ABDULKADIR SALADIN 25

25. ABDULKADIR SALADIN
Na Alhaji Nuhu Bamalli
www.bukarmada.wordpress.com
...
Kashegari muka sake haduwa da Bubakar a masallaci. Muka kebe, ya fada mini da rada, ya ce an aiko shi ne don ya taimake ni in kubuta. Ya ce amma in yi hakuri sai watan Yuli, yanzu shi zai koma Berber, ya ci gaba da shiri. Muna cikin Fabrairu ne, sabo da haka na yi ta jira har Yuli ya kama. Wata ya kai kwana goma ban ga Bubakar ba, ya raba, ban ga Bubakar ba, ya kai ashirin, kai har dai ya kare ba Bubakar.
In dai gajerce maka, Bubakar bai komo Ondurman ba, sai watan Yuli na badi, watau cikin 1893. Shekara guda ke nan har da wata guda.
Da Bubakar ya komo, ya ce sai in shirya don ya zo da rakuma biyu da za su dauke mu. Na ce haka ne, amma ko zai fi amfani mu dakata sai watan Disamba, lokacin sanyi ? Tafiya cikin Yuli ba ta yiwuwa, tumbana da ya ke daji za mu yanka. Nan da nan ya yi na’am da wannan shawara, ya koma Masar. Ashe kafin ya koma ya sami labarin Halifa na son ya kama shi. Sabo da haka da ya je can, don kada ya yi hasarar ladansa, sai ya gaya wa manyana, wai ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya tafo da ni, amma ni ne na ki. Ka ji halin ’yan duniya. Amma su manyan nan ba su yarda da jawabinsa ba. Suka sake neman wani falke wai shi Musa Wad Abdurrahman, suka yi tsada da shi, suka ce in ya kubuto ni daga Sudan za su biya shi £1000, watau jaka goma. Musa ya turo kanensa Ahmed ya zo, ya ce in shirya don kwanan nan mutum biyu za su zo su gudu da ni. Ya ce mu hadu kudu da gari.
Ran 1 ga Yuli, Ahmed ya ce shiri ya gamu zan tashi gobe da dare. A ran nan na fada wa barorin gidana, na ce wani abokina ba ya lafiya. Zan tambayi iznin Halifa in je in duba shi cikin dare, kila kuwa zan kai har wayewar gari a can. Yamma ta yi, Halifa ya shiga gida, ni kuma na koma gidana na fara shiri a boye. Muka dauki hanya da ni da Ahmed. Ga mu nan har muka kai makabarta. Muna cikin tafiya sai na ji kafata wowaf, ta fada cikin wani burmammen kabari, kasussan mutumin da ke ciki suka rike mini kafa kam, da kyar na zaro. Na ce da ba’a, “A’aha, ashe ba Halifa kadai ba, kai ma, na kabari ba ka son im bar Sudan ne ?" Muka dai wuce har inda aka ce ja-gabana za su jira mu. Ahmed ya yi dan tari ya nuna musu ga mu mun iso, amma ba mu ji motsin kowa ba. Muka yi ta nema ba mu dai gan su ba, sai muka komo gida. Na iso gida da asalatu, gari ya yi shaa, na hau gado na kifa ciki don bakin ciki. Kila hankalina bai taba tashi kamar ran nan ba sabo da wannan rashin sa’a. Aka sake kwana biyu tsakanin ban ga Ahmed ba. Ran nan sai ga shi. Na tambaye shi dalilin da ja-gaban nan suka ki zuwa wurin da aka yi alkawari da su. Sai ya ce sun sake shawara ne. Wai sun tabbata ko na gudu za a sake kame ni tare da su, za a kuwa yi musu hukunci mai zafi.
Jin haka sai na hakura, na tattara al’amarina na danka ga Ubangiji, na bar masa yi. Bayan kwanaki sai hikima ta zo mini. Na kira wani falke wai shi Abdurrahman Wad Harun, na kulla asiri da shi. Na rubuta takarda zuwa ga Manjo Wingate da kuma wakilin Austria na Alkahira na fada musu halin da na ke ciki. Manyan nan suka kulla alkawari da Abdurrahman, suka ce in ya fito da ni Sudan lafiya, za su biya shi jaka goma. A ciki suka fara ba shi jaka biyu. Har wa yau kuma gudun kada Abdurrahman ya zuke ko ya kasa, sai Manjo Wingate ya sake yin sharadi irin wannan da wani Balarabe wai shi Oshaihu Karrar.
Ran nan sai na ga wani bako ya nufo ni da wata ’yar guntuwar takarda. Na bude sai na ga an ce, “Ga Oshaihu Karrar nan. Zai mika maka allurai uku don ka gane shi. Amintacce ne yardajje. Wingate na gaishe ka." Wanda ya rubuta kuwa mishan din nan ne Ohrwalder da mu ke tsare tare, don shi Allah ya ba shi sa’a ya tsere tuni, yana Masar.
A wani maraice cikin watan Janairu, 1895, sai na ga wani mutum ya goge ni a masallaci, ya mika mini allurai uku. Na ja shi sai bayan gidana na ce ya fada mini irin dabarunsa. Ya ce, “Na zo nan garin don in kubutad da kai ne daga hannun Halifa. An ajiye rakuma a wurare dabam dabam don musaya a ko wane zango. " Ya ce amma sai im ba shi takarda ya koma Masar a ba shi kudi tukun. Ko da ya ke ina son kubuta dag a Sudan, amma na tabbata wannan ba ya iya taimakona. Na rubuta yar takarda, a ciki na ce wannan bai yi mini ba. Muka yi sallama ya tafi, ban sake ganinsa ba.
