*_💄👄How To Makeup👄💄_*
*_Makeup step 1_*
*_Jagira_*
*_Abin buqata_*
1.Gazal
2.Angled brush
3.Spooly brush
4.Concealer
*_Yadda zaki yi_*
Ki gyara girarki ma'ana tayi shape din da akeso yadda zata miki jagira mai kyau sannan ki taje da spooly brush ki kawo gazal ki zana girar ki fara da jan layin qasa sannan kizo na sama shima kija farkon ya danyi fadi qarshen ya danyi siriri saiki cika tsakiyan cikin kenan.
💄👄💄👄💄👄💄👄💄👄
Sannan ki kawo concealer da angled brush kiyi highlighting shima ki fara da qasa sannan kizo sama wato ki qara dai-daita gira yanda zata tafi yadda akeso kuma ta qara yin kyau Sannan kidan gyara gaban girar da angled brush da concealer kadan ki kuma tajeshi sama da spooly brush yadda zaiyi shara shara wato yayi haske ba kamar sauran wurin ba kar gazal ya cika a wurin.
💄👄💄👄💄👄💄👄💄👄
saiki gyara concealer wurin da kikayi highlighting da angled brush wanda kikayi highlighting dashi kenan ma'ana kidan rarrage concealer ki goggoge yanda barai cika sosai a wurin girar ba na sama kidan jajjashi sama shima na qasa kidan jajjashi qasa kinga ya ragu kenan ba ki goge duka ba.