ZUMUNCI


, *ZUMUNCI*

Wani halattaccen mu'amala ce daya samo asali tun halittun farko.
Yana da mahimmanci da alkhairi a cikin sa. Saboda mahimmancin sa Allah SWT Yace "Ya yanke Rahamar sa ga duk wanda ya yanke zumunci". 

*SU* *WAYE* *KE* *ZUMUNCI* ?
 Ana zumunci da dan'uwa na jini, da Makwabci, da duk musulmi, kamar fadar Manzo SAW "musulmi dan'uwan musulmi ne". 

Ana hada zumunci a aura tayya da zama na wurin kasuwanci da karatu. Akwai hanyoyi da dama na zamantakewa da ake hada zumunci. 

*YAYA* *AKE* *ZUMUNCI* ? 

Ana yin zumunci domin *ALLAH* *SWT.*
Ana taimakon Juna.
Ana Rufawa Juna asiri.
Ana Tausayawa Juna.
Ana Kyautatawa Juna
Ana Auratayya wa Juna
Ana Ilimantar da Juna.
Ana Ziyartar Juna.
Ana yin Nasiha wa Juna. Al'ummar da tayi Zumunci yadda ya kamata tafi kowacce samun Arziki.

Tsawon Rai, Zaman Lfy da cigaba.

Don haka mu rike *ZUMUNCI* kamar yadda yake!

Ya Allah Ka hada kan mu Ka sada Zumunci a tsakanin mu kuma Ka bamu Ladan Zumunci.🔛✔
Post a Comment (0)