ABIN YANA BANI MAMAKI




*Abin yana ban Mamaki 🤔*

Namiji da mace, dukkaninsu suna buri da fatan samun cikakken jindadi, natsuwa da kwanciyar hankali a lokacin da suka yi aure fiye da kafin auren. 

Wannan shiyasa za ka ga saurayi da budurwa sun dauki lokaci suna soyayya don su samu cikakken fahimtar juna. A kullum soyayya karuwa take a wajensu, za su iya yin duk me yiyuwa don su faranta wa junansu rai. Za ka gan su kamar su cinye kansu saboda Qauna. Wannan fa duk kafin aure kenan, 

Amma da zarar an yi aure, sai ka ga labari ya chanja, babu wata magana mai dadi tsakaninsu ballantana kuma maganar soyayya, daga lokacin ita macen za ta ji ina ma a ce har yanzu a gidan iyayenta take, shi kuma namijin ya yi ta da-na-sanin aurenta da ya yi, sai ku ga an zauna babu wani fahimtar juna, ba jindadi ba walwala, daga karshe ma sai ku ga an rabu. Abin mamaki, ina suka ajiye soyayyar da suka sha kafin aure? 

*'Yan uwa ko kun san dalili?*

Ni dai kam yau na gano dalili.

Da farko yana da kyau mu kalli irin tubalin da suka gina soyayyarsu a kai, dayawa soyayyar yanzu, wallahi ana yinta ne ba don Mahalicci ba, sai don wani kyalkyal banza wanda zai kai gi ga zama bazawara jim kadan bayan daura aure.

Za ka samu 'Yan mata ba su la'akari da zabin da Annabi (ﷺ) ya yi masu na auren mutum wanda aka aminta da addininsa da dabi'unsa, sai son abin duniya ya rufe masu idanu. Burinsu su samu *mai Kudi,* wanda zai iya sponsoring din duk kudirin da suka zo masa da shi, sun mance cewa Allah Shi ke azurta bawa kuma Ya kwace a duk lokacin da ya ga dama. Don haka ne bayan an yi aure sai ku ga yana wulakanta ta kamar dabbar da ya sayo a kasuwa, to dama meye bambanci? Ai dama ya san kudi suka kawo ta, don haka dama Bahaushe ya ce: *In da kwadayi, da wulakanci!* Ko kuma ya kasance Allah Ya jefo masa karayar arziki, to anan fa ido zai raina fata, kwanciyar hankali ya kare, fitinar yau daban ta gobe daban, dama kudi suka kawo yanzu kuma babu, within a few months sai ku ga ta koma amsa sunan *Bazawara,* ma'ana dai zama ya gagara, ya kora ta gidan iyayenta. Qalubale! 

Su kuma mazan sun fi son Kyakkyawa, sai ku ji yana cewa ai shi ya fi son 'Yar fara, slim girl, doguwa mai hanci, ikon Allah, da a ce irin wannan method din mahaifinshi ya bi wajen samun mata da yanzu be zo duniya ba! That's why sai ku ga da an yi aure, da zarar ta yi haihuwa daya zuwa biyu, kyawunta ya dan fara low, sai ya watsar da ita ya fara kallon na waje sababbi, ita kuma ta zama rubbish, ya ci moriyar ganga ya yar da.... Ki yi hankali 'yar uwa! 

Dukkansu dama suna son junansu ne saboda wani abu Temporary, to kun ga kuwa ba yadda za a yi a samu farin ciki permanent a zaman aurensu. 

*To Ina Mafita?!*

Dan uwa!
'Yar uwa! 

Ina ga hakuri kawai za mu yi mu ajiye son zuciya gefe, mu dauki zabin da Rasul (ﷺ) ya bamu na zaben abokin zama saboda addininsa da dabi'unsa. It was tested and trusted. Idan don Allah kika so shi, to hakika za ki iya jure rayuwa da shi a kowane hali, shi ma idan don Allah Ya so ki, to ba zai taba cutar da ke ba. Sai ku ga a kullum kuna ta kara samun zuri'a kuma so da Qauna na Qaruwa, a haka sai dai mutuwa ta raba, sai daya ya ci gaba da yi wa daya addu'a da fatan sake haduwa a matsayin ma'aurata a cikin gidan aljannah! 

Yā Allah Ka tsarkake zukatanmu, kuma Ka bamu abokan zama salihai👏

Allah Ya sa mudace.

 
Daga Qaninku:
*✍🏿Ayyub Musa Giwa.*
*(Abul Husnain).*
Post a Comment (0)