GUDUN TSIRA 3 COMPLETE





GUDUN TSIRA Littafi na Uku Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- SULEIMAN Zidane kd.. 
Whatsapp 09064179602
★GUDUN TSIRA★
 Littafi Na Uku(3)
Part A
★Suleiman zidane kd.

KODA JIN WANNAN BATU NA BOKA hurgas sai Sarki Darwaz ya dubi hurgas cikin matukar mamaki yace,au dama tare da kai zamu tafi neman Siyama da jama'arta?Boka Hurgas yace kwarai kuwa ai na fika tashin hankalin idan har ban tabbatar da mutuwar Siyama ba da jama'arta saboda in dai wannan lokaci yazo to duk wani Boka dayake wannan nahiyar ma sai sun kashe shi sun shafe harkar tsafi gaba daya tamkar ba a taba yinta ba a wannan nahiyar,duk cikin bincikena na ga wannan al'amari.Sa'adda sarki Darwaz yaji wanann batu sai ya gyada kai yace ai kuwa indai muka hada karfi da karfe mu ta kai dole ne muga bayan wadannan makiyan namu.Yanzu zan shiga cikin gida nayi shiri in yaso ka samemu a can kofar fada inda zamuyi zuga mu tafi gaba daya.Lokacin da boka Hurgas yaji wannan batu saiya bushe da dariya sannan yace aini bana bin zugar mutane saidai ku riskeni a can gaba ko hanya ina jiranku.Nine zan zamo mai yi muku jagora har mu riski abokan gaba tunda nine zanfi kowa saurin gano inda abokan gabar suke.Koda gama fadin sai boka Hurgas ya bace bat daga cikin fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Koda ganin hakan sai sarki Darwaz ya ruga izuwa cikin gidan sarautar ya iso cikin ainihin turakarsa ya shiga kimtsa kansa yana sanya kayan yaki.Yana cikin wannan haline matarsa Larisa tare da 'yarsa gimbiya Husaira suka shigo cikin turakar da sauri cikin tsananin tashin hankali.Husaira ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance domin da kadan Siyama zata fita kyau.Ga wanda ma bai iya tantance kyawu ba cewa zaiyi sunyi kunnen doki.Lasira da Husaira suka sha gaban Sarki Darwaz idanunua cike da kwalla suna shirin fashewa da kuka.Kawai sai Lasira ta kama kafadun Darwaz ta rike a lokacin da hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace,haba yakai mijina saboda me zaka bar karagar mulkinka ka tafi farautar kabilar Banu Hanzar alhalin baka da tabbacin ganinsu tunda sunyi hijira sun gudu.Kayi sani cewa zata iya yiyuwar cewa tuni ma sun fice daga cikin nahiyar nan gaba daya.Ka tuna cewa fa kwananka uku kacal akan karagar mulkin nan,Idan har wani tsautsayi ya sameka a cikin wannan tafiya shike nan fa ka rasa karagarka nida 'yarka kuma rayuwarmu ta shiga cikin hadari kenan tunda ka san cewa kana da makiya da yawa a cikin majalisar garin nan da cikin jama'ar gari.Lokacin da Lasira tazo nan a zancenta sai Sarki Darwaz ya bushe da dariya,al'amarin dayai matukar baiwa Larisa mamaki da haushi kenan,ta kura masa idanu,ita kuwa Husaira sai ta sunkui da kanta kas tana zubar da hawaye kawai.Daga can sai Darwaz ya tsuke bakinsa kuma ya hade fuska ya dubi Lasira yace,yake matata yanzu ke ashe har kina tunanin cewa wani abu zai iya taba lafiyata a wannan fita da zanyi?Ashe kin manta da cewa ni mutum ne mai tsananin sa'a da rabo bisa dukkan abinda na sa agabana?A iya saninki dani tun muna matasa wane abune kika taba ganin ya gagareni?Larisa ta girgiza kai tace duk abinda kasa agabanka sai kaga bayansa amma wannan karon naji a jikina cewa lallai zaka riski matsala kasancewar mai Laya ya kiyayi zamani.Darwaz ya gyada kai cikin murmushi yace,ai ko Giwa ta fadi tafi karfin karnuka su dasa mata wawa sai a sannu.Kada ki manta cewar 'yarki Husaira ta gadoni a jarumtaka gani da taurin zuciya,don haka ko babu ni dole ne ayi shakkarki saboda ita kuma itace zata gaji karagata.Ke Husaira mene dalilin da yasa kike zubar da wannan hawaye daga idanunki?Shin kina tsoron kada na fita ne wani tsautsayi ya sameni?Koda jin wannan tambaya sai Husaira ta dago kai ta dubi sarki Darwaz cikin murmushi tana mai share hawayenta tace,ko kadan ni bana tunanin akwai wani mahaluki ko wani tsautsayi da zai sameka.Ina zubar da wannan hawaye ne saboda kawai takaicin kace bazaka tafi tare dani ba.Ka sani cewa a rayuwata ban taba fita yaki ba na daukar rayukan bil'adama da yawa.Wannan ce kadai damar da nake da ita wacce zan gwada tsantsar iyakar jarumtakata kuma a yanzu ne takobina za ta sami damar shan jini mai yawa ta more,amma gashi ka hana.Ina mai rokonka don darajar iyayenka da kakanninka wadanda suka shude kayi mini izini yanzun nan naje na kimtsa cikin gaggawa ayi wannan tafiya dani.Ka tuna cewa ni kaina jarumtakata ta ninka ta marigayi sarki Ruguzan sau uku,bare kai kanka.Ai abin kunya ne ma ace kaine da