TAMBAYA TA 32

*_Tambaya ta (392)_*
:
_Mālam ināsone ayimini takaitaccen bayani agame da menene Shirka??_
:
*_Amsa:_*
:
_Dangane da abinda yashāfi magana akan *Shirka Alal-Haƙīƙa* bayānine mai fāɗin gaske wanda bazai yiwu mu iya rubutāshi acikin ɗan ƙaramin lokacin damuke dashi ananba, to amma duk dahaka *In-Shā-Allāhu* zāmuyi ƙoƙari muɗanyi bayāni daidai gwargwadon abinda *yasauƙaƙa:*_
:
_Itadai *Shirka* itace mafi girman zunubin da *Bāwā* zai aikatashi abāyan *Ƙasa,* akwai *Āyōyin Al-Ƙur'āni* dakuma Hadisai masu ɗimbin yawa waɗanda sukayi bayani afili ƙarara dangane da illar *Shirka* dakuma mai aikata ta, domin kuwa ita *Shirka* takan dawwamarda dukkan mai yintane acikin wutar *Jahannama* kamar yadda *Aʟʟαн(ﷻ)* yafaɗa acikin_
*_Sūratun-Nisā'i āya ta-48_*
:
*"إِنَّ اللَّهَ لَا يَغْفِرُ أَن يُشْرَكَ بِهِ وَيَغْفِرُ مَا دُونَ ذَٰلِكَ لِمَن يَشَاءُ……"*
*_MA'ANA_*
*_Lallai Aʟʟαн(ﷻ) bāya gāfartāwā wanda yake Shirka dashi amma yanā iya gāfarta zunubin da baikai girman Shirkā ba ga wanda yaso……_*
:
_Sannan kuma ita *Shirka* tākasune *Kashi-Kashi,* akwai *Shirkar* da za'a iya ganinta azāhiri tāfito fili, kamar irin *Shirkar* masu bautar waɗannan abubuwa kamar haka:_
:
*_1-Aljanu,_*
  *_2-Malā'ku,_*
    *_3-Matattu,_*
      *_4-Gumākā,_*
        *_5-Duwātsū,_*
          *_6-Bishiyōyī,_*
            *_7-Ƙaburbura,_*
              *_8-Annabāwā,_*
:
_Dadai sauransu, Sannan kuma akwai *Shirkar* da bata fito filiba kamar irin waccen tafarko, to amma Saidai itama wannan ɗin *Shirkāce* babba mai iya fidda Mutum daga *Dā'irar-Muslunci,* kuma idan har Mutum yamutu ahaka bai tubaba to zai dawwane acikin wuta bafita,_
:
_Kamar irin *Shirka* ko *Kāfircin Munāfikai* waɗanda sukan boye *Kāfircinsu* azuciya amma azāhiri za'aga suna wani aiki irin na *Muslunci* amma kuma zuciyarsu cike take da *Shirka dakum Kāfirci,* Sannan kuma awani lokacin *Shirka* takan kasancene ta hanyar wata *aƙīda mummūnā* da Mutum ya *ƙudurceta* azuciyarsa, kamar Mutumin dayake *ƙudurta* cewa banda *Aʟʟαн(ﷻ)* akwai wani mai iya kashewa ko rāyawa ko ya azurta wani kokuma ya talauta wani, dadai sauran dukkan wani abu da *Aʟʟαн(ﷻ)* ne kaɗai yakaɗaita da ikon yinsa kamar ruwan sama ko bāda haihuwa, kokuma Mutum ya *ƙudurta* cewa akwai wani bāwa daga cikin bāyin *Aʟʟαн(ﷻ)* wanda za'a iya yiwa cikakkiyar biyayya irin wadda akeyiwa *Aʟʟαн(ﷻ)* shi kaɗai, kokuma Mutum ya *ƙudurta* cewa banda *Aʟʟαн(ﷻ)* akwai wani Mutum wanda yasan dukkan kowanne irin gaibu, ko Mutum ya *ƙudurta* cewa akwai wani wanda ba *Aʟʟαн(ﷻ)* ba kuma yake da ikon yin gāfara ko yayi azāba gawasu,_
:
_Hakanan *Shirka* tana shiga acikin maganganu kamar Mutum yanemi taimakon wani Mutum rayayye ko matacce danufin yakāreshi daga fāɗawā cikin wata Musība kokuma ya yāye masa ita, kokuma yaroƙi wani abu awajen wani Mutum wanda bābu wanda ya isa yayi wannan abin in ba *Aʟʟαн(ﷻ)* ba, Shiyasa acikin_
*_Sūratu-Yūnus āya ta-18_* _*Aʟʟαн(ﷻ)* yake cewa:_
:
*"وَيَعْبُدُونَ مِنْ دُونِ اللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُمْ وَلَا يَنْفَعُهُمْ وَيَقُولُونَ هَٰؤُلَاءِ شُفَعَاؤُنَا عِنْدَ اللَّهِ……َ"*
*_MA'ANA:_*
*_Suna bautawa wanin Aʟʟαн(ﷻ) wanda bazai iya cutar dasuba ko ya amfānar dasu, suna cewa waɗannan sune zāsu cēcēmu awajen Aʟʟαн(ﷻ)……َ_*
:
_Hakanan *Shirka* takan iya kasancewa acikin ayyukan Ibāda, kamar Mutum yayi *Sallah ko Sujjada* ga wani wanda ba *Aʟʟαн(ﷻ)* ba, ko ya yanka dabba agindin wata *Bishiya ko Dutse* ko wani guri na musamman danufin yasamu tabarrukinsu, *Ya Aʟʟαн(ﷻ)* kayi mana tsari da *Shirka* amin,_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)