TAMBAYA TA 043

*SHIN MAI CIKI TANA IYA YIN HAILA ?*
 Tambaya: 
Malam mai ciki za ta iya ganin Haila ? .
Amsa: 
Yawanci idan mace ta dau ciki jini yakan daina zuwa mata,
Imamu Ahmad yana cewa (Mata suna gane samuwar ciki da
yankewar jini) Idan mace mai ciki ta ga jini idan hakan ya
kasance kafin haihuwa da kwana biyu ko uku kuma a tare da
shi akwai ciwon haihuwa to wannan jinin haihuwa ne, idan
kuma kafin haka ne da lokaci mai tsawo, ko kuma tsakaninsa
da haihuwa ba yawa amma ba zafin haihuwa to wannan ba
biki ba ne, saidai shin haila ne ta yadda hukunce- hukuncen
haila za su hau kansa, ko kuma jinin cuta ne ta yadda
hukunce- hukuncen haila ba za su shafe shi ba? Anan
malamai sun yi sabani: Abin da yake daidai shi ne jinin haila
ne in dai ya zo a yadda ta saba yin jinin haila, saboda asali
duk jinin da ya zowa mace ana daukarsa a jinin haila, in dai
ba akwai wani sababi da zai hana shi ya zama haila ba,
kuma babu wani dalili a alqur’ani ko a sunna da zai hana shi
ya zama haila. Wannan shi ne mazahabar Maliku da Shafi'i,
kuma Baihaki ya hakaito hakan daga cikin maganganun
Ahmad.
Don haka yana tabbata ga mai ciki mai haila abin da yake
tabbata ga mai haila mara ciki sai a gurare guda biyu :
.
.
 1. SAKI- Ya haramta a saki matar da idda ta wajaba a gare ta
idan tana haila, amma mai ciki ya halatta a sake ta a cikin
haila, saboda sakin matar da bata da ciki ya sabawa fadin
Allah ( Kuma ku sake su a farkon iddarsu) Suratud Dalak aya
ta 1, wato a farkon tsarkin da bai take ta a cikinsa ba. amma
sakin mace mai ciki tana haila sakin ta ne ga iddarta,
wannan ya hada da tana cikin haila ko tana cikin tsarki,
saboda iddarta tana kasancewa ne da haife wannan ciki, don
haka bai haramta a sake ta ba, bayan an yi jima’i da ita.
.
.
 2. Mace mai ciki idan ta yi haila ba za ta yi idda da ita ba,
saboda iddar ta tana kasancewa ne da haife cikinta, wannan
ya hada da tana haila ko bata yi, saboda fadin Allah
madaukaki ( Iddar mata masu ciki tana kasancewa ne idan
su ka haife cikinsu). Suratud Dalak aya ta 4 Don neman karin
bayani duba : Dima'uddabi'iyya shafi na 11.
Allah ne mafi sani..
Amsawa:--
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)