kanka zaka tari Siyama ka yaketa,ni ya kamata ka barni da ita a matsayina na 'ya mace kamarta nayi mata kisan gilla na ciro kanta nazo maka dashi.Lokacin da Husaira tazo nan a zancenta sai mahaifiyarta ta shara mata mari ta dubeta a fusace tace,yanzu ke dama manufarki kenan,ashe ban sani ba?Wato zuciyarki ta kekashe ta zama irin ta ubanki kin gadoshi da rashin imani da tausayi alhalin kina matsayin 'ya mace wacce nake son tayi aure ta bar mini zuri'ar dazanyi alfahari da ita mai farin jini a cikin al'umma?Koda Larisa tazo nan a zancenta sai Husaira da Sarki Darwaz suka duni junansu suka bushe da dariya.Husaira ta hade rai ta dubi Larisa tace yake ummina ki sani cewa kyan 'da ya gaji ubansa,idan mai mulki yana son ya sami karfi da biyayyar talakawansa dole ne ya kasance mara tausayinsu.Ni SARAUNIYAR GOBE ce wadda take da burin dama yafi na mahaifinta don ni so nake na mallaki duk kasashen dake nahiyar nan gaba daya su zamo a karkashin mulkina.Koda jin wannan batu sai Sarki Darwaz da Larisa suka kurawa Husaira idanun cikin tsananin kaduwa da mamaki,daga can sai Sarki Darwaz ya bushe da dariyar farinciki yace,tabbas yaune na san cewa banyi haihuwar banza ba tabbas na sami irin 'yar dana dade ina mafarkin samu.Koda gama fadin hakan sai Sarki Darwaz ya rungume Husaira cikin murna yana A*H PHYSICIST maicewa,jeki ki shirya yake 'yata lallai tare dake zamu tafu wannan gagarumin yaki.Kafin Sarki Darwaz ya gama rufe bakinsa tuni gimbiya Husaira ta ruga izuwa cikin turarkata.Ita kuwa Larisa saita durkushe a kasa ta fashe da kukan bakinciki.Ko kallonta Sarki Darwaz baiyi ba ya gama shirinsa ya zuba dukkanin makamansa na yaki a jikinsa sannan ya fice daga cikin turakar ya bar Larisa a zaune a kasa dirshen tana rusa kuka.Wannan shine abinda ya faru a cikin birnin Kisra bayan Siyama ta sami nasarar kashe Sarki Ruguzan da kyar da sidin goshi domin ta kawo karshen mulkin zaluncin da yakeyi a nahiyar harma jama'arsu su sami damar gudanar da rayuwarsu a cikin daji a kwanciyar hankali.Abinda bata sani bashine ALLURA TA TONO GARMA,domin babu wani sauki talakawa zasu samu face karin matsawa,talauci da fatara wacce sai sun gwammace mutuwarsu akan rayuwars a doron kasa.Kuma ta tsokano tsuliyar dodon daya shafe shekara da shekaru a kwance yana faman shara barci kuma ta kulla gabar da ba a san ranar karshenta ba. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ AL'AMARIN JARUMA SIYAMA KUWA,lokacin da ta samu ta fice daga cikin gidan sarautar sarki Ruguzan tayi ta gudu a cikin daji har ta isa inda ta bacewa dakarun birnin Kisra,ashe cikin wata korama ta shige tayi nutso izuwa karshenta ashe akwai wata barauniyar hanya a kasan koramar nan wacce ta bulle har izuwa cikin wani kogon dutse wanda yake a cikin wani daji daban dake nesa sosai.Koda tayi doguwar ninkaya a kasan koramar ta tabbatar da cewar ta iso cikin wannan kogo sai ta taso izuwa saman ruwan ta shaki numfashi kuma ta tsaya ta dan huta sannan ta cigaba da tafiya a cikin ruwan har saida ta iso karshen katon kogon dutsen ta cikin wani dan karamin rami wanda mutum bazai taba tsammanin cewar za'a iya ficewa ta cikinsa ba. Tana fita daga cikin kogon ta tsinci kanta a cikin wannan katon daji wanda tace jama'arta su jirata.Nan take ta kama waige waige da kalle kalle cikin tashin hankali tana zargin ko wani abu ya sami jama'arta ne?Nan take tayi wani irin fito na inkiyar da sukeyi a daji a duk sa'adda suka shiga daji farauta a yayin da suka hango dabbar da suke son kamawa.Bisa mamaki sai taji an amsa mata da irin fion nata sai ga wani babban hadimi na mahaifinta ya fito daga cikin wanu surkuki daya buya ya dubeta cikin murna ya yafito ta da hannu.Cikin farin ciki ta ruga izuwa wannan hadimi shima ya juya ya ruga izuwa wani bangare dabam na dajin.Saida sukayi tafiya mai tsawo tana biye dashi taga an shiga wani sakon daban wanda ma bata taba shigarsa ba sai taga dajin ya zamo sabo a wajenta.Kwatsam sai ta an shigo da ita wani sabon tafkeken kogon dutse wanda ya akai girman gari guda wanda bata taba sanin wanzuwarsa ba a cikin dajin.Shidai wannan kogon dutse a karkashin wadansu dogayen bishiyoyi yake masu manya manyan ganyaye wadanda suka lillubeshi babu yadda za ayi mutum yaga wannan kogon dutse face ya ture ganyayyaki da bishiyoyi.Suna shiga cikin kogon sai Siyama tayi arba da gaba dayan mutanen kabilarsu mazansu da matansu,yaransu da manyansu.Shugaba Sharwan ne kadai a tsaye,amma kowa a zaune yake a kas sun jeru sahu sahu kuma duk sunyi shiru tsit