UKU-BALA'I 24

UKU-BALA'I
NA
KAMALA MINNA
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
​​WÉ› ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucÉ‘tÉ›, MѳtiѵɑtÉ› ɑɳɗ ɛɳtɛʀtÉ‘iɳ ѳuÊ€ ʀɛɑɗɛʀร​.

BABI NA ASHIRIN DA HUDU.
"Ban san ya zanyi ba Baseera, Ban san mai ke damun zuciyata ba, sosai da sosai nake jin zuciyata wani iri, komai nake ji yana sauya mani a filin duniyata kamar bani ce ba".
Ajje numfashi take tana faman tura laɓɓanta duka cikin bakinta tana cizawa fuskarta na kara ya mutsewa kamar mai shirin fashewa da kuka a hankali ta goge gumin da ya taru a goshin ta bayan ta ja gwauron numfashi.
"Shekara daya fa...haba mana Baseera ya dace ace ko wani irin laifi akayi wa mutum yayi afuwa".
Ta sake fadi tana jin zuciyarta na wani irin duka kadan-kadan.
"Ban san laifina har ya kai haka ba...ba ma wannan ba, wallahi ban san mai ma nayi masa ba har ya yi fushi da ni har haka..anya kuwa Baseera Dr.Karami bai manta dani a filin duniyar rayuwarsa ba akan abin da yake ganin babban laifi ne nayi a garesa har ya yanke mani wannan hukuncin wanda yake kokarin tarwatsa komai nawa haba!...".
sosai take jin kanta ya shiga sarawa duniyar ta ji tana juya mata komai taji yana kwance mata kamar ba nata ba a hankali ta dago fararen idanuwanta da suka fara kaɗawa zuwa ja laɓɓanta sai faman ƙarkawa suke kadan-kadan yanayin ta ya nuna gaf! take da rushewa da kuka hakan ya sanyata tsagaitawa da maganar da take yi.
"Tun tafiyarsa Baseera...tun dan ya bar kasar nan nakasa kwanciyar hankali a filin duniya ta ban son ace ya tafi da bacin rai na a duniyar rayuwarsa ba, ban so ace tun waccan lokacin na fara bata masa rai ba, ban so ace alherin sa garemu na mai da masa da bacin rai ba".
Baseera da tun dazu ta zabga tagumi tana duban Mariya da take ta zaro zance cikin rashin hayyaci kallo daya zaka yi mata ka karanci yanayin damuwar da take ciki itama sosai da sosai jikinta da komai nata yayi sanyi.
A hankali ta shiga gyara hijabinta cikin yanayi na sanyin jiki kafun ta kau da kanta daga barin kallon Mariya domin ji take kamar ta rushe da kuka ganin yanayin da ƙawar ta ta take ciki ta sani Mariya ta jima cikin yanayin damuwa ta shafe lokaci mai tsayi lamarin na sukar mata zuciya ba tare da ta bayyana hakan ba sai dai in abun ya matsa mata take shiga damuwa sosai har fuskarta ta sauya a nan zaka gane tana cikin wani hali Mariya akwaita da ZURFIN CIKI ba komai nata take fadi ba ba komai dake zuciyarta ake saurin ganowa ba tana da daukon abu a zuciya irin mutanan nan ne masu boye duk yanayin da suke ciki suna da kokarin boye SIRRI komin girmansa.
"Na sani Mariya kina cikin yanayi amma hakan bai dace ace kin saka rayuwarki cikin damuwa har haka ba as your age ya kamata ace kin mai da hankali sosai akan wannan karatun da kike yi bai dace ace Tension ya fara samun masauki a filin zuciyarki ba a yarda kike kwakwalwarki ya kamata ace saukaken lamari take dauka ba wanda zai hargitsa komai na ta ba".
Nisawa Mariya tayi tana mai sauke wani murmushi mai zafi a zuciya.
"duk abin da kika gani a filin duniyar nan tawa na karuwa har izuwa matakin da nake yanzu SHINE SILA Baseera ya kamata ki san da hakan".
