SAƘO NA MUSAMMAN ZUWA GA MASOYAN JARUMI SALMAN

SAƘO NA MUSAMMAN ZUWA GA MASOYAN JARUMI SALMAN KHAN

Bismillahir Rahmanir Raheem.

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.

Ƴan Uwana Masoyan Jarumi Salman Khan ina muku Barka da warhaka, tare da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.

A cikin ƴan kwanaki huɗu zuwa huɗu da suka gabata na fuskanci cewa taƙaddama ta ɓalle a tsakanin ku dangane da cewa SHIN SALMAN KHAN YA TAƁA YIN SUMBA A CIKIN FIM?, abin da ya jawo cece kuce sosai inda wani ɓangare mafi girma na Masoyansa suke ƙaryata cewa bai taɓa yi ba, Yayinda wasu ƴan tsiraru su kuma suka dage akan cewa ya taɓa yi ko yana yi da dai Makamantan su. To, a zahiri dai wannan taƙaddamar cikin gida ce, kuma bai kamata in shiga ba kamar yadda kuma bai kamata in koma gefe in yi dariya ba, domin teburin babu ta yadda baya iya juyawa sai dai in Allaah ne bai nufa ba.
Don haka sai na yanke shawarar yin amfani da matsyina na Maƙwabci domin na aiko da wannan saƙon a matsayin shawara ba umurni ba. Domin kuwa bani da iko akan kowa daga cikin ku, kuma yana daga cikin haƙƙin Maƙwabtaka dama in kaga abinda zai cutar da Maƙwafcinka to kayi iya ƙoƙarin ka wajen ganin ka tseratar da shi daga wannan abin cutarwar. Kuma wannan abun ka iya janyo muku zolaya, zargi da kuma zagi daga waɗanda basu san me ake nufi da soyayyar Jarumi ba. 

Dangane da wannan taƙaddama da ake ta yi wadda kowane ɓangare sun kawo hujjoji tare da ƙalubalantar juna da dai sauran abubuwan da suka wakana. Ni ina ganin kamar ita Kalmar Sumba (watau Kiss) ɗin ce ba'a Fahimce ta ba a matakin farko. Ni a tunanina, da za'a fahimci Ma'anar kalmar da kyau, to da komai zai zo da sauƙi domin daga nan babu buƙatar a ja magana indai ba dama da wata Manufa ake yi ba. Hakan yasa na yanke shawarar aiko muku da taƙaitaccen bayani dangane da wannan Maudu'i tare da fatan zai haskakawa waɗanda basu fahimta ba hanyar da waɗanda suka fahimtar suka bi domin su ma su fahimta.

   Menene Sumba (Kiss)?

Sumba shi ne taɓi wanda mutum kan yi da laɓɓansa zuwa ga wani mutum ko kuma wani abu. Sumba ya rabu izuwa kashe-kashe masu yawan gaske, kowanne kuma ya danganta ne da irin al'adun mutanen da ke yankin da wani kaso daga cikin kashe-karshen ya faɗa. 
Misali; a ɗabi'a irin ta Nasarawa, suriki ma kan iya sumbatar surikarsa a fili. Yayinda a wurin Hausawa kuwa, tun gabanin zuwan musulunci, mata da miji ma ba sa iya sumbatar juna su a bainar jama'a. Shi sumba yana aika saƙo ne zuwa ga wanda aka yiwa, kuma kamar yadda ya rabu kashi-kashi, haka ma saƙonnin suka rabu. Daga cikin saƙonnin da sumba ke aikawa akwai irin su So, Ƙauna, Sha'awa, Girmamawa, Gaisuwa, Abota/ƙawance d.s. 

Wani bincike da aka gudanar ya Sumba shi ne aiki na biyu da mutanen Amurka suka fi aikatawa a kullum bayan riƙe hannuwa kuma kaso 85% cikin ɗari na matasa masu shekaru 15 zuwa 16 sun taɓa yin sumba. Sai dai wasu kayan Adabi sun bayyana cewa har yanzu akwai mutane masu yawa waɗanda ba sa yin sumba sam a rayuwar su.

