HUKUNCIN ALLURA GA MAI AZUMI

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum
Dan Allah menene hukuncin allura game axumi?

_*Amsa:*_

_WA'alaikumussalamu Warahmatullah._

_Ya halatta mai azumi ya yi allura matukar allurar ba mai dauke da sinadaran abinci ba ne, wato ba za ta sa mutum ya ji wani chanji a cikin sa ba._

_Domin *Hasnul basri* ya ce: babu laifi mutum yasa Magani a cikinsa, wanda hakan ya kunshi allura ne, sai dai idan tana da abinci a cikinta._

_Duba: Duba Athar na Husnul Basri (Bukhari, babi na 25, kitabus siyam)._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_

Post a Comment (0)