GYARAN JIKI

❀⁞⁝⁞⁝⁞⁝⁝《 GYARAN ・JIKI 》⁝⁞⁝⁞⁝⁞⁝⁝


yar'uwa ki kula da jikinki ta baren aske gashin hamata gami
Dana mararki a duk lokacin da kika kasance mai amfani da
irin turaren da Kansan ya hamta kanshi wato shuwa, yin
hakan zaisa hamtarki ta kasance cikin kamshi a koda
yaushe.

yar'uwa ki kasance ma'abociyar kula da kuma gyara gashin
kanki gani da shafa masa mayukan da zasu Kara
ingantashi.

🍀🌿 KURAJEN FARJI 🍀🌱

macen da take fama da kurajen farji su suke haddasa in
ana saduwa da ita taga jini ko ciwon Mara. mai son
maganin wannan sai ta nemi wadannan abubuwan:

kanunfari.
citta.
kimba.

Zaki dake su ki rikka sawa a shayi ko ruwan dumi. idan har
kina yin wannan hadin dole jikinki yayi kyau ki daure kina
yin wannan hadin domin samun lafiyar ki.

GYARAN GASHI DA LEMUN TSAMI

lemun tsami na sanya tsawon gashi sosai, ki kasance mai
gyaran gashi domin burge samari da mazajen aure.

kwai.
lemun tsami.
samu ruwan lemun tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma
man amla. sai ki shafa hadin a fatar Kai da kuma gashi, ki
bar hadin a kanki har tsawon minti 30 , sannan ki wanke da
ruwan dumi, Zaki iya yin wannan hadin sau 2 a wata.

MAN ZAITUN

man zaitun na sanya gashi yayi baki, taushi da kuma
tsawo.

hakan nema ya sa mutanan ketare suke amfani da zaitun.
gyaran fata kina shafa man zaitun fatarki zatayi laushi.
gashi yayi tsayi kina sha man zaitun idan Zaki zauna a
inuwa.

kina shafa man zaitun a cikin farji domin satsi da laushi.
shafa man zaitun akan tabo yana batar da tabo ko na
menene yana maganin zaga yan bakin tabo.

Zaki iya mayar da man zaitun ya zama man kitsonki.

MATAKI NA FARKO ( 1 )

( a) idan fatar fuskarki mai maiko ne Zaki tanadi lemun
tsami da youghurt
( b ) ki matse ruwan lemun tsamin a plate , ki Debi ruwan
lemun tsami karamin cokalin shayi daya ki zuba a yar roba
ki zuba youghurt Baban cokali daya ki gauraya sossai.

MATAKI NA BIYU ( II ) ♻

( a ) ki wanke fuskarki da ruwa da sabulun
( b ) ki goge da tawul tsabtace
( c ) kafin ya bushe sai ki dauko hadin ki shafa a fuskarki ki
barshi a fuskarki na tsawon minti goma.
Post a Comment (0)