Taƙaitaccen Tarihin Sumba. 
 
Masana a Fannin ilimin halayyar Ɗan Adam sun kasu gida biyu dangane da asalin sumba. Wasu sun ce wai sumba Ɗabi'a ce da kan zo wa mutum a matsayin bazata ko kuma bisa niyya. Yayinda wasu kuma suka ce sumba ya samo asali ne daga ciyarwa irin wacce iyaye mata ke yiwa yaransu ta hanyar tauna abinci su basu ta baki. 
Masani a fannin ilimin halayyar Ɗan Adam kuma ƙwararre a Fannin ilimin sumba wato Vaughn Bryant yace bayanai mafiya daɗewa da aka fara samu dangane da sumba ko wani abu makamancin haka sun fito ne daga Vedas, wasu rubututtuka na Sanskrit waɗanda suke koyar da mabiya Addinin Hinduism, Buddhism da kuma Jainism kimanin shekaru 3,500 da suka gabata. 

Haka kuma an samu sunan leɓe da sumba a cikin tsofaffin rubutattun waƙoƙin Sumeria. Sannan masu bincike a fannin kayan tarihi sun tabbatar da samuwar bayanai da suka bayyana sumba a cikin kayan tarihin da suka haƙo a birnin Misra (Egypt 🇪🇬) . 
Hallau kuma dai an samu wasu muhimman bayanai da suka danganci sumba a cikin Labaran almara na Hindu wato Mahabharata.
Masana waɗanda suka karanci ilimin sumba sun ce yin sumba ya samu haɓaka sosai a duniya tun bayan da Alexander the Great tare da mayaƙansa suka yaƙi wani ɓangare na Punjab da ke arewacin India a 326 BC.

Rumawa (Romans) sun taimaka Matuƙa wajen yaɗa ɗabi'ar sumba a yankunan Yuropiya da kuma arewacin Ifrikiya. Rumawa saboda son yin sumba da suke yi yasa har tattaunawa suke yi dangane da ire-iren sumba a bainar jama'a. Sumba irin wanda ake yi a hannu ko a kumatu shi suke kira da osculum. Wanda ake yi da baki kuma amma laɓɓa a rufe shi suke kira da basium, shi wannan a tsakanin ƴan uwa ake yinsa. Shi kuma Sumbar soyayya shi ake kira da suavium.
An fara karantar Sumba a matsayin gurbin karatu mai zaman kansa ne a cikin ƙarni na goma sha tara, kuma sunan da ake kiran wannan karatu shi ne philematology. Mutane da yawa sun yi karatu a wannan fage, fitattu daga cikin waɗanda suka yi wannan karatu sun haɗa da Cesare Lombroso, Ernest Crawley, Charles Darwin, Edward Burnett Tylor da Elaine Hatfield. 

Rabe-Raben Sumba 
 
Fitaccen masanin sumba wato Kristoffer Nyrop ya bayyana cewa sumba ya kasu izuwa kashi daban-daban. Daga cikin su akwai Sumbar soyayya, Sumbar ƙauna, Sumbar abota, Sumbar girmamawa, Sumbar lumana d.s 
Sai dai kuma yace, rabe-raben sumba yana banbanta daga wuri zuwa wuri dangane da irin al’adun mutanen wurin, hakan yasa na wasu ya fi na wasu yawa. Misali, Faransawa suna da rabe-raben sumba har kashi 20 Yayinda Jamusawa su kuma suke da 30.

* Sumbar Soyayya. 

Duk da cewa sumbatar laɓɓan juna a tsakanin mutane biyu ya riga ya zama ruwan dare a wannan zamani a matsayin alama ta soyayya ko ƙauna, Al'ummomi da yawa basu san da wannan ɗabi'ar ba sai ta hanyar turawan Yuropiya. 
Shi Sumbar soyayya sumba ne wanda masoya suke yiwa junansu a duk lokacin da suka haɗu ko zasu rabu ko kuma lokaci bayan lokaci idan suna tare. Su kan yi Hakane kuma domin nunawa juna soyayyar da suke yiwa junansu. Shi irin wannan sumba akan yi shi baki da baki ne ba tare da Shamaki ba. 

