BALA'I BAYA ƘETARE SADAƘA



🌼 *Bala'i* baya ƙetare *sadaƙa* ballantana ya auka ma ɗan Adam. Domin halayen kirki suna tsare mutum daga aukama musiba.

🌼 Mutumin da yake bada sadaƙa yake da halaye na kirki, to baya faɗuwa a rayuwarsa. Duk wanda ya ce maka sai ya ga bayan mutumin kirki to yayi ƙarya. Domin mutumin kirki baya faɗuwa sai in Allah Ya so, duk lokacin da ya tasanma faɗi to zai sami majinginin da zai jingina da shi. 

🌼 Shi yasa sai ka ga ana ta ƙullawa mutumin kirki abu amma suna warwarewa basa kama shi. Saboda in har musulmi yana bada sadaƙa to bala'I bai ƙetarawa ballantana ya afkoma rayuwarsa. Ko annoba aka samu to in mutum na bada sadaƙa zata tsallake gonarsa/wurin sana'arsa ko gidansa. Kamar yanda ya zo a tarihi da dama. 

🌼 Bada sadaƙa tana warkar da cuta, in mutum yayi ta jinya bai warke ba to yayi ta yin sadaka. Tana sauƙaƙa azabar kabari. Tana kariya daga talauci da musiba domin mai badawa baya rasawa. Tana bawa mutum inuwa ranar alƙiyama. Tana disashe fushin Allah. Tana kankare zunubai. Gasu nan dai da yawa.

🌼 *Ƴan'uwa mu bada Sadaƙa, mu yi ma kanmu babban tanadi ta hanyar nauyaya sikelin mu da sadaƙa da kyawawan dabi'u. Hannun da ke bayarwa dai ya fi wanda yake amsa.*

Rubutawa:- Sadiya Lawal Abubakar
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________

» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).

 ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)