"Na sani Mariya ba sai kin yi mani tuni ba amma hakan ba wai yana nufin don yana fushi dake ba kuma ki lalata komai abin da baki sani ba shine ya kamata ace kin mai da hankali akan komai musamman karatun nan ina mai tabbatar miki duk ranar da ya sako kafarsa kasar nan to abin da zai bukata shine ya kika kasance bayan tafiyarsa shin kin dauki abubuwan da duk yake miki da muhimmanci ko kuma dama can ba wani martabarsa kike gani ba to hanya daya ce shine ki mai da hankali kan komai da komai da kika san na karuwa ne kuma shine sila kamar yarda kika fadi to ki mai da hankali akan su na tabbata in ya dawo duk wani laifi naki zai kau in har kika cika masa alkawarin da kika daukar masa".
Shiru tayi tana dubanta tun da ta fara magana take kallon bakinta ta sani maganar Baseera akan hanya take sai dai kuma bata tunanin maganganun za suyi tasiri azuciyarta domin tashin hankalin da take ciki a filin duniyarta ba ta tunanin zancen wani ba na Dr.Karami ba za su sanya ta cikin natsuwa.
Gyaɗa kai ta shiga yi kamar wata ƙadangaruwa sai faman jan numfashi take.
"Tashi mu tafi Mariya zaman nan a nan ba zai yi mana ba ki dubi fa kowa ya gama tafiya mu ne kadai mu ka rage".
yawatawa da idanuwanta ta cigaba da yi a filin makarantar kafun ta dubi Baseera da ta mike take saɓa jakar ta gami da daukar sauran littatafan ta a hannu ita ma mikewa tayi ta sungumi littatafan ta suka doshi get.
"ni ban san ma abin da ya motsa miki tunanin Dr.Karami ba kwana biyu na lura kin rage amma tun da muka fara Exam din nan shikenan komai ya zama sabo fil! kuma hakan ba karamin nakasu zai kawo miki ba ba fata ake ba amma yakamata ace kin mai da hankali wajan Exam din da muke ba wai tunanin wani lamari ba wanda ba ki san ranar karewarsa ba".
GyaÉ—a kai kawai take yi tana jin zancen Baseera wanda ba ta tunanin zai iya yi mata komai a halin da take ciki.
"Shikenan".
Ta furta murya can kasar makoshi.
*******
Da Sallama a bakin ta ta shiga cikin gidan.
Kamar ko yaushe yau ma dai Da'irar aka kafa sai baza idanu ake yi ana kallon mai shigowa da ficewa.
Kofar dakin su ta kai wa kallo ganin Umma bata nan zaune hakan ya tabbatar mata tana cikin dakin domin ita dama Al'adar tace haka in dai su Goggo Marka na tsakar gidan nan to bata da filin shan iska a cikin sa in kuwa ta zauna ta san sauran.
"nikam cikin kwanakin nan gabadaya Mariya ta canza anya kuwa?".
Hafsi ce ta fadi can kasar makoshi tana duban Goggo Marka da ta kafe Mariya da kallo tana binta gaɓa gaɓa kamar wacce take neman wani boyayyan abu.
"Allah yasa ba mugun abu ta kunso ba".
Hafsi ta sake fadi tana kallon Goggo Marka cikin yanayi na son tace wani abu da zai karawa gulmar ta ta matsayi har ta kara rurata.
"Ke nima fa na so ganin haka 'yar Albarka duk naga ta ɗashe tayi fari ga shi ta rage walwala kai jama'a Allah yasa ba mugun abu ta kunso ba mu ga karshen BIRI BOKO da ake yi mana da fankama wai karatu ake yi ita ga mista ƙyanƙyan 'yar gidan mangwafan".
Muryar Abulle ne da ta fito daga makewayi ya sanya su yin mukus.
Fuskart da fara'a take duban Mariya.
"Ahh Yar gidan Umma har an ta so kenan".
Mariya da hankalin ta gabadaya bai wajan su jin muryar Abulle ta yi saurin tsayawa tana sakin yaƙe.
"Inna ina wuni".
Ta fadi tana durkusawa gabanta cikin yanayi na girmama.
"Lafiya lau Mariya ya karatun dafatan dai ana mai da hankali?".
GyaÉ—a kai tayi ba tare da ta ansa ba.
