_*Tambaya:*_
Idan mace mijinta yana cutar da,ita kuma cutarwa mai tsanani yahalatta tabuqaci arabasu
_*Amsa:*_
_To, 'yar uwa, a shawarce dai kamata ya yi ta kai kukanta wajen iyayensu ko waliyyanta a kan a yi masa nasiha ya daina cutar da ita da yake yi. Hakika hakan shi ya fi maslaha fiye da a raba auren. Allah (ﷻ) Yana cewa:_
_*”وَإِنِ امرَأَةٌ خَافَت مِنۢ بَعلِهَا نُشُوزًا أَو إِعرَاضًا فَلَا جُنَاحَ عَلَيهِمَآ أَن يُصلِحَا بَينَهُمَا صُلحًا وَالصُّلحُ خَيرٌ ....“* [النساء: ١٢٨]_
_Ma'ana: *“Kuma idan wata mace ta ji tsoron Taƙadarci daga mijinta, ko bijirewa, to babu laifi a gare su su yi sulhu a tsakaninsu kyakkyawan sulhu. Kuma Sulhu shi ya fi alkhairi....”* (An-Nisa: 128). Wato yin sulhu ya fi rabuwa alkhairi._
.
_'Yan uwa maza ku sani, matayenku suna da hakkoki a kan ku, mu ji tsoron Allah mu daina cutar da matayenmu. Allah (ﷻ) Ya ce:_
_*” وَلَهُنَّ مِثلُ الَّذِى عَلَيهِنَّ بِالمَعرُوفِ“*_
_*“Mata suna da haƙƙi a kan maza irin wanda su (mazajen) ke da shi a kansu na alkhairi (a cikin Shari'ah daga kyan zama da rashin cutarwa).”* (Baqarah 228)._
_Idan mace ba ta son mijinta, kuma ba ta son Cigaba da zama da shi, to ya halatta ta fanshi kanta daga gare shi. Allah (ﷻ) Yana cewa:_
_*“Idan kun ji tsoron cewa ba za su tsaida dokokin Allah ba, to babu laifi a gare su cikin abin da ta fanshi kanta da shi."* (Baqarah 229)_
_Don haka 'yar uwa! Yin sulhu shi ne mafi alkhairi, ta nemi waliyyanta domin a sulhunta ne ba don a kashe auren ba. Saidai kuma idan cutarwarsa ta yi yawa kuma an yi masa nasiha be gyara ba._
_Wallahu a'lamu._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_
_*🧕🏽Islamic Post Women.*_