_*Tambaya:*_
Assalamu Alaikum
Dn Allah ina tmbaya akn hukuncin fitowar maziyyi lokacin axumi
_*Amsa:*_
_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._
_Magana mafi inganci kuma wanda ita ce dai-dai shi ne *Madziyyi* ba ya karya azumi, kuma wanda ya yi madziyyi a lokacin azumi, to azuminsa bai lalace ba._
*Ibn Baaz* yake cewa: _“Fitar maniyyi ga mai azumi ba ya karya azumi, wannan shi ne zance mafi inganci a wajen malamai magabata"_
_Babu wani nassi da yake nuni da cewa Madziyyi ya na ɓata azumi. Don haka zance mafi inganci shi ne, wanda ya fitar da madziyyi ba zai rama azumin ba kuma ba zai yi kaffara ba._
_Wallahu A'lamu._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_*🧕🏽Islamic Post Women.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_