ZAMA BA AURE BAYAN MUTUWAR MIJI

*_ZAMA BA AURE, BAYAN MUTUWAR MIJI?_*


                        *Tambaya?*
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakaatuhu, Don Allah Mallam zan iya zama ba tare da na sake aure ba kasancewar mijina ya rasu kuma inaso Allah Ya hada ni da shi a matsayin mijina a aljannah?


                            *Amsa*
Wa'alaikum assalam, in har kina da bukatar auran zai fi kyau ki yi, Tunda Allah zai iya ba ki Wanda ya fishi alkairi, sannan za ki iya haifar 'ya'yan da Za su zama sababin shigarki Alanna.

Amma in har ba ki da bukata kuma za ki iya daurewa, kina kuma fatan shiga aljanna, to kina iya jira kamar yadda matar Abuddarda’a ta ki aure bayan mijinta ya mutu, lokacin da Mu’awiya ya nemi ya aure ta, taki yarda ta aure shi, saboda tana so ta zauna da Abudarda’a sahabin Annabi ï·º a lahira.

A duba silsilasahiha hadisi mai lamba ta: 128.

Allah ne mafi sani.

11/12/2016

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_____________________________________

» Zauren *_📖MIFTAHUL ILMI📖_* (WhatsApp).

→ ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren 🔑 _*MIFTAHUL ILMI*_🔑 a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu *(07036073248)* ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)