🌻Zunubi ciwo ne mai shiga lungu da saƙon jikin ďan adam, tamkar yanda jini yake kai komo. Kuma yana ragargazan ga'b'bai ta hanyar ratsa jini da jijiyoyi, qashi da 'bargo ya duhunta su. Tare da kangarar da zuciya, da tsufar da imani. Ya sanya taurin sa'bo, da kangarewar ruhi. Tun kana jin ciwon zunubi a zuciya da ga'b'bai, har raďaďin ya koma magani gare ka.
🌻Haka nan duk randa imanin ka ya samu sabon rini. Kukan nadama ya fallatsa ma zuciya. Sosan gafara ya fara wanke nacaccen sa'bo. Harshe ya ji ďanďanon ambaton Allah, ga'b'bai suka samu qarfin bauta, tsoron Allah ya dawo da kai hanyar gaskiya, sai dukkanin ga'bo'bin ka su fara ciwo. Ciwon keta duhu da dawowa cikin haske, ciwon wankewar da gafara take ma zuciya. Ciwon fitan guban haram a jiki, ciwon yaqi da shaiɗan, ciwon jure amsa kiran dai-dai, ciwon haquri da jarabawan tuba.
🌻Wahalar wa ne da shi, kuma ba ciwon da ake warkewa lokaci guda bane. Mafiya yawan masu son tuba, a nan ne suke cogewa. Wasu su cije su shallake, wasu kuma su kasa, su koma ga ayyukan su. Domin zaka jarabtu da sa'bon ka fiye da lokacin da kake aikata shi. Domin shaiďan baya son ya goge ka a cikin littafin sa. Ashe kenan lokaci ne mai mutuqar wuya.
🌻Kada mu yi saken barin sa'bo ya huda zukatan mu har yayi tsatsa. Kada mu bari zunubi ya baqanta fitilun cikin zukatan mu. Kofar tuba a buďe take, kuma Allah ba Ya gajiya da yin gafara ga bayin Sa. In ka yi zunubi yanzu, ďaga hannu ka nemi gafarar Sa. Yi nadamar sa'bon ka, yi ďamarar gyarawa da canzawa.
🌻Ka da ka ce sai gobe, shin kai ne da goben a hannun ka? Kada ka yi jinkiri, domin shi jinkiri yana iya jinkirar da zuciyar wanda yayi jinkirin baki ďaya.
🤲🏼Yaa Mai Yalwan gafara, Mara gajiya da amsan tuba. Ka yi gafara ga bayin Ka, kuma Ka amshi tuban mu.
🖎 *Sadeeya Lawal Abubakar.*
*MARKAZUS SUNNAH.*