DOMIN MA'AURATA




DOMIN MA'AURATA

Daga Sister Maryam Abubakar Sadeeq. 

Gamsar da namiji a jima’ince yafi sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa da cewa dukkannin halittar da aka yiwa mace a jima’ince suma maza suna da irinsa.

Kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma ake samu harijar mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya a lokacin jima’i hakama matan.

Ana samun maza da mata ragwaye a wajen jima’i da kuma wadanda sam jima’in ma bai damesu ba a dukkanin jinsunan biyu.

Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha’awa ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci mai tsawo ana masu wasa duk kuwa da macen tafi namiji bukatar wasan motsa sha’awa mai tsawo.

Abu na farko daya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine abunda yafi bukata a yayi wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin
kwanciya irin na jima’i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa mijinta maimakon ta motsa mishi sha’awarsa sai kawai sha’awar tashi ta gushe.

Hakama a kwanciyar jima’i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin kwanciyar da mijinki yake so. 
Shi yasa malamai na jima’i suke cewa sadarwa a jima’i yana da matukar alfanu ga ma’aurata domin ta hanyar ce zasu iya fihimtar abubuwan da suke bukata a yi musu kafin lokaci da kuma bayan jima’i.

Da akwai mazan da zarar mace ta fara wasa dasu nan da nan suke gamsuwa ba tareda sun shigeta ba, da akwai wadanda da zarar azzakarin su ya shiga shike nan kuma sunyi zuwan kai kenan. 

Akwai mazan da sukan dauki lokaci mai tsawo suna jima’i da mace kamin suyi zuwan kai, wasu mazan kuwa a lokacin da suke kawowa a lokacin ne gabansu ke kara yin
karfi har sai sun kawo sama da biyu koma biyar kafin suke gamsuwa da mace.

Ke naki mijin yaya yake, domin dole sai kin fahimci yadda yake kafin ki iya gamsar dashi.

Sai dai maza masu wuyan sha’ani a jerin mazan da na ambata sune masu saurin zuwan kai da kuma masu daukan lokaci mai tsawo suna gurza mace basu gamsu ba, 
sai dai kuma da zarar mace ta samun ilmin sarrafa irin wadannan maza ta gama dasu.
Post a Comment (0)