_*Tambaya:*_
Assalamu alaikum malam dan allah inaso akarayimin bayani gami dakaratun tahiya nafarko datakarshe.
_*Amsa:*_
_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._
_To shi dai karatun *Tashasshud* (Tahiyya) ta farko da ta karshe ba su da wani bambanci, dukkansu karatunsu daya ne. In shaa Allah. Ga yadda take a rubuce:_
*التَّحِيَّاتُ لِلّهِ، وَالصَّلَوَاتُ، وَالطَّيِّبَاتُ، السَّلاَمُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللّهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلاَمُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ للّهِ الصَّالِحِينَ. أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَاّ اللّهُ، وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّداً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ.*
*At-tahiyyatu lillahi, was solawãtu waɗ-ɗayyibat, assalamu alaika ayyuhan nabiyyu warahmatullahi wabarakatuhu, assalamu alaina wa ala ibãdillahis soliheena. Ash-hadu an Laa ilaaha illallah, wa Ash-hadu anna muhammadan abduhu warasuluhu.*
_Ma'ana: *Daɗaɗan gaisuwa na Allah ne, da salloli da kyawawan kalamai, aminci ya tabbata a gare ka ya kai Annabi, da rahamar Allah da albarkarsa, aminci ya tabbata a gare mu da bayin Allah solihai. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa lallai Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne.*_
_An ruwaito lafuza daban-daban na Tahiyya daga Annabi (ﷺ), kowani lafazi mutum ya lizimta daga cikin wadanda aka ruwaito ya yi dai-dai in shaa Allah._
_Ita ce ake karantawa a zaman farko da na karshe, duka ba bambanci._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_