Rikichin JININ HAILA

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum fatan alkairi inadatabbaya

Nafarkode jininhaila Ada yanamin kwana 7 saina yi sallah yanzu kuma yajazza idan yazo kwana 4  sai ya tsaya cak nayi kwana 2 babu jini sannan yadawo Kwana 1 yazama 7 sannan nayi sallah to abin da yake damuna Kwana 2 da babu jini zan yi wanka nayi sallah ko zan bari saiya dawo kwana 1 kafin nayi sallah?

_*Amsa:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullah._

_'Yar uwa tun da kin san kwanakin al'adarki, to za ki zauna gwargwadon kwanakin al'adarki, za ki bar Sallah da azumi, ki ba wa kanki hukuncin mai haila. Idan kwanakin al'adarki sun kare, wato kwanaki bakwai din, sai ki yi wanka ki ci gaba da ibadunki._

_Dalili shi ne fadin Manzon Allah (ﷺ) ga Ummu Habiba: *“Ki zauna gwargwadon kwanakin da hailarki take tsare ki, sannan ki yi wanka ki yi sallah”* Muslim ya ruwaito shi._

_Ita Ibadah ba a yinta cikin kokonto, kin ga kuwa za ki kokonton kila akwai yiyuwar jinin zai iya dawowa a cikin kwanaki biyun tunda ba haka al'adarki ta saba kasancewa ba. Don haka ni a tawa fahimtar, za ki zauna har kwana bakwai su cika sannan ki yi wanka, ki Cigaba da Ibadah._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Post a Comment (0)