TAMBAYA TA 1078

*_TAMBAYA TA 1078:_* πŸ•‹πŸ•‹πŸ•‹πŸŒŸπŸŒ™ 
_DAGA ZAUREN_
*_πŸ“šMATA MUMINAI_*πŸ“š

Assalamu alaikum...malam ina so a mana takaitaccen bayani akan roqan yafiyan juna da akeyi kafin a azumi Wanda ake cewa yana daga cikin sunnah...sannan kuma akan adduan daukan azumin da ake ta yawo dashi a watsapp...Allah ya sakawa malam da alkairi

_*AMSA*_

_*WA'ALAIKUMUSSALAM....*_

Duk babu abinda ya tabbata na neman gafara na musamman dan zuwan Watan Ramadan asunnance. Hakama babu wata Addu'a ta daukan Azumi. Sabodahaka cewa hakan yanadagacikin Sunnah to wannan yima addini qaryane wanda kuma wannan kadai yana iya kai mutun zuwa ga shiga Wuta. Allah shi kyauta.

Sedai babu laifi koda wani lokaci anason mutun yazama yana qoqarin tuba ga Allah kuma da neman yafiya zuwaga 'yan'uwa Musulmi,saboda zunubi yakan hana Mutun yin ayyukan Lada kaman yanda Allah S.W yafadi haka agurare dayawa acikin Alqur'ani,misali:

 ```Lokacin da suka karkace,se Allah ya karkatar da zuciyarsu.``` _Suratu Saffi aya ta 5_

 ```Allah ya rufe zuciyarsu saboda abubuwan da suka aikata.``` _suratu Mutaffifin aya ta 14_ 

 ```Acikin zuciyarsu akwai ciwo se Allah ya qaramusu Ciwo``` _Suratu Baqara aya ta 10_

To duk irin wadannan ayoyin suna nuna mutun me zunubi yana iya rasa samun dacewa daga Allah saboda zunubinshi. Amma maganan cewa adunga neman tuba saboda zuwan Ramadan to wannan Bid'ace,kuma koda anyi tuba tare da yin Bid'a to Allah ma baze amsaba. 

_Allah yasa mudace._.
.
*_πŸ“Amsawa:-πŸ“š_*
_Malam Yusuf Salisu Kaduna_
_*~Via~πŸ“š MATA MUMINAI πŸ“š*_
*+2348108407420*
*+2347033537189*
*+2347035269582*
Domin kasancewa damu ta shafinmu na facebook se abi ta wannan hanyar a shiga ayi like
https://www.facebook.com/MATA-muminai-1841397762846865/

Ψ³Ψ¨Ψ­Ψ§Ω†Ωƒ Ψ§Ω„Ω„Ω‡Ω… ΩˆΨ¨Ψ­Ω…Ψ―Ωƒ Ψ£Ψ΄Ω‡Ψ― Ψ£Ω† Ω„Ψ§ Ψ₯Ω„Ω‡ Ψ₯Ω„Ψ§ Ψ£Ω†Ψͺ Ψ£Ψ³Ψͺغفرك وأΨͺوب Ψ₯Ω„ΩŠΩƒ.
Subhanakallahumma wabihamdika ash hadu anla ilaha illa anta astagfiruka wa'atubu ilaika".
Post a Comment (0)