WASU FITATTUN JARUMAN INDIA DA SUNAYEN DA AHALIN SU DA ABOKAN SU KE KIRAN SU DA SU A BAYAN FAGE

WASU FITATTUN JARUMAN INDIA DA SUNAYEN DA AHALIN SU DA ABOKAN SU KE KIRAN SU DA SU A BAYAN FAGE 



1. Ranbir Kapoor

 Mahaifiyar Ranbir Kapoor wato Neetu Singh tana kiran sa da suna Raymond, domin a cewar ta, shi ɗin cikakken mutum ne don haka sunan ya dace da shi. 

2. Shraddha Kapoor

Abokin Jaruma Shraddha Kapoor tun suna yara, wato Varun Dhawan ya kasance yana kiran Jarumar da suna Chirkoot tun suna ƙanana. 

3. Karisma Kapoor

Yawancin abokan Jaruma Karisma suna kiran ta da suna Lolo ne, ko menene Ma'anar sunan? Da Yarbanci dai sunan yana nufin Gimbiya ne. 

4 Govinda 

Duk da cewa Jarumi Govinda ya tsani sunan da mafi yawancin abokansa suke kiran sa da shi, hakan bai hana kiran sa da wannan suna, domin sunan yana da matuƙar ƙayatarwa, wannan suna dai shi ne Chi Chi 

5. Bipasha Basu

Jaruma Bipasha na ɗaya daga cikin Jaruman Masana'antar Fina-Finai ta Bollywood da ake kira da sunaye masu tarin yawa, kaɗan daga cikin ire-iren sunayen da ake kiranta da su kuwa su ne kamar haka: Bipsy, B, Bip, BB, Bhopu, Basu, Baby Basu, Bona, Bips, sai dai sunan da makusantan ta suka fi kiranta da shi, shi ne Bonnie

6. Alia Bhatt

Kafin Jaruma Alia ta fara fitowa a cikin Fina-Finan Bollywood da fim ɗin ta farko wato Student of the Year, ta kasance ɓukekiyar mace ce, hakan yasa ake kiran ta da sunaye iri-iri. Ita da kanta Jarumar tace Mahaifiyarta takan kira ta da Aloo Kachaalu, wasu mutanen sukan kira ta d Batata Vada, Aloo Baalu ko kuma Aloo Kalu... Yayinda ƴar Uwar ta kuma ke kiran ta da Alools.

Alools dai yana iya Ɗaukar ma'anar Kutiɓa ko Lukuta 

7. Sonam Kapoor

Saboda tsawon ta yasa Mahaifin Jaruma Sonam Kapoor Wato Anil Kapoor Yake kiran ta da Giraffe wato Raƙumar Dawa 

8. Priyanka Chopra

Bayan sunan Pee Chee da kuma Piggy Chops da Jarumar tayi ƙaurin suna da su, Jaruma Priyanka Chopra tana da wani ɓoyayyen suna wanda ba kowa ne ya san da shi ba wanna suna kuwa shi ne Mimi, kuma wannan suna ya samo asali ne daga wata Fitacciyar Kyakkyawar mace ƴar Ƙasar Faransa mai suna Mimi Rogers.

9. Hrithik Roshan

Ahali da Makusantan Jarumi Hrithik Roshan Suna kiran sa da suna Duggu ne a bayan fage.


Me zaku iya cewa dangane da waɗannan sunaye? Zan so inji daga gare ku.

<><><><><><>>><><><><><><>
___________________________________

●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●●

<••••••••••••••••••••••••••••>

👳🏻‍♂ *_Haiman Raees_* <••••••••••••••••••••••••••••>

*_"""""""""""""""""""""""_*
📱 _*Phone:*_
 08185819176
*_"""""""""""""""""""""""_*
🌐 _*Web:*_ www.haiman.com.ng

*_"""""""""""""""""""""""_*
🖥 _*Facebook:*_ www.facebook.com/HaimanRaees 

*_""""""""""""""""""""""""_*
🌀 _*Twitter:*_ @HaimanRaees 

*_"""""""""""""""""""""""_*
 🎡 _*Instagram:*_ Haimanraees 
*_"""""""""""""""""""""""_*
 📧 _*Email:*_ Infohaiman999@gmail.com
*_"""""""""""""""""""""""_*
Miyan Bhai Ki Daring...
Post a Comment (0)