KUNUN TSAMIYA

💕KUNUN TSAMIYA 💕
Ingredients
Tsamiya
Sugar
Gero
Citta
Kananfari
   Method
Shima kamar yadda ake kunun kanwa akeyinshi saidai shi kafin akai nika xaki dibi gero kadan idan xakiyi kirbi sai ki farfasashi kixuba ki hada ki kirba sannan kuma xakiyi amfani da stamiya a maimakon kanwa kuma shima xaki iya kai markade
🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸
💕KUNUN MDARA 💕
Ingredients
Madara
Flour
Flavour
Sugar
   Method
Ki dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai ki dama flour a kwano daban sai ki xuba acikin ruwan da yake tafasa kita juyawa har yy kauri sai ki sauke ki sa madara amma dayawa akeso kisa sugar nd flavour sai a sha
🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷
💕KUNUN KWAKWA 💕
Ingredients
Kwakwa
Madara
Flavour
Sugar
Farar shinkafa
Method
Ki wanke shinkafa fara ta tuwo ki shanya ta bushe ayi grinding dinta sai ayi sieving
Sai ki ajiye aside ki gurxa kwakwa ki tace ruwan ki dora a wuta idan ya tafasa sai ki dama garin shinkafar kixuba ki ta juyawa har tayi kauri sai ki sauke kisa kwakwar ki gauraya kixuba sugar madara nd flavour then serve nd drink
🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺🍺
💕KUNUN GYADA💕
Ingredients
Farar shinkafa
Gyada
Madara
Sugar
Method
Kijika shinkafa ta wuni ko ta kwana gyada ma haka amma daban daban sai ki ciremata jan bayanta ki wanke ki hadesu guri guda ki sa citta kadan ki yi blending dinsu then sieve nd keep aside sai ki dora a wuta kita juyawa har yy kauri sai ki sauke ki sa madara nd sugar
NB....... Xaki iya soya gyada samasama idan kina so
🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸
💕KUNUN SABARA 💕
Ingredients
Sabara
Sugar
Gero
Citta
Kananfari
Method
Ki surfa gero ki wanke ki shanya ya bushe sai kisa citta da kananfari ki daka anfiso a daka daka dayama inkin saki karfi ya isa dan ana sanshi da tsaki sai ki kirba ki rufe ki ajiye ya kwana kashagari sai ki dora ruwa a wuta kisa sabara su tafarfasa sai ki kwaba amma da kauri kidiba kadan a kofi sai ki sa sugar kitace ruwan sabarar a kai ki rufe kamar 2mints sai ki bude ki daure da gasarar da kk diba
Wannan kunun yana matukar gyara jiki musmman ga masu jego koda kina da matsalar ruwan nono kk sha to zasu kawo
🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷🍷
💕KUNUN ALKAMA 💕💕
Ingredients
Alkama
Sugar
Method
Ki wanke Alkama ki shanya idan tabushe sai ki nika ki tankade kixuba ruwa ki kwaba garin sai ki dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai ki xuba kullun kita juyawa har yy kauri sai ki sauke ki sa sugar
🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸🍸
💕KUNUN KAMU 💕
Ingredients
Gero
Sugar
Madara
Citta
Kananfari
method
Ki surfa gero ki wanke ki jika ya wuni sai ki wanke kisa citta da kananfari ki bayar markade sai ki tace ki barshi y kwana kasha gari sai ki tsiyaye ruwa ki dibi gasarar ki kwaba kidibi wata kadan ki ajiye aside sai kisa sugar ki dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai ki xuba acikin gasarar kirufe kamar 5mints sai ki bude ki daure da gasarar da kk diba sai kisa madara


Post a Comment (0)