TASHAR ALBANIY TV


TASHAR ALBANIY TV 

¶ A madadin Annasiha Foundation tare da É—aukacin Ma'aikatanta naa taya Cibiyar Ilimi ta Daarul Hadeethis Salafiyyah, Zaria, Kaduna State, Nigeria murnar kafa sabuwar TASHA ta Satellite, wacce ake fatan fara aikin ta nan da kwanaki uku masu zuwa In Sha Allah. 

¶ Bayyanar wannan Tasha zata taimaka matuÆ™a wajen Æ™ara faÉ—aÉ—a yaÉ—a Karatukan Bijimin Malamin wanda ya assasa cibiyar wato Sheikhul Allamatul Muhadeeth; Abu Abdurrahman Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (Rahimahullah).

¶ Malam ya tsinci kansa a wani lokaci wanda masu gidajen Tv da Rediyoyi ke gudun sanya karatukan sa don irin gaskiyar da yake tsagewa cikin jawaban sa, harma acikin wani Tafseerin sa na Suratul Baqara ya tursasu yake cewa; "Ba dai akwai Internet ba, to ba komi ai, za'aji karatun mu ", ayau kuwa an wayi gari Karatukan Malam sune suke haskawa a dukkanin inda ake magana da harshen hausa a faÉ—in duniya gaba É—aya, a bisa analytics É—in mu na AnnasihaTv kuwa na watan September, Continent 5 suke sauraron Karatukan Malam, ciki harma da Europe. 

¶ Wannan kuwa na koyar da darussa da daama, daga ciki; 

~Malami kar ya sake ya É“oye gaskiya don barazanar ba za'a yaÉ—a karatun sa ba, kowa ya gane abun a hannun Allah yake. 

~Kuma yana koyar damu cewa; ka da wani gidan Tv ko Rediyo ya Æ™i yaÉ—a wata magana ta gaskiya don tsoron wata barazana, da haka muke fatan wannan gida na Albaniy Tv ya tsayu akan gaskiyar da ake mishi fata, ka da ya yaÉ—a duk wata magana ko karatu wadda bata daace da shiriyar magabata ba, duk wani Malami wanda son zuciya ya bayyana tattare dashi, ko kaucewa manhajin Annabi da Sahabbai ma'ana Salafus-Saleh, ka da wannan gida ya yi mu'amala da shi ko kaÉ—an ko da kuwa al'ummah za ta soke su, kamar yadda aka san Daarul Hadeethis Salafiyyah da tsayawa gaskiya komin rintsi lallai a tsaya a hakan. 

¶ Malam na cewa: "babu tashar da yake fatan a haska Karatun shi irin Tasha Mallakin Daarul Hadeethis Salafiyyah" Allah bai Æ™addari faruwar hakan a lokacin rayuwar Malam ba. Babban burin Malam kuma kamar yadda yasha faÉ—a shine yaÉ—a Karantarwar da Aqeedah irin ta Salaf zalla; babu sirki, tare da faÉ—a da munanan tunanuka masu cin-karo da irin wannan Aqeedar. 

 Muna roÆ™on Allah SWT kamar yadda wannan buri na Malam ya samu cika, haka muke fatan Allah Ya ida masa sauran nuface-nufacen sa na alkhairi, harma da namu baki É—aya, Ameen! 

¶ Ƙiran mu ga Al'ummar Musulmin Duniya kan wannan Tashar shine; su karkato akalarsu su bayar da lokacin su tsaf wajen kallo da sauraron wannan Tasha da sanyawa Iyalansu domin kasantuwa da abubuwan alherai da za su amfane mu Duniyar mu da Lahirah. 
 A É“angaren guda kuma kamar kullum ANNASIHA na mana Nasihar mu guje ma kallace-kallace a Tashoshin da basu da wani amfani, hasalima sai dai cutarwa da É“ata lokaci har ta kai ga cutarwa cikin Addininmu da lalacewar Tarbiyyar ƳaÆ´anmu. 
 Muna tunatar da Magidanta su ji tsoron Allah su sani da sai Allah Ya tambaye su gameda Tarbiyyar Iyalansu, lalle ne a kula da kallon abunda zai amfani mutum a Addini da Rayuwa. 

¶ Har wayau ÆŠaliban Ilimi kada ayi baya-baya wajen tarawa don kallo da sauraron Ilimoman da Malam ya zube cikin Karatukan shi a lokacin rayuwar sa. 

