INA JI MA WASU MATA TSORO


*​INA JI MA WASU MATA TSORO​*

Don fa wai mutum ya ga ya samu ni'imar duniya wannan ba ya nuna a lahira ma haka abun yake.

Akwai ban-tsoro ka ga mace bata kiyaye salla a gidanta amma tana wulakanta yar aikinta mai kiyaye salla.

Sai ka ga mace saboda alfahari ko shagala da duniya sai ta tura 'yar aikinta Islamiyya amma ita bata san addini ba kuma bata zuwa Islamiyya, kuma mutuwa na jiran ta.

Mace ce idan ta dauko 'Yar aikinta za su fita tare a mota dole dai ta yi mata wani alama da duniya za su gane baiwar ta ce ta yanda ga sarari a motan amma ta tilasta mata rike jaka a cikin mota ko daukan jariri ko a sanya ta zauna a bayan mota saitin inda Hajiya ke driving tare da cewa su biyu ne kadai a mota amma ba ta isa ta zauna a owner's conner ko gaba ba.

Babban abu lura shi ne, Shi Allah Ta'ala a ranar alkiyama da biyayyan bawa zai yi sakamako ba da babban mota, gida ko tarin dukiya ba.

​WASU ZA SU IYA ZAMA MASU ALFARMA A GIDAN DUNIYA, AMMA KASKANTATTU A RANAR ALKIYAMA​

Don haka 'yan uwana mu yi hattara.

Allah Ta'ala Ya yafe mana kuma Ya kyautata karshenmu, amin.

✍🏼Dan uwanku a Musulunci:
​​Umar Shehu Zaria​​
25/02/2018.

Daga: ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH
Post a Comment (0)