SHARHIN FIM ƊIN IRON MAN 3
Iron Man 3 fim ɗin jarumta ne da aka fitar da shi a cikin shekara ta 2013 a Ƙasar Amurka. Labarin fim ɗin ya samo asali ne daga littattafan almara mai suna Iron Man wanda Stan Lee, Larry Leiber, Don Heck da Jack Kirby suka Wallafa a ƙarƙashin kamfanin Marvel Comics. Kamfanin Marvel Studios ne ya ɗauki nauyin shirya shi, yayin da Kamfanin Walt Disney Studios Motion Pictures shi kuma ya rarrabashi. Fim ɗin shi ne na ukun Iron Man (2008) da Iron Man 2 (2010), sannan Fim ɗin shi ne Fim na bakwai daga cikin Fina-Finan duniyar Marvel mai suna Marvel Cinematic Universe (MCU).
Shane Black ne ya bada umurnin Fim ɗin Yayinda suka rubuta labarin fim ɗin tare da Drew Pearce. An fara ɗaukar fim ɗin ne a ranar 23 ga watan Mayu 2012 har zuwa 17 Disamba 2012, an ɗauki wannan fim ne a wurare da dama da suka haɗa da EUE/Screen Gems Studios da ke Wilmington, North Carolina, Florida, China da Kuma Los Angeles.
An fara haska Iron Man 3 ne a Grand Rex da ke Paris a ranar 14 ga watan Afrilu 2013, sannan aka sake shi a Ƙasar Amurka ranar 3 ga watan Mayu 2013. Fim ɗin ya samu gagarumar nasara sosai ta kowanne fanni inda masana suka yabawa faɗan Fim ɗin, Sautin sa, barkwanci, labari, kayan aiki da kuma kafcen cikin sa. Bugu da ƙari, fim ɗin ya kawo maƙudan kuɗaɗe kimanin Dala Biliyan $1.2 a harkar kasuwancin Fina-Finan duniya baki ɗaya, hakan tasa ya zama Fim na biyu da yafi kowanne kawo kuɗi a wannan shekarar, sannan kuma ya zamo Fim na biyu da yafi kowanne Fim da aka fitar a Amurka da Canada kawo kuɗi a shekarar.
Fim ɗin ya zamo Fim na shida da yafi kowanne kawo kuɗi a Tarihin Fina Finan duniya baki ɗaya, kuma shi ne Fim na goma sha shida daga cikin Fina-Finan da suka fara kaiwa matakin Dala Biliyan ɗaya a harkar kasuwancin Fina Finan duniya.
LABARIN FIM ƊIN
Fim ɗin ya fara ne da nuna mana Tony Stark a wajen bikin murnar sabuwar shekara na 1999, inda Tony Stark ya haɗu da Masanin Kimiyya Maya Hansen wacece ta ƙirƙiro hanyar yiwa Sinadaran Extremis Garambawul domin warkar da waɗanda suka gurgunce. Wani gurgun Masanin Kimiyya mai suna Aldrich Killian Sai ya basu damar zuwa Kamfanin sa mai suna Advanced Idea Mechanics domin su tattauna akan batun wannan sinadari, amma Tony sai yayi watsi da shi.
A 2013, Stark yana cikin Muguwar damuwa sakamakon shigowar baƙin haure daular mutane wanda hakan ne ya jawo rikicin Birnin New York. Wannan dalili ne yasa ya ƙera wasu sabbin rigunan ƙarfe domin Taran abinda ka iya zuwa, hakan ya fara jawo masa matsala a tsakanin sa da budurwarsa Pepper Potts .
Wasu tashe-tashen bama-bamai da wani ɗan Ta'adda mai suna Mandarin yake yi ya tayar da hankalin cibiyar binciken fasaha saboda sun kasa gano tushen al'amarin balle makama. A yayin irin wannan harin ne mai kula da Tony na musamman wato Happy Hogan, ya samu mummunan rauni,hakan yasa Tony ya sanarwa da ƴan jarida cewa baya tsoron sa kuma shi zai yi maganin sa. Domin ya bashi amsa, sai Mandarin ya aika jirage masu saukar Angulu izuwa gidan Tony inda suka ruguza gidan baki ɗaya. Hansen, wacce tazo domin ta gargaɗi Stark itama harin ya rutsa da ita, sai dai ita da Potts sun sha da ƙyar.
Stark ya samu guduwa a cikin rigar sa ta Iron Man wacce J.A.R.V.I.S. Ya tuƙa ta zuwa ƙauyen Tennessee, inda ya shirya yin cikakken bincike akan wannan ɗan ta'adda wato Mandarin. Kasancewa rigar Stark bata da isashen wutar da zata kai shi California, sai kowa yayi tunanin ya mutu.
Daga nan sai Tony ya haɗa kai da wani Fasihin yaro ɗan kimanin shekaru goma mai suna Harley, iya duk binciken da Stark zai yi yayi a wani wuri da bam ɗin Mandarin ya tashi amma babu alama. Daga baya sai ya gano cewa, waɗannan Bama-bamai da suke tashi ba bam ne na kunnawa ba, sojoji ne da aka yiwa aiki da sinadarin Extremis, idan sinadarin ya ƙi zama a cikin jikin nasu, shi ne yake fashewa tare da sojojin kamar bam, shi ne ake cewa bam ne daga ƴan ta'adda domin a kare rashin inganci aiki da sinadarin Extremis.
