*_AZUMI DA NIYYAR TUNKUDE BALA'IN BAMA-BAMAI?_*
*Tambaya*
Mal. Tambayar ita ce sarkin kano ya bada umarnin yin aximi guda uku saboda wannan iftila'in, Allah ya yaye mana shi, to yau ban yiba amma gobe ina so nayi shine nake so naji shin hakan ya samo asali ne a sunnah? nagode mal.
*Amsa*
To malam azumi yana daya daga cikin ayyukan alkairin da za'a iya tawassuli da su don neman afuwa a wajan Allah, saboda yana daga cikin manyan ibadu, kuma Annabi S.A.W ya kira azumi da cewa: Garkuwa ne, kamar yadda Nasa'i ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2217, sannan mai azumi idan ya yi addu'a, ana amsa masa, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2525, ka ga wadannan hadisan suna nuna cewa azumi zai iya tunkude musibar bama-bamai da 'yan ta'adda.
Saidai ware wasu kwanaki na musamman saboda haka ba shi da asali, a shari'a, amma dai ana iya umartar mutane da su dage da addu'a da kuma duk abin da zai kusantar da su zuwa ga Allah, don samun kariya, kamar yadda za'a iya ce musu su hada da azumi, amma ba tare da an ware musu wasu kwanaki na musamman ba, saboda babu dalilin da ya tabbatar da haka, kuma ba'a samu magabata suna yi ba.
Allah mafi sani.
19/12/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.