MATA KUYI HANKALI DA MAZAJEN KU

MATA KUYI HANKALI DA MAZAJEN KU.
*********
Wannan Labari na Rubuta Shine, Bisa Ga yardar
Wacce abin ya faru da Ita, tare da Sharadin boye
sunanta da kuma garin da take.
Ita wannan matar ta Gaya min Cewa, Yanzu haka
suna kotu ta kai mijinta da Iyayenta kara, da
farko dai ta dawo gidansu tabukaci iyayenta da
su raba aurenta da mijinta. Saboda zai lalata
mata rayuwa a banza.
Da farko Iyayen Sun tambayeta dalilin da yasa
take son a raba auren amma taki gaya musu,
maimakon ta gaya musu gaskiya sai ta ki gaya
musu gaskiya tace, "Ita dai Allah ne ya cire mata
son shi."
Iyayenta Suka ce, Hoho su bazasu raba auren ba,
Na farko dai Alhajin yana mutun ta su, tare da
biya musu duk wasu bukatu da suke so, to su
taya zasu ce ya sake ta? Suka nuna mata su ba
zasu iya wannan abin kunyar ba.
Lokacin da taga Iyayenta sunki amincewa da
bukatarta sai ta je kotu ta bukaci a raba aurenta
da mijinta. Alkali ya tambaye ta dalili amma sam
taki ta gaya masa dalilin faruwar haka.
Sai ta bukaci koda Hul'I ne ita ta yarda ayi domin
Ita bazata koma gunsa ba, da ta koma gunsa
gwanda ta zama karuwa, haka ta gaya wa Alkali.
Jin wannan furucin na ta Sai Alkali ya nemi Mijin
yayi hakuri ya sallame ta mana Yaje ya auri ya
sake aure.
Amma sam mijin yace Shi ba zai sake ta ba, A
gefen Mahaifiyarta kuma tayi Rantsuwa Cewa,
Muddin wannan matar ta rabu da wannan alhajin
to bata yafe mata ba duniya da lahira.
Mahaifinta ne kawai ke tausaya mata, Shima
kuwa ba sosai ba domin har dukanta yayi a
kwanan baya lokacin da mijin ya zo ta rika
zaginsa tana ci masa mutunci.
Innalillahi Wa Inna Ilaihin Raji'un, lokacin da ta
gaya min abinda ke faruwa sai da hankalina ya
bar jikina domin kuwa na dau ki mintukka ba ce
da ita komai ba sai daga baya.
Shi Wannan mijin nata ya kasance kafin ya sadu
da ita ta gaba sau daya yana saduwa ta baya
(Anal Sex) da ita sau goma (wa'iyazubillahi).
Lokacin da na tambayeta keko me ya kaiki yarda
da shi? Sai tace, Alkawali yayi ba zai mata
Kishiya ba, kuma zai kaita makka sannan zai
bata Kuddi ta rika juyawa." Ta kara da cemin,
Sannan ya gaya mata wannan hanya ita ce ke
kawo masa kuddi muddin ya baryin haka to zai
daina samun kuddi. (Innalillahi KAIDAI KAGA
MUTUM).
Tace Lokacin da aka fara babu wata matsala da
ta fuskanta sai dai daga baya sai ta rika jin tana
wani wari wanda Ita kanta bata san daga Ina
yake fitowa ba, haka Kuma Idan tana jin kashi
idan bata je taji ba yanzu yanzu zai zubo mata,
sannan duk lokacin da ta tashi daga bacci
takanga wasu kananan tsutsotsi a jikin bantan ta
(wa'iyazubillahi). Yanzu abinda ke damunta
Shine:
Mahaifiyarta ta tsine mata akan kada ta kuskura
ta rabu dashi.
Sannan tana gudun kada ta fayyace wannan
mummunan abu da ya faru da ita mutane su guje
ta har daga karshe ta rasa wanda zai aure ta.
Wannan Baiwar Allah tayi Nadamar wannan abu
da ya same ta sannan ta bukaci a taimake ta da
Addu'ar Allah ya yaye mata wannan musiba,
Sannan ta Bukaci da In sanarwa Jama'a
musamman ma mata domin su kula sosai da
Sosai.
Ni kuma Na sanar muku Ina Kyautata Zaton duk
wanda Ya samu wannan Sako to ya turawa 'yan
Uwa Domin Ba'a fara ba ya fi an fara.
.
Post a Comment (0)