¶ Ƙorafi da daama da akan aiko mana na rashin "Space", ko rashin "Data", ko yawan tambayar ina karatun Malam Albaniy kaza da kaza, ko kuma masu yawan tambayar mu kan ina Karatukan Sheikh Dawud Azzahiriy Hafizahullah, to yanzu Æ™orafi ya Æ™are, "nesa ta matso kusa" a kusan kullum yanzu muna fatan za ka samu Karatukan Malam da na sauran zaÆ™aÆ™uran ÆŠaliban Malam É—in gaba É—aya, hala harma da sauran Maluman Salafiyyah na Najeriya. 

¶ Muna kira ga Ƴan Kasuwa da masu KuÉ—in mu su rinÆ™a yi ma Addinin Allah hidima musamman, su cire daga cikin Taskokinsu su kawo KuÉ—i ba tare da sanya wani sharaÉ—i ba don a yaÉ—a Addinin Allah, mu sani abunda Allah Yake so muyi da Dukiyar da Ya bamu kenan.
Ƙiran mu ga Mahukantan wannan Tasha shine; a bayar da kula ta sosai da sosai wajen sanya Karatukan Sheikhul Allamah: Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria Rahimahullah fiye da na kowa, kamar yadda sunan Tashar ya bayyana. Wato Muna fatan Tashar ta zama mai share Hawaye ga duk mai Æ™ishirwar neman dukkanin Karatukan Malam Albaniy musamman ma na Video, wanda har ila yau mutane daga ko'ina ke kukan rashin samuwar karatukan. 

¶ Muna fatan Mahukantan Tashar da su samar da Æ™ayatattun shirye-shirye masu Ilimantarwa kan fannoni da dama na Rayuwa, Zamantakewa da makamantansu waÉ—anda suka dace da koyarwar Sunnah; don karkato hankulan Musulmi daga barin Tashoshin Ƴan Duniya. Lallai ka da a manta da Matasa acikin tsarin wannan Tasha mai albarka. 

¶ Wannan Tasha mai albarka za ta fara aiki ne a Watan January, 2022 kuma za iya murÉ—o ta ne akan Satellite da waÉ—annan adireshan: "Amos 17° East
Frequency: 11753
Polarity: 28200
Vertical Symbol Rate: 28000 

¶ Baza mu Æ™arÆ™are wannan Rubutu ba sai mun yi Addu'o'i na musamman ga Sheikhul Islam: Albaniy Zaria Rahimahullah wanda shine asalin wanda ya samar da wannan alheri, Ubangiji Allah Ya lulluÉ“e Kabarinshi da Rahama Ya amshi ayyukan shi Ya kyautata bayan shi Yayi ma abunda ya bari albarka, Allah Ya sanya Aljannar Firdausi a matsayin makoma, Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum. 

¶ Baza mu mance da zaÆ™aÆ™uran ÆŠalibin Malam da suka tsaya ba dare ba rana suna cigaba da hidimtawa wannan da'awa da Malamin su ya rasu ya bar su a kanta ba, irinsu Sheikh Dawud Azzahiriy Hafizahullah da makamantansu, Ubangiji Allah Ya saka musu da mafificin alheri Ya tabbatar da diga-digansu akan wannan Da'awa ta Salafiyyah Ya kuma biya su da gidan Aljannar Firdausi, Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum. 

¶ Mu ma a Annasiha muna neman mutane da su taya mu da Addu'o'in fatan alheri, Saboda muna da burin samar da tasha, wato za mu harba Satellite É—in farko na Musulmi, namu na Æ™ashin kanmu ba na wasu ba don yaÉ—a Karantarwar Musulunci abisa tafarkin Annabi SAW da SahabbanSa (Salaf) .

¶ Annasiha na gayyatar Al'ummar Musulmin duniya kaf wajen tarayyar samun lada ta hanyar sauraron Karatuka iri-iri da za a rinÆ™a watsawa a Tashar tare da kuma aiki da abunda za a karantar damu.  

Allah Ya karÉ“a mana Ya taimake mu Ya kuma yardar mana, Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum 

✍️ ANNASIHA FOUNDATION 
 (Don't Forget to like, follow, Subscribe and Share, Jazakumullahu Khairan) 

 Facebook Page 👇 
https://www.facebook.com/annasihatv/

 Telegram Channel 👇
https://t.me/AnnasihaTvChannel 

 Karatukan Malamai Channel 👇 
https://t.me/AnnasihaTvCh

 Instagram Account 👇
https://instagram.com/annasihatv?igshid=1pq1vxrx3ubp6

 Youtube Channel 👇
https://www.youtube.com/AnnasihaTvChannel 

 Twitter Handle 👇
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09

 WhatsApp 👇
https://wa.me/message/GBDQ6DR6SEF5D1

 TikTok; 👇
https://vm.tiktok.com/ZMeYYVnPP/

 Call:
+2348063836963 +2348142286718

 Email :
islamisannasiha@gmail.com

2 Comments

Post a Comment