NAMIJI UBA


NAMIJI UBA

Ka tambayi Babanka 10k sai ya faÉ—a maka cewa zai baka da safe kafin ya fita aiki bayan ya gama maka binciken me ye zaka yi da KuÉ—in.
Cikin daren gaba É—aya, Babanka baiyi bacci ba saboda yana tunanin yaya zai yi ya baka 10k É—in shi da ita kaÉ—ai ta rageshi ma shi.

Da gari ya waye, ya kiraka ɗakin shi ya baka 9k maimakon 10k daka nema. Hakan bai maka daɗi ba, ka murtuƙe fuska, sannan daga bisani kace ka gode bayan ka gama ƙorafi akan Kuɗin bai cika ba.
Mamarka bayan taga hakan bata ce komai ba, sai taje ɗaki ta sameka kai kaɗai ta damƙa maka 2k daga jakarta sai tace da kai:

"Kada kadamu my son, kayi amfani da wannan ka cika kuÉ—in".

Sai kafara murmushi kamar cartoon sai kayi maza ka É—auki waya ka nufi Facebook, WhatsApp, Instagram Ka rubuta: "I have the best Mom in the world, I love my Mom....... ".

Yanzu Babanka ya fita daga shi sai 1k a aljihunshi kuma motar shi ko mai babu, saboda kai ko motarshi bai fita da ita ba dole ya hau taxi zuwa wajen aiki.

A wajen aikin ma, ya kai har dare a office bai dawo ba, bayan ya dawo, duk gidan sai kowa ya fara cewa: "Daddy kam koda yaushe baya zama a gida, Mom ne kawai take tare damu".

Babanka mutumin kirki ba zai taɓa bari kagane yadda yake shan wahala ga iyalanshi ba saboda shi Namiji ne.

Don Allah muna godewa iyayenmu maza domin bamu isa mu faÉ—i irin tashi-faÉ—i da su keyi a kanmu ba. Idan wai baka ganin Babanka Kullum kamar Mamarka bashi ke nuna cewa bai damu da kai ba kamar Mamarka.

Allah Ya jiƙan iyayenmu da suka shuɗe, na raye kuma Ya sauƙaƙe musu rayuwa yasa su cika da imani.
Post a Comment (0)