MAZA MUJI TSORON ALLAAH MUYI ADALCI A TSAKANIN MATAN MU

*_MAZA MUJI TSORAN ALLAH MUYI ADALCI A TSAKANIN MATAN MU_*

Lallai wajibine muyi adalci a tsakanin mata ga wanda yake aure mace sama da daya dole yayi adalci a tsakaninsu,ya sani dukkan abinda yake gudana Allah yana sane kuma yana ganinsa kuma wallahi sai Allah ya tambayesa akan zaman da yayi dasu a gobe alqiyama.

Manzon Allah SAW yana cewa;
(Dukkan wanda yake da mata guda biyu sai ya karkata ga daya baya yiwa Dayar adalci,zai zo a ranar alqiyama bangaran jikinsa guda a shanye)
@رواه أصحاب السنن الأربعة،واللفظ للنسائي وصححه الألباني.

Malamai sunce karin aure ba wajibi bane ba mustahabbine ga wanda yake da iko ya kara,amma wajibine kayi adalci,idan har kasan bazakayi adalciba to kada ka fara neman kara auren ma domin karin zai iya kaika zuwa ga halaka.

Manzon Allah SAW yana cewa;
(Dukkanku masu kiwone kuma dukkan ku abin tambayane akan abinda aka baku kiwo agobe alqiyama..........)
@صحيح الجامع.

Allah acikin alqurani yayi hani akan kada mai gida ya karkata gaba daya zuwa ga wata daga cikin matansa ya kyale sauran mata saboda rashin adalci.Allah yana cewa;
(وَلَن تَسْتَطِيعُوا أَن تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّسَاءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ ۖ فَلَا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوهَا كَالْمُعَلَّقَةِ ۚ وَإِن تُصْلِحُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَّحِيمًا)
@النساء(129 Nisaa

Ma'ana
(Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin yi. Sabõda haka kada ku karkata,dukan karkata,har ku bar ta kamar wadda aka rãtaye.Kuma idan kun yi sulhu,kuma kuka yi taƙawa,to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙa)

Adalci shine baima kowacce hakkin da Allah ya daroa maka na zaman aure,wanda ya hada da ci da sha da kula da lafiya da tarbiya da bada ilimi da raba ranar girki da sauransu.

Amma baya cikin adalci ace ace sonsu ya zama daya wannan babu wanda zai iya yin hakan saboda Allah bai halicci dan adam da wannan dhabi'a ba,shiyasa Manzon Allah SAW duka cikin matansa yafi son Nana Khadija R.A amma cikin mata guda tara da suka zauna lokaci guda yafi son Nana Aisha R.A

Allah ne mafi sani.

Rubutawar: ✍
*_Malam Mustapha Musa Abu Aisha {Hafizahullah}._*

Post a Comment (0)