Stark shaida ne dangane da sinadarin Extremis domin sunyi karo da wani jami'an Mandarin masu suna Brandt da
Savin inda Yayinda suka kawo masa hari. A can gefe kuma, Killian sai ya bayyana, sannan ya sace Potts da Hansen. Yayinda su kuma cibiyar binciken fasaha suke ci gaba da ƙoƙarin ganin sun gano inda mandarin yake, tare da James Rhodes War machine Kenan a da, yanzu kuma Iron Patriot, wanda aka jawo shi zuwa ga tarko domin a ƙwace rigar sa.
Da taimakon wannan yaro dai Harley, Stark ya ci gaba da bibiyar Mandarin har ya gano shi a Miami, bayan ya kutsa cikin Sansanin sa, sai ya gano cewa Mandarin ba kowa bane face wani Shahararren ɗan Kafce mai suna Trevor Slattery , kuma Sam shi bai ma san wane irin aiki ake yi da sunan shi ba. Ashe shi kuma Killian, bayan ya yi amfani da binciken Hansen akan sinadarin Extremis wajen warkar da kansa, sai kuma ya faɗaɗa shirin ta hanyar yiwa sojojin da suka samu rauni a filin daga amfani da sinadarin domin warkar da su.
Bayan ya kama Stark, Killian sai ya bayyana masa cewa shi ne mandarin na gaskiya, kuma ya sanyawa Potts sinadarin Extremis a jikinta tare da fatar Stark zai bada tasa gudunmuwar wajen gyara ingancin sinadarin domin ya cece ta. Killian sai ya kashe Hansen yayin da tayi yunƙurin dakatar da shi.
Stark dai ya samu ya gudu inda suka haɗu da abokinsa Rhodes, a nan ne kuma ya gano cewa Killian yana shirin kaiwa shugaba Ellis hari ta hanyar amfani da rigar ƙarfen Rhodes. Stark ya samu damar ceto wasu Fasinjoji amma bai samu damar hana Killian sace Shugaba Ellis ba.
Daga nan sai suka bibiyi Killian izuwa ga wani keɓaɓɓen waje inda aka ajiye wata tankar mai wacce ta lalace. Shi Killian dama yayi nufin kashe shugaba Ellis a wajen ne a gidan talbijin inda kowa zai gani, hakan zai sa Shugaban Ƙasar Amurka ya koma yaron Killian, kuma abinda ya faɗa shi za'a yi tunda shima zai buƙaci magani wa ƴar sa wacce bata da lafiya.
Yayinda suka isa wajen, sai Stark sai ya tafi zuwa wajen Potts domin ya cece ta, shi kuma Rhodes ya ceci shugaban. Daga nan sai Stark ya Kirawo rigunan sa na Iron Man waɗanda J.A.R.V.I.S. Ke lura dasu domin su taimaka. Rhodes ya samu damar ceto shugaban Yayinda shima Stark ya samu damar ceto Potts, sai dai tuni wannan sinadari na Extremis ya zauna a jikin ta, kwatsam sai gini ya rikito musu inda ta faɗa wani rami inda kowa yayi tunanin ta mutu. Daga nan sai Stark ya tunkari Killian inda ya saka shi a cikin wata rigar Iron Man wacce take lalata kanta domin ya kashe shi, amma hakan bai yiwu ba. Potts wacce wannan Sinadari ya samarwa da ƙarfi sosai ashe bata mutu ba, a nan dai ta kashe Killian.
Daga nan sai Stark baiwa J.A.R.V.I.S. Umarnin ya lalata duk rigunan Iron Man ɗin da ya ƙera domin nuna kulawar sa ga Potts, yayin da aka kama mataimakin shugaba da kuma Slatter.
Da taimakon Stark, an samu dai an warkar da Potts daga cutarwar wannan sinadari na, inda Stark yayi mata alƙawarin cewa zai bar rayuwar sa ta Iron man, sannan akai masa tiyata aka cire wannan ɗan ƙaramin Janareta wanda ke taimakawa wajen kare shi daga mutuwa inda ya jefa shi teku. Inda ya ce ko ba rigar zai ci gaba da kasancewa a matsayin Iron man.
JARUMAN FIM ƊIN DA MATSAYIN DA SUKA FITO A CIKIN SA
* Robert Downey Jr. - Tony Stark / Iron Man
* Gwyneth Paltrow - Virginia "Pepper" Potts
* Don Cheadle - James "Rhodey" Rhodes / Iron Patriot
* Guy Pearce - Aldrich Killian
* Rebecca Hall - Maya Hansen
* Stéphanie Szostak - Brandt
* James Badge Dale - Savin
* Jon Favreau - Happy Hogan
* Ben Kingsley - Trevor Slattery
* Paul Bettany - J.A.R.V.I.S.
* Ty Simpkins - Harley Keener
* Ashley Hamilton - Taggart,
* William Sadler - President Ellis
* Miguel Ferrer - Vice President Rodriguez
* Adam Pally - Gary
* Shaun Toub - Yinsen
<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________
●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●
<••••••••••••••••••••••••••••>
👳🏻♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>
*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng
*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees
*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees
*_"""""""""""""""""""""""_*
🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees
*_"""""""""""""""""""""""_*
📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...