KYARKECI DA 'YAR TUNKIYA

💧💧💧💧💧💧💧💧💧💧
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

     DARUSSAN RAYUWA


  ࿐​ ​PRODUCTIVE WRITERS ASSOCIATION࿐​

༄༄ PWA ༄༄

 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖
                ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
     ʂɬơrყ/wrıɬɛɛŋ     
            ɮʏ✍🏻:
👉🏻© ɧãımãŋ Řâééʂ ✹••✹••✹••✹••✹••✹••✹
 ➖➖➖➖➖➖➖➖➖

                    Fitowa ta 01

   KYARKECI DA 'YAR TUNKIYA

Watarana wani makiyayi yana kiwo tare da dabbobin sa, sai wata 'yar tunkiya daga cikin dabbobin ta hango wata kyakkyawar Ciyawa daga can gefen filin da suke kiwo. Nan dai wannan 'yar tunkiya tayi ta bin wannan ciyawa tana ci har tayi nisa da sauran dabbobin da suke kiwo tare ba tare da ta sani ba. 

Tana can tana shagalin ta, bata sani ba ashe wani Kyarkeci yana ta matsowa wajen ta. Sai dai, Yayinda kyarkecin yayi tsalle ya dira a kan ta, sai tayi maza tace da shi; "Don Allaah kada ka cinye ni yanzu, domin kuwa cikina cike yake da ciyawa, da ace zaka ɗan jinkirta kaɗan da sai nafi daɗi yayin da zaka cinye ni".

Yayinda Kyarkecin nan yaji wannan shawara sai yayi tunanin lallai hakan shi yafi dacewa, don haka sai ya dakata. Bayan wani ɗan lokaci sai wannan ƴar tunkiya tace da shi, "Ai kuwa da zaka barni inyi rawa da abinda naci zai fi saurin narkewa a Cikina". Anan ma dai sai Kyarkeci ya amince da wannan shawara. 

'Yar Tunkiyar Nan tana cikin rawa sai wata dubara kuma ta zo mata, don haka sai tace; "Kaga wata' yar ƙaraurawa nan a wuyata, da zaka ɗauke ta kamin kiɗa da ita ai da zan fi jin daɗin rawar, hakan zai sa abincin na naci yayi saurin narkewa kai kuma daga nan sai ka cinye ni cikin Nishaɗi da jin daɗi. 


Ai kuwa sai wannan kyarkeci ya cire ƙaraurawar da ke wuyan wannan 'yar tunkiya ya dinga bugawa iya ƙarfin sa. Ƙarar buga wannan ƙaraurawa ce tasa wannan makiyayi ya taho da gudu shi da karnukan sa, da ganin su sai wannan kyarkeci ya yar da wannan ƙaraurawa ya runtuma daji da gudu kamar ransa zai fita. Shi kuwa Makiyayi, sai ya ɗauki 'yar tunkiyar sa ya tafi yana mai godiya ga Allaah. 


DARASIN LABARIN: A lokutta da dama ƙarami wanda ake ganin bashi da ƙarfin ceton kansa yana iya samarwa kansa da 'yanci ba tare da yayi rigima ba, domin kuwa ba kowace irin matsala ce ƙarfin damtse ke iya warwarewa ba. 


<••••••••••••••••••••••••••••>
      ɧãımãŋ Řâééʂ <••••••••••••••••••••••••••••>
       08185819176
Twitter: @HaimanRaees 
Instagram: Haimanraees 
Infohaiman999@gmail.com

Miyan Bhai Ki Daring

 
Post a Comment (0)