* Sumbar Sha'awa. 

Wannan shi ne irin Sumbar da mutane suke yiwa junansu Yayinda sha'awar su ta motsa ko kuma domin motsa sha'awar. Banbancinsa da Sumbar soyayya shi ne, a mafi yawancin lokutta an fi daɗewa wajen yinsa, sannan an fi tsanantawa. 

* Sumbar Ƙauna 

Shi Sumbar ƙauna ya banbanta da na soyayya wanda masoya ne ke yiwa junansu. Shi wannan Sumbar duk da cewa masoya suna yiwa junansu irin sa, basa yi har sai soyayyarsu ta rikiɗe ta koma ƙauna. Misali ƙarara shi ne irin Sumbar da Mahaifa ke yiwa Ƴaƴansu. Banbancinsa da na soyayya ko sha'awa shi ne, ba'a yinsa don jin daɗi ko samun wata biyan buƙata, kawai ƙaunar ce ke gudana ta cikinsa. 

* Sumbar Abota ko Ƙawance 

Wannan sumba ne da abokai kan yi wa juna haka ma ƙawaye kan yiwa juna. Bugu da ƙari kuma, ahali biyu ma su kan yiwa juna irin sa. Shi wannan sumba yawanci a kumatu ake yinsa, duk da yake dai a kwai wasu yankuna da suke yin baki da baki. Akan yi shi ne domin nuna kulawa a tsakanin abokan ko ƙawayen. 

* Sumbar Girmamawa. 

Tarihi ya nuna cewa, tun tale-tale ana amfani da sumba a matsayin girmamawa ta hanyoyi da dama. Shi irin wannan sumba akan yi shi a ƙafa ko hannu ko a tufafin wanda ake girmamawa. 

* Sumbar da ta shafi Addini. 

Wanna sumba ita ce irin Sumbar da mabiyan addinai ke yiwa abubuwan da suka shafi harkar addinansu, ko kuma a wasu wuraren wa ababen bautar kai tsaye. Shi ma wannan kai tsaye ake ɗaura laɓɓa akan abinda ake sumbatar. 

* Sumbar Lumana ko zaman lafiya. 

Shi wannan Sumbar ana yin sa ne domin Samar da lumana a tsakanin mutane biyu ko tawaga biyu. A can dauri, Mayaƙa ma kan yi irinsa domin nuna tabbacin sulhu a tsakanin su. Hallau dai, sarakuna kan yi irin wannan sumba domin nuna aminci da juna kan zaman lafiya. A wasu wuraren ma shugaba kan tursasawa abokan hamayya sumbatar juna bayan ya shirya su. Shi irin wanna sumba ana yin sa ta leɓe da leɓe, ko a kumatu ko kuma a hannu. 

Ƙarin Bayani Dangane Da Sumba. 
 
Donald Richie ya bayyana cewa a Japan, kamar yadda yake a birnin Sin, sun ɗauki sumba a matsayin alama ce ta sha'awa kawai, kuma yin sa a fili rashin kunya ne. Abin har yayi tsamari ta yadda mutanen birnin Sin suna ɗaukar duk wacce take Sumbatar Namiji a fili kai tsaye a matsayin karuwa. 

A Rayuwar ƙasashen gabashin duniya ta yau, sumba ya danganta ne da irin wuri da kuma mutanen wurin. A yammacin yankin Asiya, sumbatar leɓe a tsakanin maza ko mata alama ce ta gaisuwa da girmamawa, amma a gabashi da kuma kudancin Asiyan, a tsakanin mata ne kawai ake yin hakan, maza basu cika yi ba. 

A Ƙasar Hausa kuwa, sumba a bainar jama'a an ɗauke ta ne a matsayin alama ta rashin Tarbiyya da nuna cewa mutum ya kai ƙololuwar ƙwarewa a rashin kunya. 