tamkar babu mai rai a cikinsu.Koda aka ga shigowar Siyama cikin kogon dutsen sai kowa ya kamu da tsananin farinciki.Nan take Sharwan ya ruga gareta suka rungume juna yana mai cewa ni san cewar sai kin dawo a raye gareni.Jikina ya bani cewar bazaki mutu ba yake 'yata abar alfaharina.Cikin tsananin farin ciki Siyama ta janye jikinta daga cikin na Sharwan ta dubeshi cikin mamaki tace,yakai Abba yaya akayi ka amince da duk abinda na umarceka da ayi a cikin wasikata.Kuma yaya akayi kuka gano wannan boyayyan kogo inda Dakarun Kisra bazasu taba ganowa ba?.Koda jin wadannan tambayoyi sai Shugaba Sharwan ya bushe da dariya sannan yace yake 'yata kiyi sani cewa ba wani abu bane yasa na bi duk umarnin da kika bani ba acikin wasikar taki ba face na yarda da kwakwalwarki gami da tunaninki da hankalinki baki taba shirya wani abu ba wanda aka kasa samun nasara ba.Dalilina na biyu wanda shine ne mafi muhimmanci shine bamu da wani zabi na samu tsira daga sharrin Sarki Ruguzan face mu yanke hukuncin kashe shi kuma muyi hijira ta zuwa wani dan lokaci kafin a sami sauyin Sarki mai adalci...Saidai Kash!Mun saki reshe mun kama ganye domin sarkin daya hau karagar mulkin Birnin Kisra a yanzu masifarsa da bala'insa sun ninka na Sarki Ruguzan sau goma.Samun azzalumin sarki kamarsa a duniya sai an tona.Nidai a sanina Sarki.Darwaz wanda ya kasance yaya ga Sarki Ruguzan ya tafi wata nahiya dabam ya tare a cikin daji yana farauta kuma yace bazai dawo gida ba sai bayan shekara ashirin,ashe ya dawo birnin Kisra babu shiri sakamakon wata rashin lafiya da dan'uwan sa Sarki Ruguzan yayi bara.Ina mai tabbatar miki da cewar a duniya babu abinda Sarki Darwaz yakeso sama da dan'uwansa Sarki Ruguzan don haka duk yadda zai yi yaga ya dauki fansar ran Ruguzan a kanmu sai yayi don haka nasan cewa da kansa zai jagoranci dakaru ya fito farautarmu.Dole ne yanzu muci gaba da tafiya dare da rana babu sassauci,kuma dole ne mu kiyaye shiga cikin biranen kasar nan face mun tura 'yan leken asirinmu sun gano halin da birnin yake ciki ta hanyar batar da kamanninsu izuwa matsayin 'yan gari.Ba zamu taba samun kwanciyar hankali ba face mun ga mun fita daga cikin wannan nahiya gaba daya.Yake 'yata inason ki sani cewar muna cikin tsananin TSAKA MAI WUYA dole ne muyi niyar yaki da dukkanin karfinmu da ranmu kodai mu tsira ko kuma a shafemu daga doron kasa gaba daya.Lokacin da shugaba Sharwan yazo daidai nan a jawabinsa sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun fite da ko yaushe.Nan take idanunta suka ciko da kwalla tace,yakai Abbana ka yafeni kai da dukkan sauran jama'armu hakika na jefamu a cikin masifa.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace yake 'yata kiyi sani cewa baki da wani laifi a wajenmu domin kokin yi abinda kikayi ko bakiyi ba sai mun shiga cikin wannan tashin hankali da masifa tunda tuni Sarki Ruguzan ya jefamu a cikin wannan tafarki.Inason ki kwantar da hankalinki kuma ki tattauna da dukkan dakarunmu domin mu san hanyar da zamubi mu kare kanmu harmu sami nasarar fita daga cikin wannan nahiyar gaba daya.Yanzu ba baku rabin sa'a kacal ku gama dukkanin shirinku domin mu cigaba da tafiya.Koda jin wannan batu sai Siyama ta kirawo gaba dayan dakarun nasu suka taru a gabanta,a sannan ne taga su Muzaru ashe tuni sunzo sun riski su Shugaba Sharwan.Saida Siyama da dukkanin Dakarunta suka shafe rabin sa'a cif sannan suka kammala dukkanin shirye shiryensu,nan take akayi wata dabara aka lullube jikin kowa da koren ganya,hatta dawakai da dabbobi saida aka lullubesu da ganyaye yanda ko kada ba a ganin jikinsu sannan aka fito daga cikin kogon dutsen aka ci gaba da tafiya,mata suka goya yara kanan,su kuma tsofaffi da miskinai matasa suka goyasu a bayansu akayi ta tafiya cikin sauri sauri gudu gudu.A ko yauhse dakarun da suka kware a iya leken asiri suna kan gaba sai sunyi tafiya mai nisa sun tabbatar da cewar babu wani mugun abu a gabansu sannan suke dawowa su bayar da umarnin a cigaba da tafiya.A bayan tawagar kuma a ko yaushe wadansu dakarun leken asiri ne suna bazuwa gaba da yamma,kudu da arewa don tabbatar da cewar ba wanda ya biyo sawunsu.Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba dare ba rana har tsawon kwana uku ba tare da an gamu da wani mugun Abu bà.