"To maza aje a cire kayan a huta Ummanku ta ce mani Jarabawa ku ke ko? to Allah ya taimaka ya ba da sa'a gami da nasara".
"Ameen".
Mariya ta ansa ta na mikewa ta karasa shiga cikin dakin da Sallama a bakin ta.
Abulle dake ta faman sakin murmushi jindadi ganin yarda Mariya take duk sai taji ta burgeta sosai a hankali ta gyaÉ—a kai tana duban Hafsi wanda suke bin ta da kallo Uku ahu da sauri suka kau da kai.
"Ke yanzu ba ki ji kunya ba don Allah ki dubi Mariya ke ba abin kiyi sha'awar ta bane yarda take a natse komai tana yin sa cikin hankali".
ta fadi cikin yanayi na bacin rai sosai a fuskarta wani takaicin Hafsi take jin yana tokare mata zuciya ji take yi kamar ta rufe ta da duka.
"To sababba nuna min Mariya tafi Hafsi a wajan ki da kike cewa ita abin sha'awa ne da burgewa a hakan ki ka san mugun abin da take aikatawa kawai ta mai dake sauna da sunan tana zuwa makaranta ke kuma ki yarda nan kuwa tsiyarta take kitsawa".
Dama ta san za ayi haka shiyasa tun farko bata so cewa komai ba abin ne yake ci mata zuciya amma duk da hakan ba za ta fasa fada masu gaskiya ba don haka ta dubi Goggo Marka murya a tausashe.
"Haba Goggo ZATO ZUNUBI fa ko da ya kasance gaskiya ne ke kin san Mariya ba zata yi wannan wautar ba yarinya ce mai hankali ni zan iya shedarta wallahi akan kula da kai".
"To naji ita kuma 'yar taki ballagaza ko".
Goggo Marka ta tare ta a zafafe har tana kumfar baki.
"Nace ita Hafsi ai bata da natsuwa Zainabu ki kiyaye ni bar ganin kin tara su Hafsi hakan ba zai hana ni kwaÉ—a miki mari ba wallahi don na lura mugun halin naki na nan irin na su baki son laifin su kamar su ne suka sunkuto ki duniyar nan".
Sosai Abulle taji zafin maganar don haka ta dubi Hafsi dake ta faman turo baki gama ita ala dole anyi mata ba daidai.
"ke dai kin ji kunya wallahi ba fata zan miki ba amma wallahi sai kin yi takaici duk ranar da kika ga Mariya ta zama wani abu a filin duniyar nan da karatun nan nata da kuke ma kallon hadarin kaji...".
"Tsine mata nace in baki tsine mata ba ba ki cika ke ce ba yar bakin fata kawai ki san Allah Abulle ki kiyaye ne akan takurawa Hafsi da kikeyi acan gidan naki in taje ba ki kyale ta ba haka in kika zo nan gidan ki sakata gaba da hayyata haba! sai kace ba kya ki ka haife ta ba wannan kiyayyar har ina".
"Haba mana Goggo daga fadin gaskiya ni fa tsakani da Allah bana jin dadin yanayin da kike nuna min akan Hafsi ita kenan ba a isa a fada mata gaskiya akan abin da take yi na ba daidai ba kullum ita kenan cikin SANGARTA ni dai ba zan dauki haka ba ya kamata ace ta tsaya ta kula da kanta ita 'ya mace ce...".
"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un".
Goggo Marka ta fadi kafun ta dora.
"Zainabu me kike yi haka ba dai mugun abu kike kokarin daukowa 'yar taki ba nikam Marka ina ganin lalata yau ina ganin mugun abu".
Hannu ta daura akai ta rushe da kuka kamar wanda ka zagarwa uwa nan da nan Hankalin Abulle ya tashi takaici da bakin ciki suka turnuke ta shiyasa sam! bata son zuwa gidan nan domin in dai ta zo ba sa rabuwa ta dadi kuma duk akan Hafsi ne.
"kiyi hakuri Goggo ni fa ba abin da nake nufi kenan ba ta ya ya zan yi wa 'yar da na haifa mugun fata Allah ya tsareni ya tsari baki na da furta kalmar batacin gareta".
