TARIHIN ASALIN HAUSA DA HAUSAWA

Taskar Hikayoyi
Tarihin Asalin Hausa da Hausawa.
Gudummuwa daga Maigirma farfesa Ibrahim Malumfashi.
GA TAWA GUDUNMUWAR!
Batun gaskiya shi ne, ba Bayajidda ko Abii Yazid ne ya
zo kasar Daura ba! Domin ba yadda za a yi ya kasance
haka in ba fatalwa ba ce shi! Abii Yazid bai taka kasar
Hausa ba. Ba kuma Balarabe ba ne in ma ya zo kasar
Hausa kamar yadda tatsuniyar Palmer ta samar, domin
shi Barbar ne. Ba kuma mutumin Bagadaza ba ne a
kasar Irak, mutumin yankin Tunisiya ne, haifaffen
yankin Afirka Ta Yamma a yanzu. Bisa wannan tunani
muna iya cewa ba shi ne ya zama Sarkin Daura a
shekara ta 1,000 da muka gani a cikin littafin Palmer
da aka buga a 1928 ba. An dai kirkire shi ne a cikin
littafin Palmer na biyu a shekarar 1936. Bisa wane
dalili? Shi ne ba za a iya tabbatarwa a halin yanzu ba!
Mun dauki wannan dogon lokaci muna bin wannan
tarihi da kuma tattace duk wani bayani domin mu kara
tabbatar da rashin ingancin wannan taririhi, duk da
cewa mun ce ana iya samun kanshin gaskiya a cikin
taririhin, amma ba wani bincike da ya nuna cewa Abii
Yazid ko Bayajidda ne ya zo kasar Hausa ya auri
Daurama. Kenan akwai tababa ga dukkan bayanan da
ke tattare da taririhin.
Saboda haka abin da za mu yi shi ne, mu bi tarihin
wadanda suka kasance ginshikan wannan tarihihi, mu
ga shin su din ma sun kasance gaskiya ko kuwa dai
abin da aka saba fada ne na kunne-ya-girmi-kaka,
wanda yawanci bai zama gaskiya ba?
Mu soma da ita Daurama, bayanai da binciken masana
ya nuna cewa ita kan ta ba ta da wani tsayayyen
tarihin asali. Wasu masu bincike sun ce sunanta na
asali Fatima, ke nan musulma ce, amma kuma daga
irin yadda bayanai suka zo game da ita, bai yiwuwa a
ce musulma ce, domin kuwa al’adun da ake a kasar
Daura a zamaninta, ba na Musulunci ba ne. An kuma ce
wai a lokacin da aka haife ta ba ta jin Larabci ko
Tamashek, haka ta girma, shi ya sa ma wasu daga
cikin mutanen kasar suka ce ai ba ta jin Hausa a cikin
cikin harshen mutanen yankin na Larabci, wai daga nan
aka sami harshen Hausa.
Wannan ma bai iya zama gaskiya, domin da Larabci
mutanen nata suka yi magana, ita kuma me ya hana ta
iya yin Larabcin? Haka kuma wasu masana sun ce ai
sunanta na asali shi ne Dauratu, kuma diyar maharba
ce, wadda ta nakalci tsafe-tsafe, ke nan Fatima ba ita
ce Dauratu ba, domin tsafi bai tafiya da Musulunci, sai
fa in gamade ake yi. Wasu masanan ma cewa suka yi
ai ita da kanta zuwa aka yi da ita Daura ba ‘yan kasar
ba ce, domin wai baiwa ce daga cikin bayin sarakunan
Daular Bornu ce. Wai sayo ta aka yi, aka zo da ita
Daura, har ta zama wata jaruma ta mulki jama’ar
kasar. Kenan ba abin da ya hada ta da sauran Daurama
9 da aka yi kafin zuwanta Daura, kila su ma duk baki
ne, ba ‘yan kasa ba!
Idan kuma muka koma ga shi kan sa Karba-Gari, dan
kuyangar Daurama, za a ga cewa shi ma dai bai da
cikakken bayanin asali. Wasu na cewa ai bawa ne daga
Bornu ne shi ma. Wasu suka ce ai Bakibde ne. Wasu
kuma suka ce ba a ma yi shi ba, shaci-fadi ne.
Shi kuwa Bawo dan Daurama, daga sunansa aka fara
samun tababa na ko shi ma da ne ba bawa ba. Wasu
masana sun ce ai sunan nasa na asali Bawa ne, ke nan
bawan mutanen Bornu ne shi ma, kamar ita Daurama.
