MENENE INGANCIN ALWALAR WANDA YA/TA SANYA HAKORIN MAKKA?



MENENE INGANCIN ALWALAR WANDA YA/TA SANYA HAKORIN MAKKA?
:
*TAMBAYA*❓
:
Aslm mallam ya alamura? Don Allah malam ina tambaya game da masu sanya hakorin maka akance suna barin lam’a agun alwala wato hakorin bai samun wankuwa lokacin alwala. Nagode
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Duk wanda ya zo da wannan zance ya zo da abun mamaki, a shar'ance da hankalce. Domin kuwa ita shara'a tace a kurkure baki ne, ba a wanke haƙori ba. Babu wani Mallami daga cikin Mallamai da ya fassara madhmadhatu (المضمضة) da wanke haƙori. Ma'anar wannan kalma shine gudanar da ruwa cikin sassan baki, ba wanke haƙora ba. Yaa Salaam. 

Wannan neman fitina ne kawai, domin ko da ace sun bar lam'a a haƙori, toh ba ta lazimta sake alwala domin kurkure baki baya cikin wajibai ko rukunnan alwala.

Shaidan ne ke nema ya saka maku shubuha a cikin mafi girman al'amarin addinin ku baya shahada.

Mu sani cewa, shi haƙori shara'a tace a goge shi ne, shi yasa tayi umarni da asuwaki. Ma'ana asuwaki daban da kurkurar baki. Wanda kuma bai yi asuwaki ba, alwalar sa ta inganta.

Wallahu ta'ala a'lam.

 *_Amsawa_* :
 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)