Ramadaniyyat 1442H [14]
Dr. muhd Sani Umar (Hafizahullah)
Sahabbai Shaidu ne Nagartattu
_______________________________
1. Daga cikin abin da yake nuna nagartar wadannan bayanin Allah shi ne abin da Allah (SWT) ya fada a cikin Alkur’ani yayin da yake magana da Annabi (ο·Ί) game da Alkibla. Annabi (ο·Ί) ya kasance yana addu’a Allah ya juyar masa da alkibla ya dawo yana kallon ka’aba maimako Baitul Makdis da yake kallo shi da sahabbansa idan suna salla. Allah kuma ya karbi addu’arsa, ya umarce shi, shi da sahabbansa da su kalli ka’aba a sallarsu. Sannan Allah (SWT) ya fada masa cewa jahilai da wawaye daga cikin Ahlil kitabi za su rinka sukarku da cewa, me ya sa a da suna kallon arewa, watau nahiyar Sham, amma suka dawo suna kallon nahiyar kudu, watau ka’aba? Allah ya ce: (Da sannu wawayen mutane za su ce: “Mene ne ya sa su juyawa su bar alkibilar da a da suke a kanta?” Ka ce: “Gabas da yamma na Allah ne, Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.”) [Bakara: 142]
2. To sai kuma Allah (SWT) ya ce bayan wannan ayar: (Kamar haka ne Muka sanya ku al'umma tsaka-tsaki (zababbu) don ku zamo masu shaida ga mutane, kuma Manzo ya zamo mai shaida a gare ku. Kuma ba Mu sanya alkiblar da ka kasance a kanta ba sai don Mu bayyana wanda yake biyayya ga Manzo da wanda zai ja da baya (ya bijire). Kuma lalle wannan babban lamari ne sai dai ga wadanda Allah Ya shiryar. Kuma Allah ba zai taba tozarta imaninku ba. Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai jin kai ga mutane.) [Bakara: 143]
3. Allah (SWT) ya yi wannan maganar ne da farko da sahabban Annabi (ο·Ί) kafin wasu su shiga. Saboda su ne suke a halarce lokacin da ayar ta sauka, don haka ba zai yi wu a tsallake su ba, sannan wadanda suka zo a bayansu su shiga.
4. Don haka Allah (SWT) ya nuna ya dora Annabi (ο·Ί) da sahabbansa a kan tafarki madaidaici a karhen ayar farko, watau fadarsa: (Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.”) [Bakara: 142]
5. Watau yayin da ya dora su a kan fuskantar ka’aba a maimakon baitul makdis ya dora su ne a kan tafarkinsa madaidaici. To kamar yadda ya dora su a kan wannan tafarki madaidaici, to hakanan kuma ya zabe su ya sanya su suka zama al’umma adila a cikin sauran al’umomi don su yi shaida.
6. Don haka sahabban Annabi (ο·Ί) sun samu wannan shaida ta zama adalai kafin wani na bayansu ya samu, su ne ma’auni na dukkan wani wanda zai zo a bayansu. To ya aka yi suka samu wannan matsayi? Dole sai da suka hada sifofin mutumin da ya cancanta ya yi shaida. Don haka duk wanda ya zo daga baya yana son ya shiga karkashin wannan aya, to sai ya siffantu da abin da suka siffantu da shi kafin ya shiga karkashinta.
7. Wannan ya nuna cewa, sahabban Annabi (ο·Ί) sun samu yabo daga Allah (SWT) kafin ma wani ya zo yana ba su kariya, don haka sun samu ta’adili daga Allah (SWT).
8. Babbar hikimar dake cikin wannan ita ce, kasancewar su ne za su zauna a gaban Annabi (ο·Ί) su ji sakon da ya zo da shi, domin su isar wa wadanda za su zo daga baya. To ka ga ashe idan ya kasance su ne za su yi dakon wannan amana, watau amanar Alkur’ani da amanar sunnar Annabi (ο·Ί) da amanar rayuwarsa da yadda ya tafiyar da ita, gaba daya duk su za a dorawa, to babu shakka yana daga cikin hikima ya zamanto sun samu wata tarbiya ta musamman da zai zamanto sun rike wannan amana kuma sun isar da ita don wannan addini ya ci gaba.
9. Ba zai yi wu a saka wani ya yi shaida ba alhali makaryaci ne ko mayaudari ne ko marar amana ne. A cikin dukkannin al’amari ko da mutum biyu ne ko uku ba za su dauko shaida wanda suka san cewa makaryaci ne ba, sai dai su dauko mai amana da gaskiya.
10. To idan ya zamana a mu’amala ta yau da gobe, wadda ta hada mutum da mutum a harkar duniya ya zamana ana son shaidar da za a saka ya zama amintacce, kamar yadda Allah ya fada dangane da harkar bashi: (kuma ku kafa shaidu biyu cikin mazajenku; kuma idan ba su kasance mazaje biyu ba, to sai a nemi namiji daya da mata biyu daga shaidun da kuka yarda da su…) [Bakara: 282]
10. Idan ya zamanto a harkar bashi da ta shafi mutum biyu rak, wdda idan da za a samu matsala su biyu kawai za ta shafa, amma duk da haka Allah ya ce a saka shaidun da aka yarda da su, to ina ga abin da yake addinin Allah ne? Addinin da yake shi ne addinin karshe da ya zaba al’umma ta bautawa Allah da shi, kamar yadda ya ce: (A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku.) [Ma’ida: 3]
Da fadinsa: (Duk kuma wanda ya nemi (bin) wani addini ba Musulunci ba, to har abada ba za a karba daga gare shi ba, kuma shi a lahira yana cikin hasararru.) [Ali Imran: 85]
11. Addinin mai irin wannan girma, addinin da babu wani addini da ya kai shi; addinin da ya shafe dukkanin addinai gaba daya, a ce kuma wadanda za su zama shaidu ko wadanda za su dauko dakon addinin, a cikinsu akwai bara-gurbi ko marasa gaskiya masu cin amana, ko wadanda ba su son zaman gaskiya da Manzon Allah ba. Babu shakka wannan wani abu ne wanda hankali da tunani ba zai karba ba. Idan ba haka ba sai mu dauka cewa Allah ya fifita sha’anin bashi a kan sha’anin addini gaba daya, saboda ga shi bashi ya ce, a nemi shaidu yardaddu. Wannan kuwa lafiyayyen hankali ba zai taba karbar wannan ba.
https://t.me/miftahul_ilmi