ADDU'AR RUKUU

*Addu'ar Ruku'u*

سُبْـحانَ رَبِّـيَ الْعَظـيم . (ثلاثَ مَرَّاتٍ)
Subhana rabbiyal-a'zeem (3)

Tsarki ya tabbata ga Ubangijin mai girma (Sau uku).

سُبْحانَكَ اللّهُمَّ رَبَّنَا وَبِحَمْدِك، َاللَّّهُمَّ اغْفِرْ لِي.
Subhanakal-lahumma rabbana wabihamdik, allahummagh-fir lee

Tsarki ya tabbata gare Ka, ya Allah! Ya Ubangijinmu, tare da godiya gare Ka. Ya Allah! Ka gafarta mini.

سُبُّوحٌ قُـدُّوسٌ، رَبُّ الْمَلاَئِكَةِ وَالرُّوحُ .
Subboohun kuddoos, rabbul-mala-ikati warrooh.

(Ubangiji) abin tsarkakewa, mai kubuta daga dukkan abin da bai kamace shi ba, Ubangijin Mala'iku da Jibrilu.

اَللَّهُمَّ لَكَ رَكَعْتُ وَبِكَ آمَنْتُ، ولَكَ أَسْلَـمْتُ، خَشَعَ لَكَ سَمْعِي، وَبَصَرِي، وَمُخِّي، وَعَظْمِي، وَعَصَبِي، وَمَا اسْتَقَـلَّ بِهِ قَدَمِي.
Allahumma laka raka'atu, wabika amantu, walaka aslamtu, khasha'a laka sam'ee, wabasaree, wamukhkhee, wa'azmee, wa'asabee, wamas-takalla bihi kadamee.

Ya Allah! Gare ka na yi ruku'u, kuma da Kai na yi imani, kuma gare ka na mika wuya. Jina ya yi kaskanci gare Ka, haka ma ganina da bargona, da kashina, da jijiyata, da kuma abin da kafata ke dauke da shi.
سُبْـحَانَ ذِي الْجَبَرُوتِ، والمَلَكُوتِ، وَالْكِبْرِيَاءُ، وَالْعَظَـمَة.
Subhana thil-jabaroot, walmalakoot, walkibriya, wal'azamah.

Tsarki ya tabbata ga (Allah) Mai dole, da mulki, da kasaitar daukaka, da girma.

____________________________________

*VIEW ONLINE V.O GROUP WHATSAPP*

@ummar fahad khan.
+2347032203744.

Post a Comment (0)