LOKACIN SANYI

*_💨 LOKACIN SANYI 🤧 (HUNTURU) ABIN ALFAHRI NE A GURIN MUSULMI MUMINI 💨_*


بسم الله الرحمن الرحيم.

_💨 Alhamdulilah, Sanyi ya shigo 🌬 😁_

_💨 wasu daga cikin mu har sun fara bazama wajen sayan kayan sanyi 🧤, kula da jikinsu, sayan Man shafawa don kare fatar su daga sanyi, sayan su Hula da sauran abubuwan da ke kare mutum daga sanyi, To amma Masu dabara daga ciki murna sukeyi da zuwan wannan lokaci saboda lokaci ne da zasu nemi Gwaggwaban Lada mai yawan gaske._

_💨 Shiyasa Abdullahi Dan Mas'ud ya ce: *“Maraba da shigowar kakar sanyi 💨, tana da alkhairai, Darensa yana da tsayi, wanda ake samun damar bautar Allah, kuma ga masu yin azumi ranakun su basu da tsayi”*_

_💨 Allah Mungode maka 😁, ماشاءالله Sanyi yana da irin wannan Albarka masu girma wanda *“Ranakunsu”* gajeru ne *“Darensu”* kuma yana da tsayi, sannan zamu iya aiwatar da ibadar *Azumi* da safe, *Sallolin Nafila* da daddare._

💨 🥀 *“Sallah tana daga cikin Ginshikin Musulunci guda 5”* 🥀

_💨 Muna da Abubuwan yi da yawa a wannan fannin na *Dare* daga ciki Zamu iya yin sallar Tahajjud, muyi Sallolin Nafila, mu dinga karanta Alqur'ani, Muyi Zikiri (ambaton Allah), mu yiwa Annabi salati, mu karanta hadisan Annabi (Sallallahu alayhi wa sallam), muyi ibadah mu kadai daga mu sai Ubangijinmu, Mu nemi gafararsa, mu nemi Tuba zuwa gare shi, duk a cikin wannan dogon Dare mai albarka na lokacin Sanyi, don mu kara Girman imanin mu mu kuma tsayuwa akan addinin mu_

*☕ Azumi Garkuwa ne ☕*

_💨 Wadanda suka ajiye azuminsu saboda Al'adarsu (haila) ko rashin lafiya ko saboda halin tafiya, ko masu son yin Azumin Nafila, to *Lokacin Sanyi* Shine lokaci mafi dacewa ga yin wadannan ibadun naku da kuka rasa, wallahi wannan lokacin shine yafi sauqi ga bawa da yayi Azumi saboda karancin lokaci da sauqin yanayi da muke dashi, babu rana ☀, balle zafinta, gashi lokaci baya dadewa yanxun nan zaka ji kiran sallah ⏰_

_💨 Wani abu mafi burgewa da *Sanyi* shine yana hanamu sakat wajen saka tufafin da muka ga dama, domin kuwa kowa gani zakayi ya rufe jikinsa kaf, wata ko idonta baka gani saboda tana tsoron sanyi, Oga *Sanyi* shine yake ladabtar da Mata wajen yin shiga cikakkiya, babu fitar tsiraici balle alfasha ta afku. Allah yasa ka *Sanyi* 👍_

*💨 Yawaita Alwala 🚰 a lokacin 'Sabarat' 💨*

_💨 Sabra yana nufin 👉 Hunturun sanyi. Yawaita Alwala a wannan lokaci yana daga cikin manyan halayyar Kara Imanin mutum, idan ya daure wajen yin alwala a lokacin sanyi don ya bautawa Allah, kuma idan akayi ibadah to ladan Zai ninku 2, kuma za'a gafarta zunubai إنشاءالله_

_💨 *Yan uwa masu albarka kada mu bari wannan Rahma ta huce mu,* kada muce *“Bacci”* kawai zamuyi da bata wannan Dogon daren akan Gadon baccin mu 🛏, Mu tashi mu yi alwala mu hau kan Daddumar mu (sallaya) mu tsaya a gaban *Ubangijinmu (Ar rahman)* mu roke shi tare da Farin ciki da annushuwa._

_*🥀 Ya Allah kasa wannan Lokaci Na sanyi ya zamo mana lokaci na aikata aiyukan alkhairi da samun kusanci zuwa gare ka.*_ 👏

*✍ 🌺 Abdullah A Abdullah Abu Khadija (أنصار السنة) 🌺*

15/11/2018

+2348060027244

*You can Follow and read my posts at my new blog 👇*

https://sirassalafeey.wordpress.com
Post a Comment (0)