*_ANA YIWA IYALINA WANKAN JEGO, KO YA HALATTA?_*
*Tambaya*
Salam malam don Allah ka taimaka min ka amsa tambaya ta. ni dai mallam gaskiya hankali na ya ki kwantawa sakamakon al'adar wankan jego da ake yi a kasar hausa. iyalina ta haihu an kawo wata tana yi mata wanka, to malam ya hukuncin ya ke duba ga haramcin nuna tsaraici ga wani, don Allah malam ka daure ka amsa don hankalina ba'a kwance yake ba.
*Amsa*
To malam akwai hanyoyin na zamani wadanda za'a iya amfani da su ba tare da an yi wankan jego ba, kamar amfani da kwayoyi na asibiti, saidai idan ya zama babu makawa sai an yi wankan na jego kuma wata ce za ta yi mata, kamar ya zama haihuwar fari ce kuma babu halin da za'a iya sayen kwayoyi saboda talauci, to hukuncin wannan zai yi daidai da hukuncin likitan da take kula da lalurar mata, saboda shi ma wankan jego ana yinsa ne saboda magani.
A shari'ance ya wajaba ga likita ya yi taka tsantsan wajan kallon al'aurar mara lafiya ta yadda ba zai kalli wani bangare na al'aurar mara lafiya ba sai gwargwadon lalura, domin daga cikin ka'idojin shari'a shi ne duk abin da ya halatta saboda lalura, to ya wajaba a tsaya gwargwadon lalurar, wannan ya sa idan da zai kalli sama da haka, sai ya zama mai laifi a wajan Allah.
Al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa a zance mafi inganci, don haka mai wankan jego za ta kalli gwargwadon abin da ya wajaba ta kalla don tabbatar da lafiyar mai jego, idan kuma akwai hanyar da za ta bi ta yi mata wankan ba tare da kallon al'aurar ta ba, to wannan shi ne ya wajaba.
Allah ne mafi sani
15\12\2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.