ƘUR'ANI



🍁🍁Qur'ani cike yake da maganganun da suka isa wa'azi ga ko wane mai saɓo. Ɗauke yake da maganganun hikima da basira masu tausasa zuciya mai ƙunci. Kuma mai warware ma bawa ko wane irin matsala da zuciyarsa take ciki. Ga shi da labarai da busharori masu sanya farin ciki da nutsuwa a zuciyar da take cikin damuwa ko tsoro. Haske ne shi mai ɓullawa cikin ko wane lungu da saƙon zuciya ya haskaka ta. 

🍁🍁Tamkar ruwan sama ne shi mai sauka ya sanyaya zazzafan zuciya, har ya kai ta ga zubda hawayen tuna Mahaliccinta da kwaɗayin rahamarSa. Shi ne alƙiblar ko wane mai karanta shi, duk yanda ka kauce sai ya juyo da kai dai-dai. Kariya ne shi daga dukkanin sharrin mutum ko Aljan. Qur'ani yana ƙara tsoron Allah ya sabunta Imanin bawa. Kuma yana sanya tawakkali da mayar da dukkan al'amura ga Allah. Yana raunana tunanin saɓo ya goge shi. A dunƙule dai, shi waraka ne kuma Rahama ga mutane.

🍁🍁Kaico! Ga mutumin da ya bama Qur'anin sa hutu tun da ramadana ya wuce. Ka iya karanta dubannin kalmomin iska, wanda ba lada kuma ba zasu amfaneka a duniya da lahira ba. Amma karanta aya goma na Qur'ani ya zame maka aiki. Ka jure ka koyi karanta shi ko da aya biyar ne kullum. Ka ga irin canjin da zaka samu a rayuwarka. Sai ka zama kainuwa dashen Allah wurin maƙiyanka (mutum ko aljan).

🍁🍁Allah Ka Ƙarfafa mana Imanin mu, Ka bamu ikon karanta littafinKa. Ka kuma bamu kariya da kariyarKa.

🖎 *Sadeeya Lawal Abubakar.*

📚 *MARKAZUS SUNNAH*
Post a Comment (0)