RUBUTACCIYAR WAΖAR TSILLA-TSILLAR TSUNTSAYE
* Sunan WaΖa: Tsilla-tsillar Tsuntsaye
* Rubutawa: Jamilu Abdurrahman
* Shekara: 2018
* Baituka: 10
* Jigo: Jan Hankali
(Amshi)
Tsilla-tsilla Ta Tsuntsaye
Ga Gantalin Gaulaye
1
Da Fari Zan Sa Rabbi Wanda Shi Yai Tsuntsaye
Shi Yai Bishiya Yai Mata Rassa Dogaye
Kuma Yai Akuya a Gefe Can Ga shanaye
Ni RoΖona Ka Raba Mu Da Sharrin Mugaye
Ya Allaah!
(Amshi)
2
Tsira Da Aminci Gun Manzo Mai Sunaye
Da Sahabbansa HaΙa Duka Harfa Da Alaye
Da Masu Sonsa Cikin Maza Har Mataye
Domin Darajarsa Ilahu Raba Mu Da Sharrin Ζeraye
Ya Allaah!
(Amshi)
3
Ku Sani Jama'a Akwai Wasu Gungun Kuraye
Sunci Sun Ζoshi Jikin Su Kamar Fa Na Giwaye
Gasu Can Fa him Kuma Basa Shakkar Kowaye
Ya Rabbana Tsare Mu Da Sharrin Zomaye
Ya Allaah!
(Amshi)
4
Sun Ζau Talakawa Sai Kace Wasu Wawaye
Sun Tai Gaba Bayansu Fa Basa Waiwaye
Ga Alama Dai Imanin Su Ya Tafi Ζaraye
Ya Sarkin Mu Ka Raba Mu Da Sharrin Kuraye
Ζ³an Ζota!
(Amshi)
5
Dukiyar Jama'a Ita C Suka Ciccinye
Ba Ruwansu Da Kowa Yara Koko Mataye
Sun Ιauke Mu A Yashe Kamar Wasu Banzaye
Sun Zamo Kaska Jinin Talakka a Shashshanye
Ζ³an Ζota!
(Amshi)
6
Sun Tara KuΙi Sun Auro Mata Jajaye
Bayan HaΖΖin Mu Shi Suka Tat-tauye
Matsabbai Sun Taru Kuma Gefe Can Ga Bokaye
Sun Bar Talakka A Gefe Yana Hawaye
Ζ³an Ζota!
(Amshi)
7
Su Burinsu MuΖaminnan Fa Suyo Haye
Mazalunta Masu Son Rigima Ai Kumayye
Talakka A Yau Wai Shi Za Ai Wa Kiranye
Ya Rabbana Tsare Mu Da Sharrin Guntaye
Ya Allaah!
(Amshi)
8
Matasanmu Mu Taru Mu Bar Shaye-shaye
Komai Nisan Dare Ku Sani Fa Gari Ai zai Waye
Domin Yanzu Kan Mage Ya Fa Waye
Ku Fito Mubi Gaskiya Ba Garwaye
Don Allaah!
(Amshi)
9
Su a Tunaninsu Su KaΙai Ne gwanaye
Gani Fa Suke Wai Bamu Da Wayau Gaulaye
Wankan Nan Fa Yafi Kama Da Jirwaye
Duk Wanda Yazo Da Zamba Mu Taru Mu Tunkuye
Ζan Ζota!
(Amshi)
10
Ya Sarkin Mu Gamu Mun Ζaga Hannaye
Zuciyoyin Mu Dukka Muna Hawaye
MaΖiyan Mu Dukka Ilahu A Tunfaye
Da Sun Nufo Mu Da Sharri Rabbana Ka Kiyaye Mu
Ya Allaah!
Tsilla-tsilla Ta Tsuntsaye
Ga Gantalin Gaulaye
•----------•✬(✪)✬•----------•
Jamilu Abdurrahman
•----------•✬(✪)✬•----------
+23481858191
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Twitter: @jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Instagram: Jamiluwriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
https://m.facebook.com/JamiluWriter
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Tumblr: Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Bakandamiya: Jamilu Abdurrahman
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Telegram: https://t.me/Jamiluwrite
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
LinkedIn: https://www.linkedin.com/in/jamilu-abdurrahman-36b88211
──────⊹⊱✫⊰⊹─────
Haimanraees@gmail.co
──────⊹⊱✫⊰⊹───── ─m─8─r─ ─r─/:─ ─ ─76•