INA SON CIKAKKEN BAYANI AKAN KUL'I

*_INA SON CIKAKKEN BAYANI AKAN KUL'I?_*

                             *Tambaya*
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Malam ina so amin cikakken bayani akan kul'i?

                                  *Amsa*
Wa'alaikum assalam, Khul'i shi ne mace ta fanshi kanta daga wajan mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa mijinta a hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan musulunci.

Ya halatta à shariar Allah mace ta yiwa miijnta Kul'i in har ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokinsa na aure ba, kamar yadda aya ta (229) a suratul BAKARA ta tabbatar da hakan.

À zance mafi inganci Kul'i yana saukar da saki daya, saidai yana nisanta mace da mijinta ta yadda ba zai iya sake zama da matar ba, sai in ya bayar da SADAKI sannan an kara daura sabon aure.

Allah ne mafi sani

20/06/2017

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)