HUKUNCIN AZUMIN NAFILA RANAR ASABAR

_*Tambaya:*_

Assalamu alaikum dafatan malam na lfy malam ya hukuncin yin azumin nafila ranar asabar kamar sutta shawwal?

_*Amsa:*_

_Wa'alaikumussalamu Warahmatullahi Wabarakatuh._

_A mafi ingancin Zance gaskiya ya halatta a yi azumin nafila a ranar Asabar, domin hadisin da yake hani a kan yin azumi ranar Asabar malamai sun ce akwai kuskure a ciki, wasu ma suna ganin cewa hadisin karyane domin ya ci karo da wasu hadisan._

_A hadisin Abu Huraira (r.a) wanda Bukhary da Muslim suka ruwaito, Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *“Kada dayanku ya yi azumi a ranar Juma'a sai dai idan ze azumci yinin da ya gabace shi, ko wanda ke gabanshi”* Yinin da yake gaban na Juma'a a shi ne yinin ranar Asabar, wannan ke nuna cewa ya halatta mutum ya yi azumin nafila a ranar Asabar._

_Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya halatta irin azumin Annabi Dawud (A.S) Wanda mutum zai yi yau ya tsallake gobe, kuma duk wanda ze yi irin wannan azumin dole ne Asabar ta shigo ciki._

_Don haka zance mafi inganci shi ne ya halatta mutum ya azumci yinin Asabar idan ta shigo jerin ranakun azuminsa, kamar idan ya yi azumi ranar Juma'a, to babu laifi ya yi ranar Asabar._

_Wallahu a'lamu._

_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_*08166650256.*_

_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_

Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Post a Comment (0)