INA JI MA WASU MATA TSORO


*INA JI MA WASU MATA TSORO*
Don fa wai mutum ya ga ya samu ni'imar duniya
wannan ba ya nuna a lahira ma haka abun yake.
Akwai ban-tsoro ka ga mace bata kiyaye salla a
gidanta amma tana wulakanta yar aikinta mai
kiyaye salla. Sai ka ga mace saboda alfahari ko
shagala da
duniya sai ta tura 'yar aikinta Islamiyya amma ita
bata san addini ba kuma bata zuwa Islamiyya,
kuma mutuwa na jiran ta.
Mace ce idan ta dauko 'Yar aikinta za su fita
tare a
mota dole dai ta yi mata wani alama da duniya
za su gane baiwar ta ce ta yanda ga sarari a
motan
amma ta tilasta mata rike jaka a cikin mota ko
daukan jariri ko a sanya ta zauna a bayan mota
saitin inda Hajiya ke driving tare da cewa su biyu
ne kadai a mota amma ba ta isa ta zauna a
owner's conner ko gaba ba. Babban abu lura shi
ne, Shi Allah Ta'ala a ranar
alkiyama da biyayyan bawa zai yi sakamako ba
da
babban mota, gida ko tarin dukiya ba.
*WASU ZA SU IYA ZAMA MASU ALFARMA A
GIDAN
DUNIYA, AMMA KASKANTATTU A RANAR
ALKIYAMA*
Don haka 'yan uwana mu yi hattara. Allah Ta'ala
Ya yafe mana kuma Ya kyautata
karshenmu, amin.
Post a Comment (0)