"Ke dalla can rufe mani baki ai dama tuntuni na lura kin fi kaunar makiran can akan mu ni da 'yarki ke kenan kullum baki yi mata abun kirki sai dai fada da kushe a haka ki ke so ta dinga zuwa wajan ki a haka kike so ta dinga miki kallon uwarta bayan bakya kaunarta".
Sababi na kin kari ta cigaba da yi tun Abulle na danne zuciyarta har idanuwanta suka kawo ruwa da sauri ta zari mahaifinta tana bata hakuri ta bar gidan zuciyarta cike da bakin ciki da takaicin abin da MAHAIFIYARTA take yi mata akan 'yarta.
Umma da Mariya da tun da suka ji hayaniyar suka leko ganin abin da ke faruwa ya sanya su tsayawa daga bakin kofa domin sun san in har suka takka kan su komai zai koma a shiga kwashe musu Albarka.
Sosai Umma taji rashin jin dadi a zuciyar ta ganin halin da Abulle ta bar gidan da hawaye wanda ta tabbata na bakin ciki ne da takaici ba komai ba.
Ba ta san mai yasa Goggo Marka ke haka ba sam haka bai dace ba ya kamata ace tana baiwa Abulle matsayin ta na Uwa ga Hafsi domin nuna mata hanyoyin da suka dace ba wai ita Goggon Marka ta dinga nunawa Abulle bata isa da Hafsi ba hakan ba karamin ganganci ba ne domin ta tabbata Hafsi ba zata taba ganin Mutuncin uwarta ba sai tafi ganin Goggo Marka da mutunci akan uwarta hakan sam bai da ce ba AKWAI ILLA! sosai da sosai a ciki.
"Umma mana".
Mariya ta fadi da sauti tana mai jinjiga Umma ganin tayi nisa a tunanin.
Dubanta tayi tana ajje numfashi mai karfi ta shiga gyaÉ—a kai kafun ta juya ta koma cikin dakin fuskarta na kara bayyanar da damuwa sosai da sosai.
"Ban san wacce irin rayuwa bace wannan ake yi, Ban san mai zan kira wannan rayuwar ba, mai dauke da son zuciya da son kai, sosai ake shiga hakkin zainabu wanda sam hakan bai dace ba ita uwa ce fa ya kamata, ace ana bata hakkinta da damarta akan Hafsi domin 'yarta ce dole ta kula da rayuwarta komai ya same ta ita zata fi kowa kuka akan abin da ya faru da 'yarta haka in abin farinciki ne ya same ta zata fi kowa son haka maganar gaskiya ya kamata Goggo Marka ta daina irin haka SANGARTA da take sanya Hafsi nayi ba zai haifa musu É—a mai idanu ba".
Numfashi Mariya taja tana komawa gefe tana zaunawa hannayenta duk biyu a haɓarta ta zabga tagumi tana duban Umma cikin yanayi na rashin abin cewa ta tabbata da Goggo Marka zata ji wannan maganar kila cewa zatayi Umma ta kafurta ta a filin duniyar rayuwar musulunci gyaɗa kai tayi kafun ta sake duban Umma.
"Allah ya kyauta".
Da sauri Umma ta dube ta jin abin da ta ce cikin yanayi na son karin bayani.
"Umma mu bar maganar nan don Allah a nan in ma son yin ta kike yi gwanda ki je gidan Inna Abulle kuyi domin na tabbata in kika ce wani abu kwaɓarki ce za tayi ruwa wallahi".
"Amma Mariya Anya rayuwar zata kasance a haka 'Ya mace ce fa ita Hafsi din nan gaba so take yi a kira ta Uwa anya kuwa hakan za ta kasance haba mana ake duba da idon basira ana daura abin da ya dace a MIZANIN HANKALI...".
Cikin yanayi na gundura da batun Mariya ta haÉ—e hannayenta waje guda alamun roko tana kara marere ce fuska kamar za tayi kuka ba abinda take tsoro illa Goggo Marka ta sani ba za a kwashe ta dadi da ita ba in har ta ji wannan batun...