★GUDÛN TSIRA★ Littafi Na uku (3) Part B ★A-H Physicist★ Ba tare da an gamu da mugun abu ba kuma duk sa'adda aka gaji ko lokacin barci yayi sai a nemi wuri mai huduwar gaske mai hadarin gaske inda baza a taba zaton cewa wani abu mai rai ba zai iya shiga wajen ba,sai a shiga a kwakkwanta.A safiyar kwana na ukun ne suka hangi wani babban Birni wanda ake kira MADINATUL SULTAN a can gaban dajin da suke,tazarar dabata wuce ziri'a dari da sittin ba.Koda hango wannan birni na Madinatul Sultan sai kowa ya cika da farin ciki musamman Shugaba Sharwan.Nan take Sharwan ya dubi Siyama cikin murmushi yace,yake 'yata ki sani cewa mun iso birnin Madinatul Sultan inda zamu iya hutawa har tsawon kwana uku a cikin kwanciyar hankali kuma mu kara hada guzuri mai kyau mu ci gaba da tafiyarmu.Koda jin haka sai Siyama tayi ajiyar zuciya sannan tace,yakai Abbana kayi sani cewa nikam bani da kwanciyar hankali a duk inda zamu shiga,ina mai shawartarmu damu hakura da shiga cikin birnin Madinatul Sultan kawai mu kewaye ta bayan birnin mubi ta cikin daji mu ci gaba da tafiyarmu.Yayin da Sharwan yaji wannan batu sai ya girgiza kai yayi murmushi sannan yace,shin kin manta ne cewar shugaban da yake mulkin birnin madinatul Sultan abokina ne kuma aminina?Tun muna yara kanana muka saba a daji wajen farauta saboda shakuwar da mukayi dashi ne ma na bashi 'yar kabilarmu guda daya ya aura a sirrance ba tare da Sarkin Kisra ya sani ba.Akwai amana da alkawari mai girma a tsakaninmu dashi,ai na tabbatar da cewa baza a hada baki dashi ba a cutar damu ba,kuma ko me ake ciki ma ai yanzu mun baro dakarun kisra a can bayanmu,koda an aiko manzon sai mun rigashi isa birnin Madinatul Sultan bare batun dakaru masu yawa wadanda zasu dana tarkon cutar damu.Siyama ta numfasa tace na yarda da duk abinda ka fada ya Abbana.Bazan hanamu shiga cikin wannan birni ba,amma kafin mu shiga din inason ka fara aikawa da manzo a sirrance yaje ya gana da Sultan ya sanar dashi duk halin da muke ciki,idan har yace mu shigo cikin birnin nasa sai mu shiga tunda dai mun bashi amanar kanmu.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi yace,tabbas nima na gamsu da wannan shawara.Nan take aka tashi wani kwararran dan leken asiri wanda ake kira da Jamar yayi shiga irin ta fataken birnin Kisra aka bashi dukiya da dakaru kimanin mutum arba'in bisa keken doki suka durfafi birnin Madinatul Sultan.Suma dakarun nasa gaba daya shigar irin dakarun Birnin Kisra sukayi.Lokacin dasu Jamar suka iso kofar birnin Madinatul Sultan basu fuskanci matsalar komai ba don ana ganinsu aka bude musu kofa ko cajesu ba ayi ba suka kunna kai cikin birnin,sukayi ta tafiya basu tsaya a ko ina ba har saida suka iso kofar fadar birnin.Suna zuwa aka yi musu iso suka shiga cikin fadar suke zube a gaban Sultan suka kwashi gaisuwa.Sultan ya dubesu cikin alamun mamaki yace yaku wadannan bakin fatake ku gabatar da kanku domin ban sanku ba daga cikin fataken dana saba yin mu'amala dasu ba daga Birnin Kisra ba.Koda jin wannan batu sai Jamar ya zura hannunsa a cikin aljihu ya dauko wata wasika ya bayar a mikawa Sarki Sultan.Koda Sarki Sultan ya warware wasikar ya karantata a gaban fadawansa sai ya kamu da tsananin farinciki ya mike tsaye da sauri ya rungume Jamar yana mai yi musu lale marhaban tamkar yaga 'yan uwansa na jini.Al'amarin daya daurewa 'yan majalisarsa kai kenan.Nan take Sarki Sultan yasa aka kai su Jamar masauki mai kyau aka kawo msu abinci da abin sha mai rai da lafiya.Kafin ma su fara cin abincin sai ga Sarki Sultan da kansa yazo har cikin turakar da suke,dakarunsa na take masa baya.Nan take ya sallami dakarun nasa yace duk su kama gabansu su bashi wuri yana son ya gana da bakinsa.Nan take kuwa dakarun suka fice daga cikin gidan suka barshi tare dasu Jamar.Suna gama fita Sultan yasa aka rufe kofar turakar da tagoginta don kada ma iska ta dauki sautin zancen da zasuyi takai izuwa kunnen dakarun nasa.A sannan ne Sarki Sultan ya dubi Jamar yace,Ya kai wakilin babban aminina,kayi sani cewa lallai rayuwar kabilar Banu Hanzar tana cikin tsananin hadarin gaske domin tuni wani aljani yazo da sako daga sabon sarki na Kisra cewar da zarar kun iso Birnina na sa a kamaku gaba dayanku a tsare a kurkuku har Sarkin yazo ya riskeku.Tuni na karbi wannan sako kuma na tabbatar da cewar zanbi umarni a zahiri,amma a badini nayi watsi da umarnin Sarki Darwaz domin irin amanar dake tsananina da Shugaba Sharwan bazata barni na bari a cutar daku ba.Tuni wannan aljani ya juya da nufin ya koma wajen Sarki Darwaz ya sanar dashi cewa ya isar da sakonsa a gareni,amma sai na tura wani babban hadimina wanda yafi aljanin karfin damtse dana sihiri ya bishi a baya ya tsafanceshi ya kulleshi a cikin wata kwalbar sihiri domin kada ya ganku