*ILLAR ANNAMIMANCI❗*
﷽
_Muna farawa da sunan Allah ﷻ, wanda cikin ikonShi ne na samu gabatar maku da wannan tunatarwar, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta (ﷺ)._
_Tunatarwar mu ta yau in shaa Allah za ta Fadakar ne game da *Annamimanci.* Kamar yadda muka sani, Annamimanci ba bakuwar kalma ko aiki ba ne a wajen mu, abu ne da ya zama ruwan dare a cikin Al'umma. Allah Shi kyauta._
_A taqaice dai annamimanci na nufin haddasa husuma (fada) tsakanin mutane biyu, ko fiye da haka, ko wasu kungiyoyi domin ya haifar da rashin jituwa a tsakaninsu._
_*Annamimi* tamkar munafuki ya ke, a koda yaushe aikin shi yin Ƙazafi, ko daukar firar wani ya kaima wani domin ganin cewa an samu rashin jituwa a tsakani. Subhanallah._
_Hakikanin gaskiya, annamimanci laifi ne da addinin Musulunci ya kyamata kuma ya yi hani a kan shi, kuma a al'ada ma, annamimi ba ya cikin sahun mutanen kirki._
_Annamimanci laifi ne da ya ke iya katange mutum daga samun rahamar Allah a ranar Lahira, domin ya na jawo wa bawa shiga wuta 🔥. Wa iyyadzu billah! Makoma ta yi muni._
_عن حذيفة بن اليمان رضي الله عنه قال: قال رسول الله ﷺ: *«لا يدخل الجنة نمام»* رواه البخاري ومسلم._
_An kar6o daga hudzaifata binil Yamani (r.a) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: *«Mai annamimanci ba zai shiga aljanna ba»*. Bukhary da Muslim._
_'Yan uwa Musulmi! Kun dai ji daga bakin da ba ya karya cewa; Annamimi ba ya shiga aljanna. Don haka mu guji aikata wannan laifi, mu guji yawo da gulma da zantukan wasu domin hada fada ko gãba tsakanin wasu mutane._
👏🏽أللهم إني أسألك الجنة وأعوذ بك من النار🔥
_Allah Ya sa mudace._
Ƙaninku kuma Ɗan uwanku a Musulunci:
_*✍🏿Ayyoub Mouser Giwa.*_
_Daga Zauren:_
_*🕌Islamic Post WhatsApp.*_
_Domin kasancewa tare da mu a group din *Islamic Post WhatsApp* sai a turo da cikakken suna da address zuwa wannan number *08166650256.*_
Wassalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.