"To Almunafunfun masu lissafa zunubai da ladan bawa tare da yanke masa hukunci shiga aljanna ko wuta ina shiryayyin 'yar taki".
Kamar daga sama suka tsunkayo murya Goggo Marka a kofar dakin su tana kokarin shigowa wata irin zabura Mariya tayi tana komawa can gefen katifar daki inda Mu'azzam ke kwance yana barci tana duban Umma da taja wani Numfashi mai girman gaske tana sauke idanuwanta a kofar dakin.
A daidai lokacin da Goggo Marka ta bankaÉ—o labulan kamar zata tsinke ta ajje shi gefe ta karasa shigowa wani kallo ta watsa musu su duka.
"Ai duk É—an da bai san darajar tirelan itace ba to uwarsa bata dumame da wankan jego kuma sanin darajar 'Ya yake sanya iyaye rikon ta ko da ta aikata ba daida ba".
'Yaa hayyu Yaa kayyum'.
Umma ta fadi tana mai dafe kanta da take ji yana juya mata yana wata irin sarawa kamar zai rabe gida biyu idanuwanta lokaci guda suka kada sukayi jajir sosai da sosai taji zuciyarta da kasan ruhinta na wani irin tururin zafi kamar an rura wutar makera.
A hankali take jan numfashi da take ji kamar zai samu a rauni a tattare da ita sosai take jin wani irin tashin hankali na ziyartata komai na duniyar rayuwarta taji yana canzawa maganganun Goggo Marka ba karamin tayar mata da hankali sukayi ba sosai ta lura shaguɓe da haibaici ta watsa mata wanda hakan ba karamin sanyata cikin ɗacin rai yayi ba gyaɗa kai ta shiga yi cikin rashin abin yi.
"wai har mu za nuna wa bariki a filin duniyar nan ni ban san lokacin da dan yawo da shanu jeji jeji ba har ya san bariki...ko da yake ba abin mamaki bane tunda kullum ana zarya da gantali a ko wani titi da layi na cikin gari ana koyon kissa da yarda barbaÉ—aÉ—É—un mutane ke yi ba shagon gardawa ba a gidan caca".
Hawaye suka zubowa Umma lokaci guda ba tare da ta ba su dama ba, tashin hankalin da take jin kanta aciki a wannan lokacin yafi gaban kwatance sosai take jin wani iri a zuciyarta sosai take jin wani abu mai girma ya tsaya mata a kirji sosai take jin wani irin yanayi mai tattare da kayan takaici da bakin ciki tun daga kasan ruhinta har zuciyarta.
Ba za ta iya cigaba da sauraron wadannan bakaƙen kalaman ba. Zuciyarta..Zuciyarta da kwanyarta sosai take ji ba za su iya daukar tashin hankalin dake cikin kalaman Goggo Marka ba ba ta san lamarin tsana da ƙyarar da take yi akanta har ya kai haka ba, ko da yake ba abin mamaki ba ne in dai Goggo Marka ne za ta iya fiye da haka.
"Nace wani Kullin ku ka jefi 'yata dashi ta sanyawa 'yarta karan tsana a filin duniyar nan, gabadaya na lura natsuwa da hankalin Zainabu ya na kan ku ko ku ne kuka yi nakudarta sai haka".
Ba ta san mai zata ce ma taba a wannan lokacin, ba ta mai ya dace ma tace da ita ba domin komai ya gama kwance mata ta gama tsinkewa da lamarin Goggo Marka.
Hawaye ne suka shiga zubo mata ba ƙanƙautawa kanta a kasa lamarin yana kara sanyata tashin hankali dukan ya yi yawa ta lura Goggo Marka so take yi ta kashe ta da ranta ta kunsa mata bakin cikin da zai sanya zuciyarta bugawa.
"Da ke fa nake kikayi banza dani Habeeba kisan Allah zan baki mamaki sai na shayar dake ruwan tashin hankali ba dai ki dauki damarar tsayawa a rayuwata ba da ta 'yata mu zuba shege ka fasa a tsakanina dake".
Ta na gama fadin haka ta juya tana huci kamar kububuwa ta bar dakin.