akan hanya yaje ya tona muku asiri a riskeku a kawar daku.Yanzi ina son ku bari sai dare ya raba sannan kuje ku shigo da mutanenku izuwa cikin garin nan.Hatta masu gadin kofar birnin nan zansa a sauyasu a cikin daren nan na yau na zuba yardaddu a kan aikinsu.Idan ku ka shigo zan rana muku dukkan kayayyakin daya kamata domin ku saje da jama'ata domin ku sami damar tanadar da guzurin da kuke bukata ku kammala dukkan shirinku sannan ki ci gaba da tafiyarku harku cimma burinku na fita daga wannan nahiyar gaba daya. Ina mai tabbatar muku da cewar sai kun bar birnina da kamar kwana bakwai sannan su Sarki Darwaz zasu iso kuma duk irin binciken dasuyi bazasu taba gano cewar na baku mafaka a birnina.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa Sai farinciki ya lullube su Jamar suka zube kasa suna yi masa godiya.Kamar yadda Sarki Sultan ya shirya kuwa haka al'amarin suka kasance wato saida dare ya raba san nan aka sauya nasu gadin birnin na Madinatul Sultan sannan akaje aka shigo da kabilar Banu Hanzar gaba dayansu izuwa cikin birnin a sirrance ba tare da kowa ya sani ba bayan an yi musu shiga irinta mutanen birnin.Siyama da mahaifiyarta da shugaba Sharwan kuwa har cikin ainihin turakar Sultan aka kaisu suna yin arba da juna sai Sultan ya ruga ga Sharwan suka rungume juna suna masu fashewa da kukan farin cikin sake saduwa domin rabonsu da ganin juna a kalla yakai shekara goma sha biyar.Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan a lokacin daya Hango Siyama da mahaifarta ya dubi Siyama cikin tsananin mamaki sannan ya dubi Sharwan yace,yanzu wannan Siyama ce ta girma haka?Sharwan ya gyada kai cikin murmushi yace,kwarai kuwa wanna Siyama ce rabonka da ita tun tana da shekara uku kacal a duniya,wata rana sa'adda ka kawo mana ziyara a lokacin da ka fito farautarka ta karshe harka daura mata wata laya a wuyanta kace mu adanata a jikinta har abada.Yanzu haka layar na jikinta tun wancan lokacin tana bata tsananin kulawa yadda ya kamata.Koda gama fadin hakan sai Sharwan ya taka yaje inda Siyama take ya zura hannunsa cikin wuyan Rigarta ya janyo wata siririyar laya dake zagaye a wuyanta wacce akayita da hakorin zaki guda daya.koda Sultan yayi arba da wannan laya sai ya kamu da tsananin farinciki sannan ya dubi Siyama yace yake 'yata kiyi sani cewa asalin wannan laya ta kakana ce wanda ya haifi ubana nima gadonta nayi kuma ubana ya tabbatar mini da cewar duk wanda ya girma tare da layar a jikinsa babu makiyinsa dazai taba samun nasara akansa.Kuma duk irin tsananin rintsin da mutum zai shiga sai dai kawai yasha wuya.Har yau har gobe ban haihu ba kuma bisa binciken danayi a tsafi da wanda matsafa sukayi mini bazan taba haihuwa ba a takaice dai har na mutu bazan sami magaji ba.Mahaifinki yayimini abinda har na mutu bazan iya saka masa da komai koda kuwa zan bada raina a matsayin fansa ga nasa,bisa wannan dalili ne na sallama wannan laya tawa a gareki tunda kina yarinya karama,tunda shima bashi da wani 'da a duniya saike kadai.Rayuwarki taci gabanki har izuwa lokacin da zaki gajeshi shine kadai babban burinsa a doron kasa.Ina son mahaifinki yaga wannan rana da idanunsa kafin ajali ya riskeshi.Koda Sultan yazo nan a zancensa sai na take Siyama taji ta kamu da tsananin kaunarsa don haka bata san sa'adda ta ruga gareshi ba ta runguemshi tana mai fashewa da kukan farin ciki domin ta tabbatar da cewa basu da wani masoyi a doron kasa wanda yafi Sultan.Bayan hake ne Sultan ya kirawo Matarsa wacce ta kasance 'yar uwar Ilela mahaifiyar Siyama uwa daya uba daya wacce ake kira da suna SHAMIRAT.Koda Shamira ta shiga cikin turakar tayi arba da yar uwarta Ilela sai ta cika da tsananin mamaki gami da farinciki.Lokac i guda suka ruga suka rungume juna suna masu fashewa da kukan murna suna kankame jikinsu tamkar kara aka tsaga,kuma a danginsu su kadai ne suka rage.Bisa dole aure ya rabasu suna kuka kuma tin daga ranar da Sultan ya auri Shamirat ya dawo da ita birnin Madinatul Sultan ita da Ilela basu sake ganin juna ba,kuma basu taba zaton zasu sake saduwa ba,domin a ka'idar dokar Birnin Kisra duk mutumin da aka bashi mukamin shugabanci na wani Birni to shida Iyalansa shiga cikin Birnin Kisra da dukkan dazuzzukan da suke kewayenta sun haramta gareshi.Saida Ilela da Shamirat suka dade a kankame da juna suna kukan murna sannan Shamirat ta farga da Siyama ta hangota a tsaye a can gabansu.Da yake Siyama tana kama da mahaifiyarta,Shamirat na ganinta ta gane cewa 'yar suce,don haka sai ta cire jikinta