SUMBA A CIKIN FINA-FINAI 

Sumbar soyayya da ya fara bayyana a jikin majigi ya bayyana ne a cikin wani fim ɗin Amurka mara magana mai suna THE KISS a 1896. Sumbar da aka yi a cikin shirin ya ɗauki tsawon daƙiƙa talatin ne wanda hakan ya haifar da gagarumin cece-kuce tare da samun Zafafan kalamai daga masu kare Tarbiyya da ɗa'a na birnin New York. Wani daga cikin masu sharhin Fina-Finai na wancan lokacin ma dai cewa yayi: "wannan abun Allah wadai ne, irin wanda ya cancanci a kira wa ƴan sanda. 
Daga nan ne sai matasa dake kallon irin waɗannan Fina-Finan suka fara kwaikwayon Jaruman soyayya irin su Ronald Colman da Rudolph Valentino. Ƴan Fim mata da yawa a wancan loton sun zama Shahararrun Jarumai ne saboda iya nuna jin daɗin su yayin sumba a cikin Fina-Finai. Daga cikin su akwai Nazimova, Pola Negri, Vilma Bánky da kuma Greta Garbo. 

Sumba irin ta leɓe-da-leɓe ba'a fara yin ta ba a cikin Fina Finan Bollywood har sai zuwa ƙarshen 1990s duk kuwa da cewa ana sane da shi kuma an shirya wa Yinsa tun lokacin da aka kafa Bollywood. 
Wannan kuma ita ma magana ce mai zaman kanta tun da yake bayanai sun nuna cewa sumba ta bunƙasa kuma ta yaɗu ne sosai da sosai a India. Wataƙila hakan yasa tun da aka fara mutane suka amshi abin hannu biyu. Sumba mai tashi ita ce irin Sumbar da ake haurawa zuwa ga wanda ake so, irin wannan sumba ce aka fi yi a cikin Fina-Finan India na farko-farko, kuma har yanzu ana yin sa a cikin Fina Finai. 


A Fina-Finan Japan na farko-farko, nuna Sumba ko wani abu da ya shafi saduwa ko sha'awa abu ne da ke ƙunshe da Jimirɗa Matuƙa. A 1931, wani mai bada umurni ya taɓa yin coge ya sa wata fitowa da ake sumba a ciki har ta shallake masu tace Fina-Finai. Amma ana fara haska shirin a wani gidan haska Fina-Finai da ke Tokyo, nan da nan aka dakatar da shirin kuma aka ƙwamushe fim ɗin.

Dokar Yin Sumba 

Akwai doka mai tsanani a wasu ƙasashen, musamman ƙasashen musulunci. Misali, a Iran duk mutumin da aka kama shi ya Sumbaci wacce ba Muharramarsa ba ko ya taɓa ta, za'a yi masa bulala 100 in bai ci sa'a ba ma sai yayi yari. 
Haka ma a sauran ƙasashen musulunci dokar take. Duk da cewa ya halatta Ma'aurata da muharramai su Sumbaci junansu a fili (musamman a kumatu ga ƴan uwa), sumbatar waɗanda ba muharramai ba ka iya jawo wa mutum abinda bai yi tunani ba. Domin a 2007, gwamnatin Dubai ta ci tara tare da garƙame wasu mutum biyu a kurkuku saboda sun Sumbaci juna tare da yin runguma a bainar jama'a. 


A Ƙasar India, nuna soyayya ko ƙauna ta hanyar runguma ko sumba a bainar jama'a yana matsayin ta'addanci ne kamar yadda yake rubuce a sashi na 294 na Indian Penal Code, 1860 kuma hukuncinsa shi ne garƙamewa a magarƙama har na tsawon wata uku ko tara ko kuma duka biyun. Wannan dokar kuma har yanzu Ƴan Sanda da kotu na amfani da ita wajen ƙwamushe Masoyan da ke irin wannan aiki. Sai dai kuma a wasu sassa na Ƙasar, kotu kan yi watsi da irin wannan cajin. 


To idan mun Fahimci waɗannan bayanai, Tambaya ɗaya ce kawai Ta rage mana. Wannan tambaya kuwa ita ce: WANE IRIN SUMBA NE SALMAN KHAN BAYA YI A FIM? 

Na Barku Lafiya. 

<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ  
<••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring


Post a Comment (0)