BABA NA YA RASU ANA BINSA AZUMI

*_BABANA YA RASU ANA BINSA AZUMI, SABODA RASHIN LAFIYA_*

                              *Tambaya*
Dr. Allah ya yiwa mahaifina rasuwa be samu yin azimin watan  Ramadan ba sakamakon rashin lpy da yake fama da ita awannan lokacin.

Tambaya ta anan shi ne za'a ciyar ne ko za'a rama masa aximin ko kuma babu komai akansa duba da ayoyin da sukayi bayani akan hakan Allah ta'ala ya karawa mln lpy yasa agama lpy da kyakkywan karshe?

                                   *Amsa:*
Wa'alaikum assalam, in har rashin lafiyar ya zarce masa tun daga watan ramadanan har ya mutu, to ba za'a rama masa ba, saboda Allah ba ya dorawa rai abin da ba ta iya ba, amma idan ya samu saukin da zai iya ramawa, amma ya yi sakaci bai rama ba, wani daga cikin makusantansa zai rama maşa kamar yadda malamai suka fahimci haka a hadisin da Bukhari da Müslim suka rawaito, wanda Annabi s.a.w  yake cewa: "Duk wanda ya mutu ana binsa azumi,to waliyinsa zai biya maşa"  

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.

Post a Comment (0)