daga cikin na Ilela ta bude hannayenta a lokacin da hawaye ya zubo mata tana kallon Siyama tace,taho gareni yake 'yata naji dumin jikinki kafin mu sake rabuwar karshe.Nice kadai 'yar iwar mahaifiyarki wacce tayi saura a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Zuciyar Siyama ta karaya,nan take itama idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar da hawaye bata san sa'adda ta ruga izuwa ga Shamirat ba suka rungume juna suka suna kuka.A'amarin daya baiwa su Sharwan matukar tausayi kenan suma suka ci gaba da kukan.Kamar yadda Sultan ya tsara haka duk al'amarin ya kasance wato saida Kabilar su Siyama suka kwana biyu a cikin Birnin Madinatul Sultan ba tare da wani dan garin ya fahimci hakan ba,sannan Sultan yasa aka shirya musu guzuri mai yawan gaske,kuma aka nuna musu hanya mafi sirri wacce zasu fice daga cikin nahiyar gaba daya.Lokacin da Sharwan yazo suyi bankwana da Sarki Sultan sai duk su biyun suka kasa cewa komai suka fashe da kuka suka rungume juna.Tsawon 'yan dakiku suna kankame sannan Sultan ya janye jikinsa daga cikin na Sharwan ya dubeshi a lokacin da hawaye ya zubo masa yace,yakai abokina kayi sani cewa wannan rabuwa da zamuyi yanzu ina ganin cewa itace rabuwarmu ta karshe wadda har abada baza mu sake saduwa ba tunda zaku bar wannan nahiyar tamu ne gaba daya,bansan ranar da zaku sake dawowa ba.Wata kila kafin ku sake dawowa bana raye,wannan hawaye nawa da kaga ya zubo bisa dalili biyu ne.Dalili na farko shine na SO da KAUNAr dake tsakanina dakai.Dalili na biyu kuma hawaye ne na takaici bisa zamu rabu alhalin har yanzu ban sami damar dazan iya saka maka bisa abinda kayi mini a baya ba.Koda Sharwan yaji wannan batu sai nan take shima hawaye ya zubo masa yace,yakai Abokina kayi sani cewa bana fatan naga ranar dazaka saka mini bisa abinda nayi maka a baya.Kuma ko a yanzu ka gama saka mini tunda harka bamu mafaka a cikin birninka a irin wannan lokaci wanda babu wani shugaban birnin dake karkashin masarautar Kisra yayi kundunbalar dakayi domin ka siyar da rayuwarka ne Domin tamu. GÛDÛÑ TSÃŽRA★ Littafi Nà uku ( 3 ) Part C ★A-Haleefah Physicist★ Domin ka siyar rayuwar ka ne domin tamu.Koda jin wannan batu sai Sultan yayi murmushi yace ai taku rayuwar itace mafi amfani akan tawa domin kune kadai zaku iya kawo sauyin rayuwa a wannan Nahiya gaba daya,ku kawar da zalunci ku shimfida adalci.Abokina idan har hakan zata tabbata raina fansa ne akan naku.Inason ka saurara da kyau kaji shawarar dazan baku yanzu wacce idan karkuyi amfani da ita sai mafarkinku ya tabbata gaskiya a wannan Nahiya.Abinda nake nufi shine sai sauyi yazi mana an kawar sa zalunci irin nasu Sarki Darwaz.A duk sa'adda kuka hadu da wadansu mutane wadanda suka zo muku da wani sabon addini to ku yarda dasu kuma ku karbi addinin nasu.Sa'adda Sharwan yaji wannan batu shida Siyama da Ilela sai suka cika da tsananin mamaki.Sharwan ya dubi Sarki Sultan yace,yakai abokina yanzu kana nufin kenan akwai wani addini wanda shine na gaskiya wanda yafi duk Allolin da ake bautawa a wannan Nahiya,kuma yafi tsafi da dukkan Aljanun da akayi imani dasu?Sarki Sultan ya gyada kai yace kwarai kuwa kuma saduwa da ma'abota wannan addini shine burina na karshe.Tuni na dade da samun labarin wannan addini a wajen iyayena kuma suma tun suna yara suka sami labarinsa a wajen nasu iyayen.Da zarar na sadu da wadannan mutane zan ajiye tsafi na rungumesu.Lokacin da Sultan yazo nan a zancensa sai Sharwan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubi Sultan yace,yakai abokina yanzu yaza ayi na shaida wadannan mutane a duk sa'adda na sadu dasu?Sultan yayi gyaran murya sannan yace zaka iya shaida wadanan mutane ta hanyoyi guda biyu,hanya ta farko itace yanayin shigarsu.Ko yaushe zaka gansu a cikin sutura ta kamala mazansu da matansu,basu barin tsiraicinsu ya bayyana ba.Abu na biyu kuma shine sun kasance mutane masu gaskiya,amana gami da rikon alkawari.Basu dauki duniya a bakin komai ba.Babu abinda suke gudu sama da dukiya da mulki.Koda jin wannan batu Sai Sharwan ya girgiza kai yace,ni kuwa zan sa ido sosai duk ranar dana sadu da wadannan mutane zan karbi addininsu hanni bibbiyu domin kana fadin halayensu yanzu naji na kamu da tsananin kaunarsu bisa kyakkyawar mu'amalarsu,wanda duk wani mahaluki daya dauki irinta zai gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali dajin dadi na har abada.Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Sultan ya rungume Sharwan yana mai masa godiya sannan ya sake janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya ce,yakai abokina kayi sani cewa tafiyar dake gabanku da kuma hadarin dake cikinta ba kadan bane domin kafin ku sami damar fita daga cikin Nahiyar nan sai kunyi tafiya ta a kalla wata bakwai da rabi,kuma akwai manyan kasashe guda uku a gabanku.Wannan birni nawa na Madinatul Sultan yayi iyaka da wata babbar lasa da ake kira DARUL HUNAN.Kafin ku isa iyakar sai kunyi tafiya ta kwana arba'in da daya.Indai kuka ketare wannan iyaka lafiya ba tare dasu Sarki Darwaz sun riskeku ba kun tsallake dukkan hadari.Ina ji a jikina cewa abune mayuwaci ku isa har can su Sarki Darwaz basu cimmuku ba domin nasan cewa sai sunyi amfani da kowacce hanya don ganin sun riskeku saboda da zaarar sun iso nan Birnina sunga bakwa nan zasu tabbatar da cewa kun wuce gaba.Tunda bani da tabbacin zan tsira da rayuwata,ina son ku tafi da matata Shamirat tunda kune kadai kuka rage mata a doron Kasa.Idan kuka barta anan tare dani Sarki Darwaz zai iya kashemu tare.Koda jin wannan batu sai Shamirat dasu Ilela suka fashe da kuka,shi kansa Sharwan bai san sa'adda ya kama kukan ba.Sultan ya dubi Siyama yace,yake 'yata kiyi sani cewa sai kin gaji da wannnan GUDUN TSIRA da kukeyi kinji kamar ki tsaya a kasheki ki huta,amma inason ki kasance mai juriya bisa duk irin tsananin da zaki fuskanta,kisa a ranki cewar dukkan tsanani yana tare da sauki.Idan gaba dayan Kabilar Banu Hanzar zasu kare ya zamana cewa ke kadai kada ki sare kuma kada ki cire babban burin dake ranki nason dawowa wanna kasa tamu domin kawar da zalunci.Koda gama fadin hakan sai Sultan yayiwa Sharwan bankwana na karshe inda matarsa Shamirat ta rungumeshi suka fashe da matsanancin kuka na bakin cikin rabuwa.Da kyar yar uwarta Ilela ta janyeta daga cikinsa,ai kuwa sai Sharwan ma ya sake rungumeshi ya fashe da kuka yana mai cewa Abokina bazan yarda na tafi na barka basaidai na zauna azo a kashemu gaba daya tare ko kuma mu tafi tare mu mutu a cikin wannan GUDUN TSIRA da mukeyi.Sa'adda Sultan yaji wannan batu na abokinsa Sharwan sai yakamu da tsananin tausayinsa ya dubeshi yace,na sani cewa babu ranar bakin ciki sama da ranar rabuwa da masoyi,to amma babu yadda zamuyi da kaddara,haka tamu kaddarar tazo,babu abinda zamuyi face mu kasance masu tunawa da junanmu tare da yiwa junanmu fatan alkhairi har sa'adda mutuwarmu zata riske mu,zanji dadi mutukar ka rike wannan a ranka.Haka dai Su Sharwan suka yiwa Sultan Sallama suka tafi matarsa Shamirat tana waigensa tana faman rusa kuma ana janye da ita.A lokacin Sharwan da Siyama ma suka yi ta waigen Sultan Suna zubar da hawaye zuciyarsu na kuna kamar zasu fasa yin tafiyar.A cikin daren ne su Sharwan suka sake sulalewa daga cikin Birnin Madinatul Sultan suka fice suka sake nausa cikin daji suna tafiya cikin sauri sauri gudu gudu kamar yadda suka saba ba dare ba rana har tsawon kwana bakwai.Duk sa'adda suka hadu da gungun yanfashi ko wadansu mugayen dabbobin daji sai kaga sun tarwatsasu farat daya sunci gaba da tafiyarsu. ¤¤¤¤¤¤¤¤¤ A DAREN KWANA NA BAKWANI NE DA tafiyarsu Sharwan,Sarki Darwaz ya iso cikin Birnin Madinatul Sultan tare da rundunarsa ta yaki,'yarsa Husaira na daf dashi bisa kan doki sun jera.Suna isowa kofar Birnin saiga Boka Hurgas ya baiyana tsulum a gaban Sarki Darwaz yana mai kyakyacewa da dariya.Cikin fishi Sarki Darwaz ya dubeshi yace da kana ina muka shafe wannan doguwar tafiyar baka bayyana ba sai yanzu alhalin kace kaine zaka yi mana jagora a cikin tafiyar?Yayin da Boka Hurgas yaji wannan tambaya sai yayi murmushi yace ya shugabana ai tunda aka fara wannan tafiya ina biye daku kuma ina muku jagora saidai na baku tazara mai yawa,domin na iso nan Birnin tun a kwanaki shida da suka wuce.Tabbas zuwana da wuri yayi amfani domin na samo mana wani labari mai muhimmanci dangane da abinda muke zargi.Ko shakka babu shugaba Sultan yayi wadansu baki daga birnin Kisra a matsayin yan kasuwa,wato fatake,amma a cikin kwanaki biyu aka nemesu aka rasa acikin birnin nan.Bisa bincikena danayi na tura wadansu zakwakuran hadimaina na aljanu sun bi bayan wadannan fatake basu gansu ba kuma basu ji duriyarsu ba.Ya shugaba kasani cewa Sultan gawurtaccen matsafi ne don sihirin tsafinsa yafi nawa karfi,Ni abinda nake zargi shine wadannan fatake da akace sunzo fatauci kabilar banu Hanzar ne,kuma Sultan ne ya basu mafaka suka sauka har tsawon kwana biyu sannna suka sulale suka bar birnin nasa.Idan har Sultan yana son ya kubuta daga wannan laifi toya gaggauta fada mana inda wadannan