ME YASA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE?

*_MEYA SA ALJANU SUKE SHIGA JIKIN MUTANE?_*

                              *Tambaya:*
Assalamu alaikum malam, me yake kawo aljanu jikin Dan adam, Kuma meza a yi a rabu da su?

                                    *Amsa:*
Wa'alaikum assalam sakaci da ibada da zikirori na daga cikin abubuwan da suke kawo aljanu,duk mutumin da yake yawan azkar yake kuma kiyaye dokokin Allah,da wuya aljani ya shiga jikinsa, Saboda şu zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da shiga bandaki da fitowa suna kariya daga shaidanu.

Saidai ko da mutum yana da nagarta, aljani yana iya shiga jikin mutum ta hanyar sihiri ko kambun baka, ko yawan fushi.

Ayoyin Alqur'ani na korar aljani daga jikin dan'adam,musamman Suratul Bakara da Kula'uzai biyu da ayatul kursiyyu da surorin tauhidi guda biyu.

Allah ne mafi sani.

11\5\2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)