Wasu suka ce ai shi ma Bakibde ne daga Masar. Wasu
kuma suka danganta shi da Babar na Arewacin Afirka.
Daga binciken masana, ba wani da ya ce haihuwar
Bawo aka yi Daura kamar yadda tarihihin Bayajidda ya
nuna, sai dai a ce zuwa ya yi da girmansa.
Shi kuwa Bagauda da aka ce ya sari sabon birnin Kano,
shi ma an nuna cewa zuwa ya yi da girmansa, kuma
sunan Bagauda lakabi ne, ba sunan yanka ba, shi ya
wasu ke ce da shi Bagoda, ko kuma Bakoda, ko kuma
mutumin da ya fito daga al’ummar Copitcs, Kibdawa,
kenan Bakibde ne, wato mutumin kasar Masar ne shi
ma.
Ke nan Bagauda ba shi ne asalin Kano ba, ba kuma dan
Bawo ba ne ko jikan Bayajidda, wani dakaren ne can
daban, kila daga cikin dakaru ko ‘ya’yan Bayajidda ko
Abii Yazid da muka yi bayani can baya! Me ya sa muka
ce haka? Ko a cikin Tarihin Sarakunan Kano da ake
bayanin Bagauda cewa aka yi a daidai shekara ta 1,000
Bagauda ya yi zama a wani gari da ake kira Adirani har
tsawon shekara biyu, daga nan ya wuce zuwa wani gari
da ake ce da shi Barka, nan ma kusan shekara biyu ya
yi, daga can sai garin Sheme, a kasar Kazaure, inda
daga can ne ya isa Kano. A Kanon ne ko dai shi ko
danginsa suka yi mulki na kusan tsawon shekara 60.
Tambayar da za a iya yi ita ce, shin ana haihuwarsa ne
ya bar gida don mulkin wadannan kasashe? Ko kuwa
dai sai da aka dauki tsawon lokaci? An yi wannan
tambaya ne ganin cewa yawancin tarihe-tarihen da ake
da su game da Abii Yazid ko Bayajidda da zuwansa
kasar Daura daga shekara ta 1,000 ko 1,100 suka fara.
Da yake kuma ba wani takamaiman lokaci ko rana ko
wata ko kuma shekara da aka nuna cewa sun iso kasar
Hausa ko Daura, ba mai iya cewa ga daidai lokacin da
aka haife su ko yadda suka girma har suka fice daga
Daura ko Biram domin zama asasin Hausa Bakwai da
Banza Bakwai. Abin da muka riga muka ayyana tun can
baya daga nazarce-nazarcen masana shi ne, wanda ake
kira Abii Yazid ko Bayajidda ya dai rasu tun a shekarar
947, saboda haka shekara 53 ko 153 ke nan iyalansa
ko dakarunsa suka yi bisa hanya kafin su shigo Daura,
idan har sun shigo din, har aka yi aure da Daurama.
Akalla ana neman shekara kafin a haihu, idan kuma an
haihu (wato su Karba-Gari da Bawo), ana bukatar a
girma, a zama mutane kafin a hau kan gadon sarauta.
Idan mun dauki shekarun girma daga 16 zuwa sama, ke
nan akalla ‘ya’yan za su kasance ‘yan shekara 18 kafin
su yi aure da haihuwa da hawan gadon sarauta. An ce
Bawo ya haifi ‘ya’yan nasa su shida (duk da ba mu san
wane ne na farko ba) cikin su akwai Bagauda, akalla
shi ma zai yi shekara 18 kafin ya fita watangaririya
zuwa wasu sassa na duniya. Idan kuma muka bi tafiye-
tafiyen Bagauda zuwa Adirani da Barka da Sheme, inda
akalla ya yi shekara 6, a daidai lokacin da ya isa Kano
yana da shekara 24 ke nan. A nan kuma shi da
iyalansa da magada sun yi mulkin shekara 60, za mu ce
ke nan daga shekara ta 1,000 ko 1,100 zuwa karshen
mulkin Bagauda a Kano, an sami shekara 102. Kenan
idan tarihin daidai ne, karshen mulkin Bagauda a Kano
zai kama a shekara ta 1102 ko1202, wanda daga
dukkan bincike da hannu ya kai gare su, ba hakan ba
ne.

Post a Comment (0)