fatake suke ko kuma ya gaya mana garin da suka nufa tafi muje mu gansu da idanunmu.Abu na biyu shine a bisa binciken danayi kafin mu baro Birnin Kisra na gano cewa akwai wata tsohuwar alaka ta zumunci mai karfi tsakanin Sultan da shugaban Kabilar banu Hanzar tun suna yara kanana,sa'adda suke haduwa a daji wajen farauta Kaga kenan akwai yiyuwar shugaba Sultan zai iya taimakon Kabilar Banu Hanzar ta kowacce Siga.Koda Boka Hurgas yazo nan a zancensa Sai Sarki Darwaz ya fusata ainun har jikinsa ya kama tsuma,zuciyarsa kuma ta kama tafarfasa,kawai sai ya yunkura zai sakarwa dokinsa limzani ya zabureshi da gudu izuwa Birnin Madinatul Sultan,amma sai Boka Hurgas ya daga masa hannu yana mai tsayar dashi.Kawai sai Boka Hurgas ya tsugunna ya debo kasar kofar Birnin ya shinshinata kawai yayi murmushi ya dubi Sarki Darwaz yace,ba shakka babu mutanen kabilar Banu Hanzar sun shiga cikin wannan birnin gaba dayansu don haka duk inda ma suke shugaba Sultan ya sani domin naji kamshin sawayensu a kan wannan kasa.Kafin Hurgas ya gama rufe bakinsa tuni Husaira ta zare takobinta ta sakarwa dokinta limzami ta banke masu gadin kofar birnin da karfin tsiya ta kunna kao cikin birnin a fusace.Ai kuwa sai Sarki Darwaz da sauran Dakaru suka rufa mata baya suka bar Boka Hurgas a tsaye anan yana ta kyalkyala dariyar mugunta da farinciki.Kai tsaye Gimbiya Husaira suka durfafi gidan sarautar Sarki Sultan.Bisa mamaki suna isa gidan sarautar sai suka iskeshi a bude wanwar ko masu gadi babu.A cikin gidan sarautar kuwa gaba dayan dakarun suna zazzaune sun ajiye makamansu a kas,kuma basa shirin tararsu.Koda suka iso tsakiyar gidan sarautar inda wani badakare yake sai suka iske wani mutum guda daya jal a cikin gagarumar shigar yaki.Koda suka matso daf dashi sai sukaga ashe ba wani bane face Shugaba SultanKoda suka zo dab dashi sai suka ja Linzamin dawakansu suka yi tirjiya kuma suka yi masa KAWANYA.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz ya dakawa Sultan tsawa yace,yakai Sultan kayi sani cewa kaci amanarmu ka hada kai da makiyanmu da basu mafaka,idan kana son ka tsira da rayuwarka data iyalanka to ka hanzarta sanar damu inda kabilar Banu Hanzar Suke.Koda jin wannan tambaya sai Sultan ya bushe da dariya,Al'amarin dayayi mutukar baiwa su Sarki Darwaz mamaki kenan.Daga can sai Sultan yayi shiru ga barin dariyar ya murtuke fuskarsa ya dubi Sarki Darwaz yace,ko me zai faru bazan sanar daku inda Kabilar Banu Hanzar suke ba kuma matata tana tare dasu.Yakai wannan azzalumin shugaba nawa kayi sani cewa ni bani da sauran buri a rayuwata face guda daya jal,wanda ko ban cika shi ba wadda ta kashe Dan'uwanka Sarki Ruguzan sai ta cika mini shi,wato Siyama 'yar aminina shugaba Sharwan.Na sani cewa zan mutu a hannunku amma ku sani kafin a kashe Gwaggon Biri sai yayi muguwar barna.Sultan na gama fadin hakan sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama kamar tsuntsu ya hau dakarun Birnin Kisra da SARA DA SUKA a saman yana fille musu kawuna tamkar ya kasance mai fuka fukai,yana shawagi a kansu saboda karfin sihirinsa.Koda Sarki Darwaz da Husaira suka ga irin mummunar barnar da Sultan yake yi musu sai suma suka zare takubbansu suka daka tsalle sama suka tare shi aka ruguntsume da sabon azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban al'ajabi. WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNNAN GAGARUMIN GUMURZU TSAKANIN SU SARKI DARWAZ DA SARKI SULTAN? SHIN SARKI SULTAN YANA FADUWA KASA KUWA? A WANE HALI KABILAR BANU HANZAR SUKE CIKI? SHIN ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA NAHIYAR NAN HAR SU HADU DA MA'ABOTA ADDININ MUSULUNCI SU MUSULUNTA? SIYAMA NA CIKA BURINTA NA DAWOWA NAHIYAR TA KAWAR DA MULKIN ZALUNCI? YAUSHE ZA'A YI GABA DA GABA TSAKANIN SIYAMA DA GIMBIYA HUSAIRA 'YAR SARKI DARWAZ,INDAN SUN HADU ME ZAI AFKU A HADUWAR TASU? WANE IRIN BURI BOKA HUGAS YAKE DASHI A RAYUWARSA? Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na hudu don jin ci gaban wannan kasaitaccen labari Amsa: Su Sarki Darwaz ne suke samun Nasara. Eh Sarki Sultan yana faduwa kasa. kwarai kuwa suna samun damar fita bayan sun sha wahala har su hadu da ma'abota addinin musulunci. Eh Siyama tana cika burinta,amma ba'azo gunba. Idan Siyama da Husaira sun hadu ana tafka azababben yaki mai tsoratarwa. Burin Boka Hurgas ya mallaki Birnin Kisra da Nahiyar tasu.
GUDUN TSIRA Littafi na Uku Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creator:- Suleiman Zidanekd whatsapp 09064179602

Post a Comment (0)