﺍﺩ ( 1/440 )*
_Awata Riwayar: *"Ya kasance idan yayi Sallar juma'a sai ya shiga gidansa sai yayi Raka'a guda biyu ko hudu na Nafila".*_
_*2-ANAYIN RAKA'A HUDU(4)*_
_Daga *Abi Hurairata R.A* yana cewa: "Lallai Annabi ﷺ yace: *(Idan dayanku yayi Sallar juma'a to yayi raka'a guda hudu a bayanta ta nafila).*_
*@ ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ ( 881 ).*
_Awata Riwayar: *Annabi ﷺ* yana cewa: *(Idan dayanku yayi Sallar juma'a to yayi Sallar nafila raka'a hudu bayanta).*_
_Awani lafazin: *(Wanda zaiyi nafila bayan juma'a to yayi raka'a hudu).*_
*@ ﻣﺴﻠﻢ ( 881 ).*
_*Shiekul Islam ibn Taimiya Allah* yayi masa Rahama yana cewa: *"Idan dayanku zaiyi nafila bayan juma'a a masallaci sai yayi raka'a hudu, Amma idan a gidane sai yayi raka'a biyu".*_
_Mafi yawan Malaman Fiqhu sun tafi akan: "Mustahabbine akan wanda yaje sallar juma'a yayi nafila raka'a hudu, wannan shine maganar *Ibn Mas'ud* da wasu daga cikik Sahabbai"._
*@ ﻣﺼﻨﻒ ﺍﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺷﻴﺒﺔ "* *( 2/40 41- ) ،ﻭﻫﻮ ﺍﺧﺘﻴﺎﺭ ﺍﻟﺤﻨﻔﻴﺔ ،ﻛﻤﺎ ﻓﻲ " ﺭﺩ ﺍﻟﻤﺤﺘﺎﺭ " ( 2/12 13- ) ، ﻭﺍﺧﺘﻴﺎﺭ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺸﺎﻓﻌﻲﻓﻲ " ﺍﻷﻡ " ( 7/176 )*
_*Imam Ahmad* yana cewa: *"Wanda ya so yayi raka'a biyu ko raka'a hudu".*_
*@ ﺍﻟﻤﻐﻨﻲ " ( 2/109 ) .*
_Amma abinda yafi shine wanda zaiyi nafilar a masallaci yayi Raka'a hudu wanda zaiyi a gida sai yayi raka'a biyu. Wannan shine ra'ayin ibn Qaiyim da Ibn Taimiya._
*@ ﺯﺍﺩ ﺍﻟﻤﻌﺎﺩ " ( 1/417 ) .@ ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺍﻟﻠﺠﻨﺔ ﺍﻟﺪﺍﺋﻤﺔ ( 6/131 )*
_*Allah* ne mafi sani._
Rubutawa:- Mustapha Musa
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.