Ramadaniyyat 1442H [21]
Dr. muhd Sani Umar (hafizahullah)
Sahabban Annabi (ﷺ) Kakaf Ba Munafuki:
_______________________________
1. Allah (SWT) ya tabbatar mana cewa cikin sahabbai kakaf babu munafuki, domin su da ma can ba su ma yi imani da Annabi (ﷺ) ba, ballantana har su kasance daga cikin sahabbai.
2. Allah ya tabbatar mana da cewa munafukai ba a lissafa su a cikin sahabban Annabi (ﷺ), inda ya ce: (Shin ba ka ga wadanda suka yi abota da wasu mutane da Allah Ya yi fushi da su ba, su ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba; su kuma rika rantsuwa a kan karya, alhali kuwa su suna sane (da yin ta)? [Mujadila, aya ta 14 ].
3. A wanann ayar Allah (SWT) ya bayyana wani mummunan hali na munafukai wadanda suke abota da Yahudawa wadanda Allah ya yi fushi da su saboda kafircinsu da laifuffukansu, ga shi kuma su ba daga cikin muminai suke ba, domin addini ya raba su, kuma ba daga cikin Yahudawan suke ba, domin su ma addini ya raba tsakaninsu sannan jinsinsu ba daya ne ba, domin su munafukai Larabawa ne mutanen Madina, su kuma Yahudawa Isra’ilawa ne baki a Madina. Kuma duk da wannan zagon kasa da suke yi wa Musulunci, suna yi wa Musulmi rantsuwa da cewa su ma lalle Musulmi ne, wai kuma ba sa kai wa Yahudawa labarin Musulmi, alhalin karya suke yi, kuma su ba muminai ne ba. [Fayyataccen Bayani, juzu'i na 6, shafi na 352].
4. Hakanan yana cewa: (Sukan kuma rantse da Allah cewa lalle suna tare da ku, alhali kuwa ba sa tare da ku, kawai dai su wasu mutane ne matsorata). [At-Tauba, aya ta 56].
5. A nan kuma Allah (SWT)ya ba da labari cewa, munafukai makaryatan gaske ne sannan ga su da tsoro, don haka suke yawan rantse wa muminai cewa suna tare da su, amma alal hakika ba sa cikinsu, sai dai kawai suna jin tsoron muminai ne shi ya sa suke rantsuwar cewa suna cikinsu don su sami aminci da zaman lafiya. [Fayyataccen Bayani, juzu'i na 2, shafi na 537].
6. Allah ya tabbatar da cewa munafukai ba muminai ne ba, kamar inda yake cewa: (Kuma suna cewa: “Mun yi imani da Allah da kuma Manzo kuma mun bi,” sannan wata kungiya daga cikinsu takan ba da baya bayan wancan (imanin). Wadannan kuwa ba muminai ba ne.) [Nur: 47].
7. Da fadinsa: Ma’ana: (A cikin mutane kuma akwai wadanda suke cewa: “Mun yi imani da Allah da kuma ranar lahira,” alhalin su ba muminai ne ba.) [Al-Bakara: aya ta 8]
8. Saboda haka su da ma can ba su yi imani ba, ballanta wadannan abubuwa biyu, watau karanta musu ayoyin Allah da kuma kasancewar Manzo (ﷺ) a cikinsu, wadannan abubuwa biyu ba za su kare su daga barin fadawa kafirci.
9. Sabanin sahabbai da suka yi imani da Annabi (ﷺ) tun daga kan muhajiruna, wadanda suka yi imani da shi tun yana cikin tsaka mai wuya, a lokacin da aka tsangwami duk wani wanda ya yi imani da shi, kuma ba ya tare da kowa sai raunana, kamar su Bilal da Khabbab da Suhaib da Ammar da mahaifinsa Yasir da mahaifiyarsa Sumayya. Suka hakura da danginsu, suka bar gidajensu da duk abin da suka mallaka, suka yi wo hijira tare da shi, wadannan imaninsu na gaskiya ne.
10. Hakanan suma Al’ansar wadanda Allah ya yaba musu cewa, sun yi imani, Sun tanadi wurin da za su ba wa muhajiruna na zama, sun kuma tanadi duk irin kyautatawar da za su yi musu, kamar yadda Allah ya ce: (Da kuma wadanda suka tanadi gida (watau mutanen Madina) suka kuma (karbi) imani gabaninsu (watau masu hijira), suna son wadanda suka yi hijira zuwa gare su, ba sa samun wani kyashi a zukatansu game da abin da aka ba su (masu hijira), suna kuma fifita (masu hijira) a kan kawunansu, ko da kuwa suna da tsananin bukata. Duk kuwa wanda aka kiyaye shi daga son kansa to wadannan su ne masu babban rabo.) [Hashr: 9]
11. To, wadannan sune muminai na gaske, ba zai yi wu ana karanta musu ayoyin Allah ba, kuma ga Manzo a cikinsu a tsakiyarsu, amma su kafirta, wannnan ba za ta taba yiwu wa ba.
12. Allah ya nuna wa sahabbai da duniya cewa, zaman da Annabi (ﷺ) ya yi a cikinsu ba karamin matsayi suka samu ba, kamar yadda yake cewa: (Kuma ku sani cewa Manzon Allah yana cikinku. Da zai biye muku game da al’amura masu yawa, tabbas da kun wahala, sai dai kuma Allah Ya sa muku son imani Ya kuma kawata shi a cik
in zukatanku, Ya kuma sa muku kin kafirci da fasikanci da sabo. Wadannan su ne shiryayyu.) [Hujurat: 7]
13. Saboda haka wannan daraja ta zama da Annabi (ﷺ) da sahabbai suka samu, babu wanda zai iya samunta, komai matsayinsa, haka komai takawarsa, kuma komai zuhudunsa da ibadarsa.
14. Saboda haka wadannan su ne sahabban Annabi (ﷺ), wanda duk yadda mutum ya kai ga ibada da walittaka ba zai iya kamo su a matsayi ba. Shi ya sa Annabi (ﷺ) yake gargadin kada a sake a zage su, inda yake cewa: “Kada ku za gi sahabbaina, da dayanku zai ciyar da kwatankwacin dutsen Uhudu na zinare, to ba zai kama kafar wanda ya ciyar da mudu ko rabin mudu (na hatsi) ba daga cikinsu”. [Bukhari#3673 da Musulunci#2540].
15. Wane ne zai iya mallakar kwatankwacin dutsen Uhud na zinare har ya ciyar da shi, ballantana har ya yi tunanin kamo sahabban Annabi (ﷺ) a matsayi?!
16. Don haka idan dai muna son mu samu albarkar rayuwa, to dole mu kiyaye darajar wannan sahabbai na Annabi (ﷺ).
https://t.me/miftahul_ilmi