_*Tambaya:*_
Assalamu alaikum
Dafatan malam na lafiya? Shin ya halasta da a sa zobe a hannu dama?
_*Amsa:*_
_Wa'alaikumusallamu Warahmatullahi._
_Eh, ya halatta mutum ya sanya zobe a hannunsa na dama._
_Domin an karbo hadisi daga Anas Ibn Malik (r.a) ya ce: “Lallai Manzon Allah (ﷺ) ya sanya zoben azurfa a damarsa cikinsa akwai mahadar zobe na irin na habasha, ya kasance ya kan sanya mahadar zoben ta bangaren tafin hannunsa)). Muslim._
_Saboda haka babu laifi sanya zobe a hannun dama, domin Annabi (ﷺ) ma ya sanya._
_Wallahu a'lamu._
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*🕌Islamic Post*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_
Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.