*_Tambaya_*
:
_Menene hukuncin *Azumin* Mutumin da yayi mafarkin jima'i da rana kuma har *Maniyyi* yafito masa, shin azuminsa yana nan kokuma ya lalace??_
:
*_Amsa:_*
:
_Dangane da hukuncin *Fitar Maniyyi* ga wanda yake azumi mafi yawan Malamai cikinsu harda *Mazhabobin nan guda huɗu wato:*_
:
_*(1)---Malikiyya,*_
_*(2)---Shafi'iyya,*_
_*(3)---Hanafiyya,*_
_*(4)---Hanabila,*_
:
_Dukkansu suntafine akan cewa fitar da *Maniyyi* da gangan ta hanyar da ba jima'i ba yana lalata azumi, kamar idan *Mai-Azumi yayi Istimna'i,* ko ya rungumi *Matarsa, ko yayi wasa da'ita,* hartakai ga yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace, danhaka Malamai sukace dukkan Mutumin da yasan cewa *Sha'awarsa tana da ƙarfin da indai zaiyi wasa da Matarsa Maniyyi zai iya fito masa* to haramunne agareshi yayi hakan da'ita, idan kuwa yayi har Maniyyi yafita to wajibine sai yarama wannan azumin, amma idan yakasance *Maniyyin yafitane ta hanyar mafarki* kokuma tunani ko kallon Mace batare da yayi wasa da'itaba, mafi yawan Malamai sukace azuminsa bai lalace ba saidai wajibine yayi wankan janaba, amma *Mazhabin MALIKIYYA* sukace koda mafarki yayi dolene sai yarama wannan azumin guda daya da yayi mafarkin acikinsa,_
:
_Amma idan da gangan yayi wasa da Mace koyayi Istimna'i, ko kallo na sha'awa haryafitar da maniyyi, to anan *Malamai sunyi Saɓani* dangane da yanayin ramuwar azumin da Mutum zaiyi, Mafi yawan Malamai sun tafine akancewa zai rama azumi guda ɗayane kawai batare da yayi wata Kaffara ba, domin *Nassin yin Kaffara yazone akan wanda yayi Jima'i da Matarsa da rana,* Saidai Mazhabin *MALIKIYYA* suntafine akan cewa idan Mutum yayi *Mafarki* har yafitar da Maniyyi to azuminsa ya lalace kuma dolene sai ya rama batare da kaffaraba, amma idan wasa yayi da Mace ya rungumeta ko ya Shafata ko yayi *Istimna'i har yafitar da Maniyyi,* to wajibine sai yayi ramuwa tare da Kaffara, domin *sunyi Ƙiyasine akan hukuncin wanda yayi Jima'i da Matarsa da gangan da rana,*_
:
_Amma *Mazhabin ZAHIRIYYA* suntafine akan cewa wanda yafitar da Maniyyi da gangan ta dukkan wata hanyar da ba *Jima'i yayi da Matarsa ba* sukace azuminsa yana nan bai lalace ba, domin babu wata *Hujja afili Ƙarara daga cikin Al-Ƙur'ani ko Hadisi* datace azuminsa ya lalace, to amma Saidai maganar Malaman da sukace azuminsa ya lalace tafi *Ƙarfi,*_
:
_Amma maganar da tafi inganci wacce mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da'ita shine, *fitar Maniyyi ta hanyar mafarki baya karya azumi,* domin *Ɗan-Adam* bashi da wani iko na ya'iya hana kansa yin mafarki alokacin da yake barci, hakanan magana mafi inganci *fitar Maniyyi ta hanyar tunani ko kallo shima baya karya azumi,* amma duk dahaka ba'ace Mutum yarika sanya irin wannan tunanin acikin Zuciyarsa ba, amma *fitar Maniyyi dagangan tahanyar wasa tsakanin Ma'aurata, ko tahanyar Istimna'i,* wannan kam yana lalata azumi, kuma za'ayi ramuwane kaɗai batare da *Kaffaraba,* amma idan Mutum yayi jima'i da *Matarsa* da gangan da rana, tofa koda baikawo *Maniyyiba* ramuwa da Kaffara sunhau kansa:_
:
*_o(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)o_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
*_↓↓↓_*
:
*"المغني لإبن قدامة" (4/363)*
:
*الشرح الممتع" (6/234)*
:
*"المجموع للنووي" (6/349)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
*Daga Zaυren*
*Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
*_→AMSAWA←_*
*Mυѕтαρнα Uѕмαи*
*08032531505*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Tags:
Tambaya Mabudin Ilimi