Zuciyata ta dagula da kashewar al’amari haka. Ko yaushe kofar tsira ta samu sai ka ga ta rufe. Amma ban karai ba, don na tabbata Allah ma ji rokon bawansa ne. Haka kuwa ya yiwu, don ba a dade ba, sai ga wani wai shi Muhammed, danuwan Abdurrahman, wanda suka kulla sharadi da manyana a Masar, ya zo masallaci. Da aka gama salla, ya zo kusa da ni ya rada mini ya ce, “Mun shirya. An kawo rakuma, an sami ja-gaba amintattu. Za ku tashi in wata ya shiga duhu, watau wajen ashirin da shi. Sai ka shirya.” Ya tafi abinsa. A wannan karon fa sai na ji karfi a zuciya. Ran wata Talata, na ga Muhammed yana jirana a kofar masallaci. Ya ce shiri ya gamu za mu tashi gobe.
Daren ran nan ko runtsawa ban yi ba. Ina tunanin ko wannan shirin zai yiwu, ko shi kuma zai watse. Wata zuciya ta ce misali muna cikin gudu a kama mu, a komo da mu gun Halifa, ko wace irin azaba zan sha? Sai Allah ya sani. Wata zuciyar kuwa ta ce ba kome, har mu isa Masar babu mai kama mu. Da haka dai har gari ya waye.
Da na je fada da safe, sai na ce ba ni da lafiya. Ko da Halifa ya dubi idona, sai ya gaskata lalle haka ne, bai san rashin barci ba ne. Aka ce in je in kwanta. Da faduwar rana sai na tara mutanen gidana na fada musu cewa na sami sakon kudi da kaya daga wurin ’yanuwana a Turai. Ina so in je in dauko cikin dare, amma ban da su ba na son kowa ya sani. Na ce su kame bakinsu, zan yi musu babbar kyauta. In kuwa sun fada har labarin ya je kunnen Halifa, sun san za a kwace kudin duk, da ni da su duk mu rasa. Don gudun kada in ta da kura su gane nufina, na ce yarona guda Ahmed ya tarye ni da alfadarina gobe a kofar gari, in hawo in komo gida. Na ce ko an zo nemana daga gidan Halifa, su ce na kwana ina amaimai, sabo da haka da safe na hau na shiga gari wurin neman magani. Amma su ba su san unguwar da mai maganin ya ke ba. Shi kuma Ahmed na fada masa. cewa kada ya ce zai komo gida, kome dadewa ya jira ni, sai na zo. Duk dibarun nan wai ni ina bad da kafa ne. Don kafin Ahmed ya gaji da jira ya komo ya ba da labari, mun yi nisa. Kuma ko ya komo, sauran yaran gida ba za su yi farat su ce ga lokacin da na bar gida ba, don suna kwadayin kyautar da na alkawarta musu.
Karfe goma na dare na yi, sai Halifa ya shiga gida, duk aka rurrufe kofofi. Nan da nan na tashi na dauki farda, watau dardumar salla, da farwa, watau bargon ulu, maganin sanyi, na saba a kafada, na sulale ta masallaci sai kan titi. Na sa fuska arewa, ga ni nan, ga ni nan har bayan gari inda muka shirya da Muhammed. Da zuwa sai na ji dan tari, ohom, ashe shi ne ya gan ni. Na ja na tsaya cif, zatona wani ne. Sai ya kawo mini jaki na hau muka nufi wani kango can a gafen gari. Muna isa sai ga mutum ya jawo rakumi. Muhammad ya ce mini, “Ga ja-gabanka. Sunansa Zeki Belal. Zai kai ka inda rakuman da za su dauke ka su ke a cikin hamada. Hau maza maza. Allah ya fisshe ka lafiya. Sai wata rana.”
Belel ya dora ni kan rakumi, shi kuma ya dare, muka duka. Ga mu nan har sha dayan dare, sa’an nan muka iso inda rakuma su ke. Belal ya hau guda, ni kuma na hau guda. Hamid Ibn Hussein shi kuma ya hau guda. Tafiya ta mika har gari ya waye. Muna tafe muna tadi, Hamid ya ce, “Kana zaton yaushe za su fara nemanka?” Na ce, “Bayan sallar safe.” Ya ce, “Wus, in haka ne kuwa sai mu cira kafa. In dai ba wani abu ya faru ga rakuman nan ba, kafin lokacin ai mun tsere, da ikon Allah!”
Muka ci gaba. Don tsoro, im mun taba ’yar tafiya kadan sai in waiga. Ni har yanzu jikina bai ba ni ba. Muna cikin tafiya bayan wayewar gari sai Belal ya ce, “Ku tsaya, ku tsaya. Kwantad da rakuma, kwantar da sauri!” Muka kwantad da rakuma, na ce masa ko lafiya ? Ya ce, “Na hango rakuma can nesa, da dawaki biyu, na kuwa tabbata sun hango mu.”
Tir, malam, ai ba ka ji zuciyata a lokacin ba! Na ce, “Amma in har sun gam mu, ai gwamma mu yi gaba. Kwantad da rakuma zai sa su zaci wani abu.” Hamid ya ce, “Gaskiyarka.” Na dura harsashi cikin bindigata muka duka. Can sai muka hango daya daga cikinsu ya dare bisa doki, ya nufo mu a sukwane.
...
(c) 2017 Waziri Aku
(c) 2017 Taskar Hikayoyi
http://bukarmada.blogspot.com
http://bukarmada.wordpress.com
bukarmada@yahoo.com
WhatsApp: +2348021218337
Twitter: @bukarmada
Instagram: @bukarmada
Post a Comment (0)