CUTAR BASIR



CUTAR BASIR
👇👇👇👇👇👇👇👇

 Cutar Basir ko kace BAWASIR da larabci da turanci kuma ana cewa File. 
 Cutar Basir cuta ce wadda take da dadadden tarihi.
  A zamanin manzon Allah saw Akwai wani Sahabi mai suna IMRAN IBN HUSSAIN, Wansa wannan bawan Allah yayi fama da jinyar Basir tsawon shekara da shekaru bai Sami sauki ba, a koda yaushe yana kwance, baya iya tashi zaune. Amma Da haka kuma mala'iku suke zuwa suna masa sannu. Harma su mika masa hannu suyi musabiha, manzon Allah saw ya tabbatar masa da cewar Mala'iku ne. Wanda wannan jinyar itace ta kaishi ga Ajalinsa. Harma an rawaito cewar IBN SIREEN yana cewa, duk lokacin da Naje dubiyar IMRAN BIN HUSSAIN Sai naji Kamar in kamu da jinya, Sabida yadda nake tarar da jikinsa.
  
👉 NAU'IN JINYAR BASIR GA DAN ADAM.
-Akwai Basir mai tsiro. Wanda wannan shine Basir Mafi zama Worst ga Rayuwar Dan Adam. Sabida wani lokacin idan ba'a dace ba, yana da wahalar komawa, ko kuma da zarar mai wanan cutar Basir din mai fitowa yaje Asibiti to Za'ayi masa tiyata, a yade tsiron. Wanda kuma da yawa idan akayi tiyata ba kowanne bane yake tsallakewa ba.
 Sau da yawa masu irin wannan Basir din, idan ya zama shine Ajalinsu, ana musu tsargin cewar Kamar HIV ce ta kashe su. Sabida yadda yake maida Rayuwar Dan adam.
- Akwai Basir mai yawan kumbura ciki. Mai irin wannan Basir din, Zaina ganin Cikinsa yana kumbura, yana daukar Iska. Kuma hakan zaisa mutum yana yawan Tusa. Babu kai babu kafa. Sabida wannan kumburin. Wani ma Sai yayi alwala sau babu Adadi. Sabida yana yi tana karyewa.
- yana daga alamar basir, mutum zaina jin duburarsa tana Zafi, Amma ba tare da tsito ya fito masa ba.
- Yana daga Alamar Basir mutum zaiji Tsantsarsa wani lokacin Kamar zata cire. Har Sai ya Sami wuri ya zaina ko ya kwanta.
- Yana daga Alamar Basir idan mutum yana jin Cikinsa yana murda masa, kuma idan ya Murda Sai yayi bayan gida. Sannan ne zai Sami sauki.
- Yana daga alamar Basir idan mutum yaji bayan gidansa yana Yin tauri, yaki fitowa, Harma wani lokacin Sai mutum ya goga sabulu, sannan ne zai samu ya fito daga duburarsa. Ko idan mutum yaje zaiyi ba haya Sai yaga yayi Dan kadan.
- Yana daga alamun Basir, idan mutum yana jin Kashin jini. Wani idan yayi kashi zaiga jini, sannan idan ya zauna zaiga jini a daidai wurin da ya zauna, Kamar Matar da ta haihu.
- Yana daga alamar Basir idan mutum yana Tsarki Bayan ya gama Bayan gida, Sai yana jin Maiko a duburarsa.

👉 ME YAKE JAWO WANNAN CUTA TA BASIR?
 Abubuwan da suke kawo wannan jinya ta Basir Akwai:-
 Yawan zama. Musamman masu sana'ar zama, su sukafi kowa jinyar Basir. Kamar direbobi Ko Teloli ko masu zaman office.
 Musamman ma direbobi ko mai yawan tafiye-tafiye. Ga yawan zama ga kuma zafin inji.
- Yawan cin abinci mai 
 tsananin Maiko ko tsananin Zaki.
- Zama akan abinda yake da Zafi. Kamar zama a sit din mashin a lokacin da ya dauki Zafi.
- Rashin Amfani da magungunan Basir Akai-Akai. Sabida jinya ce da kusan kowanne Dan adam yana dashi.

👉 WACCE HANYA ZAMUBI WAJEN KAUCEWA DAGA WANNAN JINYAR.?
  Hanyar da zamubi wajen kaucewa wannan jinyar shine. Kauracewa zama sosai da kauracewa yawan shan Kayan zaki da Maiko da Amfani da sabulu wajen yin Tsarki idan mutum yayi Bayan gida.

Wanda ya gamsu kuma yake bukatar ingantattun magungunan Basir (Harbals) mun tanadesu na gida Nigeria da na wajen Nigeria. Sai ya tintibemu a lambar Waya 08137783797 ko ta whasapp da wannan number din.
  Kasuwarmu Online ne, Aikawa muke ga Wanda ya bukata cikin sauki. Idan baka gamsu ba, karka Tintibemu.

ZAUREN SUNNAH ISLAMIC MEDICINE CENTER 08137783797
Post a Comment (0)