Mariya da tun dazu jikinta ke ƙarƙarwa hawaye na zuba ganin irin cin mutuncin da ake wa Umma gabadaya ta shiga tashin hankali mai tsananin gaske zuciyarta na faman yi mata zafi da raɗaɗi kamar zata faso kirji ta yo waje.
Kuka ta rushe dashi mai tsananin zafi da sanya zuciya tashin hankali , kuka take yi da dukkanin yanayin da ta samu kanta a ciki, kuka take yi da duk wani tashin hankalin da zuciyarta ke dauke dashi.
"wannan wani irin BALA'I ne, wannan wani irin tashin hankali ne, Yaa Allah...".
Da sauri ta tsaigaita jin wani sabon kuka ya zo mata dunkulewa tayi waje guda tana haÉ—e jikinta hannunta guda ta tura cikin baki tana cizawa ji take yi komai kamar ba a gaske ba jin komai take yi kamar A MAFARKINTA ba a zahiri ba.
"Ya isa haka Mariya".
Umma ta fadi da wata irin murya mai dauke da tsananin rauni da damuwa.
"Haba mana Umma wai don Girma Allah haka za mu ci gaba da zama ana gaya miki irin wadannan bakaken kalaman ba tare da laifi ba tsakani har ga Allah Goggo Marka ba ta k...".
"Nace kiyi shiru ko Mariya".
Yanayin zafi mai zurfi da ya fito a muryarta ya sanya Mariya sakin sabon kuka mai cike da haushi.
"Ban san mai yasa har yanzu baki san rayuwa ba, Ban san mai yasa har yanzu baki san abin da duniya ta kunsa ba na lura har yanzu baki san kaifaffan ALKALAMIN ƘADDARA ba a duniyar rayuwar dangin rai".
numfashi taja tana jin yarda zuciyarta ke kara matsewa waje gudu da tashin hankali mai girma.
Sakanni ta kwashe kafun ta sake numfasawa.
"ƘADDARARMU CE haka Mariya ya kamata ki san wannan duniya tamkar makaranta take rayuwar da muke yi jarabawa ce mai matukar muhimmanci bai kamata tun yanzu ki karaya da wannan rayuwar ba bai kamata ace tun yanzu ki nuna kosawarki akan ALKALAMIN ƘADDARAnki ba ki sani duk wani rai da yayi saura a filin duniyar nan yana DA SAURAN KALLO ita fa rayuwar nan dama uku ce farko tsakiya karshe misali farko shine haihuwa ki san wannan tsakiya kuma baki san abin da ALKALAMIN ƘADDARA zai dauko miki ba karshe kuma mutuwa ce wanda take tamkar riga a jikin ko wani bawa kullum tana makale dashi har ranar da zata dauke shi".
Sosai Mariya kukan ta ya ragu tana duban Umma da jin irin kalamin da take sanar da ita cikin murya mai laushi da kokarin kwantar da hankali gareta sosai take jin zuciyarta na sassautawa komai na raguwa HAWAYEN ZUCIYA da take jin suna kona mata ko ina na kirjin ta suna raguwa.
"Mariya ki koyi rayuwar zaman duniya DUNIYA MAKARANTA CE mai girma wacce tafi ko wacce makaranta dake cikinta ba abin da ba a koya a cikinta na dadi da akasinsa sannan a makarantar duniya akwai fannoni masu zafi kuma akwai masu sauki kamar yarda kike ganin salo a makarantun da kike zuwa kamar jarabawa ce in kayi karatu ka jajirce sai ka samu nasara amma in ka saka wasa a lamarin sai ka rasa gane kan komai".
Gyara zama tayi sosai tana duban Umma bayan ta tankwashe kafafuwanta kamar mai shirin cin abinci hannayenta a haɓarta ta zuba mata ido.
Murmushi Umma tayi kafun ta sake motsa laɓɓanta da salo na rarrashi.
"Na shiga cikin yanayi na cuta bayan na warke na rasa miji na kafun nan kuma ga halin da nake ciki tare da Goggo Marka kin ga duk wannan ALKALAMIN ƘADDARA ta tuni ya rubuta su da izinin Rabbil izzati za su faru dani tun kafun na zo duniya".
"UKU BALA'I kenan".
