IBB BAMU MANTA DA ƁARNAR KA BA

*IBB BAMU MANCE BARNARKA BA, ZAMU TUNAWA JAMA'A KADAN DAGA CIKI:*

*1-* IBB ya shirya zabe lokacin su Shehu Yar'adua bayan komai ya kankama, sai ya soke zaben kuma yace ya hana duk wani fitaccen dan siyasa sake tsayawa takara, ba tare da wata hujja ba face danniya da neman dawwama kan mulki.

*2-* Bayan soke zaben su Yar'adua, IBB ya sake shirya zaben su Abiola da Bashir Tofa, bayan anyi nisa da Kidayar kuri'a, Abiola da Babagana kingibe Musulmi da Musulmi suna gaf da lashe zabe, sai IBB ya sake yin halinsa ya soke zaben, ya hana Musulmi Mulki ya dauko Arne Chief Shonikan ka dora.

*3-* Katafawa sun yiwa Musulmi kisan gilla a Zangon Kataf, aka gabatar da shugabannin da suka shirya kisan gaban Kotu, Alkali Kirista Okadigbo ya duba zaluncin da aka yiwa Musulmi ya wuce misali sai ya yanke *Hukuncin Kisa* ga su Zamani Lokob da Zamani Kaza etc, abin takaici IBB yaki aiwatar da hukuncin, akarshe aka sake su, har yanzu kudancin Kaduna bata zauna lafiya ba.

*4-* *IBB ne kan gaba wajen dora Obasanjo mulki a 1999,* "yan Arewa munga wulakanci lokacin Obasanjo, *Kusan galibin Matsaloli da muke ciki a Arewa sakamako ne na gadar zare da Obasanjo ya kafa mana. !!!*

*5-* Shekaru 6 *"yan Boko Haram na kashe mutanen Arewa da korar su daga Gidajensu, IBB bai taba fitowa yace kada Jonathan ya nemi tazarce ba, sai yanxu da muka fara fitowa daga kangin da suka Jefa mu.*

*Ina IBB* ya shiga lokacin da Boko Haram suka Kame Kananan Hukumomi 20 a cikin Nigeria *?*

*Ina IBB* ya shiga lokacin da Boko Haram suka Kori mutanen Arewa Milyan biyu daga Gidajensu *??*

*Ina IBB* ya shiga lokacin da Makiya Musulunci suka Kashe mutum 500 a Masallacin Jumu'a dake Kano *???*

*Ina IBB* lokacin da "Yan Boko Haram suka yanka yara 50 "yan Makaranta a Buniyadi Yobe State *?*

*Ina IBB* lokacin da "Yan Boko Haram suka farwa Kasuwar Shanu a Potaskum suka Kashe 250 *??*

*Ina IBB* lokacin da Kiristocin Kudancin Kaduna suka Kashe sama da Musulmi 500 a Zankowa *???*

Duk lokacin da akayi wannan barnar kunyi shiru sai yanzu da Makiyinku yake mulki sannan zaku rarraho ku yaudari mutane marasa basira *?*


Post a Comment (0)