Mariya ta fadi can kasar zuciyarta da wani irin yanayi mai zafin gaske domin ita dai ba abin da za ta kira wannan lamarin sai haka ba ta hango alheri a cikin su ba sam! balle ta ce musu UKU ALHERI.
"Karki dauki wannan a matsayin bala'o'i ki dauke su a matsayin jarabawa da kuma abin da ALKALAMIN ƘADDARA ya rubuta miki TUN FIL'AZAL da sahalewar ubangijin".
Da sauri Mariya ta dubi Umma tana ware ido gani take yi kamar ta jiyo abin da ta ke zantawa da zuciyarta.
"Sannan ki sani ba ko wacce Ƙaddara ba ce take samun bawa hka kawai sai da sanadi ko sila sannan kuma akwai abubuwa da yawa da suke faruwa a filin DUNIYARMU wanda da yarda mu da sanadinmu komai ke faruwa damu sosai muke daukan wasu abubuwa da suke faru damu mu jinginawa ƙaddara bayan da saka hannunmu komai ke faruwa shiyasa ake so komai DAN'ADAM zai yi a filin rayuwar duniyarsa ya dinga dubawa yana daurawa a MIZANIN HANKALI kafun ya aikata shi, saboda gujewa kuskure domin KUSKURE DAYA TAK! yake saka mutum a da na sani".
Sosai jikin Mariya yayi sanyi hawaye kadan-kadan suka shiga zubo mata ji take yi kamar JIRWAYE Umma ke yi mata da zantukanta ba wanda ta tuna a wannan lokacin sai Dr.Karami da fushin da yayi da ita ta tabbata ita ce sila ita ce sanadin faruwar komai amma kuma ai ba ta san sanadi ba ba ta san abin da ya sa yayi fashi da ita ba har haka.
"Kan Uban can ke! Habeeba".
Kamar daga sama sukaji Goggo Marka ta lailayo ashar ta kudunma ta daura da fadin haka sosai gabansu su duka ya fadi.
"Yaa Rabbi?".
Umma ta fadi tana mai sakin wani murmushi mai ciwo a zuciya.
"Ni za ku mai da 'yar iska ko".
Ta sake fadi tana fadowa cikin dakin hannun ta rike da zanin atamfa da ya sha jiki kallo daya zaka yi masa ka gane mugunta da aka yi masa reza ce aka saka aka kekketa shi ketawa wanda baza ta bari a sake morarsa ba.
"Uban waye yayi mani wannan mugun abun?".
Ta fadi tana mai duban Umma kafun ta sake idanu akan Mariya da tayi mata kuri da idanu tana jiran Sharrin da zai biyo baya don ta lura TUTAR MAKIRCI ce ta motsa.
"Da ku fa nake yi ku ka yi mani carko carko da ido kamar kwarto ya fada dakin suruka ya rasa dan kamfansa".
Ajiyar zuciya suka saki su duka zuciyarsu da wani irin yanayi mai sanya É—aci a kasan zuciya da ruhi.
"in ban da bakar mugun ta da bakin sharri yanzu Mariya saboda an koya miki bakin hali irin na dangin uwarki shine zanin nawo kika kama ki ka kekketa sabo mugun abu".
'Yaa Salam!'.
Umma da Mariya suka fadi a zuciyoyin su
Ba su an karaba sai kawai saukan mari Mariya taji a kuncin ta ji kake kau!.
"Dan uban uwarki LamiÉ—o ne ya saka ki yi mani mugun halin nan ko billahillazi sai kin biyani in ba haka ba na dake ki dukan shan gishiri".
Tana gama fadin haka ta jefa mata zanin a fuska ta juya tana watsa wa Umma wani makirin kallo da tukuicin tsaki sannan ta fice daga dakin.
Hawaye suka ciccko a idanun Mariya ta shiga gyaÉ—a kai ganin irin kallon da Umma take yi mata mai kama da TUHUMA.
"BA NI BA CE".
"Na sani".
Umma ta fadi tana mai sakar mata murmushi kafun ta kau da kai tana dauke Kwallar da suka kawo idanunta farmaki...
*KAMALA MINNA*😘😘😘

Post a Comment (0)